Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : HAUSA.IR
Alhamis

26 Nuwamba 2015

08:50:53
721635

Iraki: Matakan Tsaro na karuwa Saboda kusantowar Arba’en Hussaini{a.s}

Matakan Tsaro na karuwa Saboda kusantowar Arba’en Hussaini{a.s}

Hukumar  Iraki ta fara gudanar  da matakan tsaro domin kare masu ziyarar Arba’en ta Imam Hussain (a.s). hukumar  tsaron Irakin ta tabbatar da cewa daga jiya laraba ne dai aka fara gudanar  da matakan tsaro a duk fadin kasar, saboda fara tattakin kilo mitoci  daga sassa daban-daban zuwa birnin Karbala mai tsarki. Akan iyakar Iran da Iraki da akwai dubban masu ziyara da su ke shirin tsallaka iyaka domin shiga cikin kasar ta Iraki. An baza ‘yan sanda akan manyan hanyoyin da masu ziyarar su ke shirin bi ta kansu zuwa birnin Karbala mai tsarki. Pira ministan kasar Haydar Abadi ya yi kira da a bada cikakken hadin kai domin tabbatar da tsaro a tsawon lokacin ziyarar. A kowace shekarar dai miliyoyin Irakawa da kuma baki daga kasashen waje ne su ke shiga cikin kasar ta Iraki domin ziyarar 40 daga shahadar Imam Husain. (a.s)288