Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : mu'assasatul thaqlin
Litinin

20 Afirilu 2015

06:37:16
685039

AUNA ZABEN 2015 DA WASU MUHIMMAN AL’AMURA DANGANE DA SIYASAR NIGERIA kashi na{ 3} Daga Shaikh Hamzah Muhammad Lawal

Wanda ya rubuta Abu Ahmad Addaurawiy A’UZU BILLAHI MINASH SHAYDANIR RAJIM BISMIL-LAHIR RAHMANIR RAHIM WASAL-LAHU ALA MUHAMMADIN WA ALIYID DAYYIBINAD DAHIRIN

Da suka ga ba zasu ci zabe ba kaman yadda muka ce in da an yi shi 14 ga wata Febreru sai suka fake da dalilin tsaro,wannan ba dalili bane saboda ba sojoji ke conducting zabe wato suke tafiyar da zabe.Sannan na biyu inda ake rigimar a Arewa maso gabas ba duka Nigeria bane saboda haka da za a ce an kai wa Nigeria hari da ya za a yi in ya zama a wannan wuraren kawai ake rigima amma soja za su shagaltu da wannan?Misali in da a ce an kawo wa Nigeria hari ne daga bangarori daban daban ya za a yi kenan?saboda haka ala kulli hal wannan ba dalili bane,sun kawo shi kuma suka daga zaben.Wannan jinkirta ranan asara ce ko asara ce kawai amma bai taimake su da komai ba duk da yake sunyi kokari sun yi tunani akan cewa idan suka yi haka zasu fi samun Karin lokacin makirce makircen su kaman misali: “Zasu dinga amfani da kudin gomnati a wurin kamfen din su sai ya zama APC kudin da suke amfani dasu kila zai kare da wasu dalilai daban da kuma basu daman su kara inganta hanyoyin su na magudi”,haka duk wadannan suka wuce aka zo aka yi zaben sai ya zama inda ya zama basu iya yin tasiri ba saboda mutane sun fito duk da yake ba sosai ba.Ta bayyana kiri-kiri akan cewa wadanda suka fito aka tan-tance su a asali da safe ba dukkansu bane suka koma suka yi zabe da yamma ba,mutane kadan suka yi zabe a wannan lokacin,wannan ya bayyana kiri-kiri.Sannan ta bayyana kiri-kiri akan cewa katin yayi aiki duk da yake akwai inda ba a fahimce shi ba wato katin bai karanta zanen yatsu ba duk da yake ba laifin katin bane laifin su ma’aikatan ne wadanda bas u san cewa sai an bare ledan ba.Sannan haka kuma ta bayyana kiri-kiri akan cewa su ma’aikatan zaben sun yi Nigeriyanci a wurare masu yawa da  yanda basu je wajen aikin ba a lokacin day a kamata su je ba,akwai irin wadannan matsalolin nan da can. Zaben gabaki dayan sa in ka dauke shi zaka ga yayi inganci sosai domin shi Card Reader din yayi aiki dari bisa dari a wurin tan-tance masu zabe da kuma sauran ayyukan da suka sa shi duka yayi wurin aikawa da Information da kuma tabbatar da cewa wadanda aka tan-tance su kadai zasu yi zabe ba wadanda suke a registan zabe ba da kuma cewa ya hana ayi aringizo na kuri’u da ma’anar cewa ba yanda za ayi misali an tan-tance adadi  300 sai kuma ace mutune 350 suka yi zabe,ba zai yiwu ba.Card reader ya taimaka sosai wajen sanin kowane Polling Unit mutum nawa suka kada kur’a a wurin amma a da irin wannan raran ne aka yin magudi ayi dangwale sai ya zama hakan bai yiwu ba,a lokacin da PDP ta ga wadannan mashinan suna aiki sai suka yi ta matsawa akan a dinga amfani da wannan abinda ake cema INCIDENT REGISTER din ya zama a ajiye card reader din,a lokacin INEC ta yadda a ajiye Card Reader din a wasu jihohi wanda wannan babban kuskure ne amma kuma wanda yake ya kautar da kasar daga masifar da zata iya faruwa da wannan kuskuren bai faru ba,sune irin su Delta da Rivers da sauransu anyi haka saboda haka sai aka zo da kuri’u suna da ban mamakin gaske amma gwara da suka bari aka zo da wadannan miliyoyin kuri’un sai ya zama ba suyi tasiri ba akan sakamakon gabaki daya ba.Daga cikin abubuwan da suka tsara su yan PDP din shine ya zama cewa ba yi zabe wanda yake CONCLUSIVE ba wato sun so ayi zaben da a cikin shi akwai tababa da shakka an kaishi zuwa wani miqdari sai ya tsaya,kila INEC ta kalli wannan shi yasa ta bari aka yi magudin a wancan wurin tun da bai canja sakamakon n agama gari ba. To yanzu anyi zabe an ce Buhari ne ya ci zabe da sauransu sai me kuma?Mutane da yawa suna ganin wannan cewa idan Buhari ya ci zabe to komai zai canja wato yanzu kaman aljanna za ta zo.Tabbas wasu abubuwan zasu canja,kaman a Chatham House ya fadi ba za a samu cin hanci da rashawa  wato ba za a samu CORRUPTION ba,ee wannan gaskiya ne ba za a samu cin hanci da rashawa ba akalla kaman yanda ake samu a da ba.Sannan kila zai kokari ya sake Civil Service zuwa yanda yake a da,sannan za samu DISCIPLINE da ESPIRIT DE CORP  da REGIMENTATION a Armed Forces din Nigeria,sannan kila darajar Nigeria za ta karu a kasashen duniya,sannan za a yiwa mutane ayyuka sosan gaske,sannan kuma kila zai zama matakan tsaro na mutane zai karu,wannan tabbas zai yiwu sun samu amma akwai tsoro ni SHAKSAN  da nake kallo kuma zan so wannan tsoron ya kai ga wadanda zasu kai gomnatin sa din in zai yiwu in akwai hanya. Na farko na fada maku abinda Femi Fani Kayode ya fadi wanda na dauke shi da muhimmanci saboda Empirical Evidence ba saboda LOGIC,ko EMOTION,ko MANDIQ,ko THEORY ko HYPOTHESIS ko SPECULATION ko IMAGINATION ko abinda yayi kama da wannan ba.Femi Fani Kayode ya yi da’awa kila karya ne kila gaskiya ne ko kuma don siyasa ne amma tana da muhimmanci a da’awa.Femi Fani Kayode yayi da’awa cewa a lokacin da General Buhari ya  tafi London yayi wa kasashen turai wasu alkawuka,ban san ko kun ji wannan da’awan da yayi ba,wannan din muna so mu san ko gaskiya ne ko ba gaskiya bane.Kafin Femi Fani Kayode yayi wannan da’awan ni Shaksan(personal)na yi mamaki kuma na ji haushi kuma nayi bakin ciki a lokacin da ta bayyana General Buhari a London yayi taro da GORDON BROWN da TONY BLAIR,wadanda wadannan mutane kwata kwata basu da tasiri a cikin siyasar Ingila a yau,sannan musamman Tony Blair  wanda shi WAR CRIMINAL ne tare  da GEORGE BUSH a idanun masu hankali masu yawa a America da duniya gaba daya saboda yakin da suka jagoranta a Afganistan da Irak da sauran kasashen musulmi da kashe miliyoyin mutane da suka yi da kuma matsayin Tony Blair akan larabawan Palastine saboda shugabantar wannan QUARTET din da yake yi akan matsalolin mutanen Palastine da kuma abubuwan da suka aikata Ruwanda da Burundi da irin su Angola da South Sudan da kasashen da suka yi kama da haka.Tony Blair mutum ne wanda kwata kwata mai mutumci bai kamata a ga yana alaka dashi ba.Sannan Gordon Brown kuma wanda ya karbi gomnati a hannun Tony Blair akan asasin yarjejeniya,mutum ne wanda shi kanshi Tony Blair yayi DISCREDITING dinsa wato shi Tony Blair a kanshi ya riga ya rusa Godon Brown shi kuma Gordon Brown ya taimaka sosan gaske a wajen ha’inta da cutan mutanensa na Scotland a lokacin wannan zaben raba gaddama da aka yi akan cewa Scotland ta cigaba da zama UK ko kuma ta zama yantatta ?shi Gordon Brown ya taimaka a wajen rusa wannan yunkurin na mutanen Scotland akan su samu yanci su balle daga United Kingdom.Kuma mun san ra’ayoyinsa dangane da al’amura na AKLAQ ko kuma rashin Akhlaq a cikin duniya,mun san tsoro da barazana da suke a Nigeri,Jonathan ya yi kokari a wurin cijewa da jajircewa a tursasawan Tony Blair da Gordon Brown da Obama akan majalisar kasa a Nigeria ta shigo da rashin Akhlaq a cikin Nigeria duk da yake ya fadi a wasu wajajen wanda muna so mu tabbatar da wajajen day a fadi ba zai cigaba da faruwa ba,kaman misali a Nigeria a yanzu inda Jonathan ya fadi sosai a bangaren Akhlaq a Nigeria yanzu ana karfafa yan fim da waka kuma ana daukan kudi daga kasafin kudin Nigeria a Miliyoyin kudi ana ba wadannan yan fim din da mawaka,kuma Hollywood ta shigo cikin Nigeria a Industries din fim da wake wake musamman suna zuwa da African-American ma’ana Amerikawa wadanda suna da asali da Africa domin su gurbata dabi’un masu fim da masu waka a Nigeria shi yasa wasu mawakan da yawa za ka dauka masu RAP din America ne suke yi a Nigeria.To muna so mu san wannan da’awan da Femi Fani Kayode gaskiya ne ko karya?a cire SENTIMENT da EMOTION a ajiye gefe. Sannan na biyu Mutane irin su Nasiru El-Rufa’i wadanda suke tare dashi General Buhari din muna so mu fahimce su fiye da yanda muka fahimce su a da da yanzu,a kwakwalwansu da yanda suke tunani da tsare tsarensu da sauransu.Zai iya yiwuwa a cikin wadanda suka fito takara kila Nasiru El-Rufa’i duk ya fi su kuma haka ne,ya fi su a fagage masu yawa a tunani da abubuwa masu yawa amma muna so mu san dukkan tunaninsa gaba daya saboda ra’ayina dangane da Nasiru El-Rufa’i akan asasin abinda ya rubuta da kanshi a littafinsa ACCIDENTAL PUBLIC SERVANT shine cewa yana da alaka sosai da jami’an gomnatin America,gomnatin Bush da gomnatin Obama da sauransu.Sannan wannan karatun da yayi naMASION FELLORSHIP yana bukatan bincike sosai da abinda ya sanya a kwakwalwanshi da wadannan shafuka 300 da ake sa su a Harvard University yana karanta wa a kowacce rana wanda shine requirement na cin nasara a karatun da yayi da cin jarabawa da sauransu.Sannan wasu daga cikin tsare-tsaren da Nasiru El-Rufa’i da yake so yayi ko ya aiwatar da jihar Kaduna idan ya zama gomna suna da Mulahaza masu yawa,kamar misali:-tsarin shin a Boarding School,yana so ya maido da makarantun kwana maimakon na yini,tsari ne mai kyaun gaske tun tuni nima ina goyon bayan makarantun kwana maimakon makarantun yini.Ya fahimci mahimmancin wadannan makarantun na kwana sosai saboda shima ya bi cikin irin wadannan makarantun ne da kuma tasirin da suka yi masa na hada mutane daban daban waje daya su tattauna su  san junan su ILA AKHIRIHI,sannan yana kallon yaran shi akan kanshi yana ganin sun fi bada muhimmanci akan talabijin da game da satellite da Internet da sauransu wato sun fi alaqa da wadannan fiye da alaqa da mutane masu rai a waje,sannan wasu daga cikin yayansa sun tafi kasashen waje suka yi karatu sun rasa wannan abin da shi ya samu a Boarding School kuma yana takaici akan wannan.Na dan san shi kadan ko?.To  amma abin da ya faku masa shine cewa kila ya taimaka wajen yayansa su zama yanda suka zama duk yake zai iya kare kansa yace yayi haka saboda tsarin ilimin Nigeria bai da kyau sannan kuma kudin sa ne yayi amfani dasu ai kuma zai iya kasha kowanne irin MIQDARI na kudi wajen yiwa yayansa tarbiyya ta bangaren ilimi amma wannan zai iya zama uzuri ne a wajen ba dalili ba.Muna so mu sani wannan batun Boarding School din,Mulahazar itace makarantun kwana a wancan lokacin ba yanda za a yi kwatanta su da makarantun kwana a wannan lokacin wato yanzu.Shi yana magana makarantun kwana ya dinga ba da abinci kyauta sannan ya kara albashin ma’aikata,to wadannan guda biyun basu wadatar ba don saboda ka kara albashin malami ko kuma ka rage ko saukake kudin abinci a makaranta ko kuma ka mai dashi kyauta bai wadatar ba saboda muma mun bi ta wannan boarding  secondary school din saboda haka mun san yanda abubuwa suke gudana.A lokacin da muke makarantan kwana malaman mu suna da mutunci kuma ana girmama su,alal hakika ma idan ina kallon malaman mu a wancan lokacin sai in dinga kallon su kamar wasu shugabanni kasa ya kamata su zama ta hanyar gogewar su a wajen karantarwa da Discipline dinsu da mutumcin su da ababen da suka yi kama da wadannan.Ni nayi House Captain a lokacin ina Secondary School kuma ina da House Master wanda nake mu’amala dashi kuma na san yanda suke domin mutane ne masu mutumcin gaske sannan a lokacin muna da malamai da sun taho daga kasashen waje,mutane ne sosai gogaggu daga Canada da Indiya da Pakistan,da Ghana da Bangaladash daga kasashe masu yawa na duniya,mutane idan ka gansu zaka ga mutane sosai da iyalansu da yayansu da ababen da suka yi kama da wannan.To akwai mutane wadanda suke gogaggu an tantacce su an tarbiyantar dasu sun san abinda suke koyarwa?suna da hankali?Malaman mu a lokacin da muke secondary school sababbin motoci suke hawa wato BRAND NEW,sannan su malaman da suke zuwa daga kasashen waje gidaje aka ba su da kuma REMITTANCES wanda suke aikawa kasashen su da sauransu.Kuma a lokacin akwai discipline sosai saboda shi kanshi yana magana game da Principal dinsu na Barewa College wanda tsohon soja ne kamar yayi yaki ma amma a yau fa?ka je makarantun ka ga inda suke. Sannan banda kamar irin su Nasiru El-Rufa’i wadanda sune gaba gaba kila ko in ce tabbas a cikin tafiyar APC sannan a gomnati ko da yake shi ba zai zama a Federal Level ba tunda ya nuna yana so ya zama gomna a Kaduna amma sauran mutane wadanda suke ba Buhari shawara akwai mulahazozi akan suma akan su sosai,kaman Pastor Tunde Bakare wanda yana goyon bayan General Buhari sosan gaske sannan kwanan nan ma ya fadi cewa  ya yarda da Buhari amma bai yarda da wadanda suke kewaye dashi ba,sannan kuma yace shi tare da Buhari yake duk da yake bashi bane yake mashi mataimakin shugaban kasa ba yanzu sannan banda haka ya taba yin wani jawabi wanda aka dauka a talabijin da yake yana jawabi ana sawa a talabijin,to akwai jawabin da yayi wanda yasa aka yanke sa jawaban da yake yi a talabijin,to wannan jawabin  ya fadi abubuwa masu yawa sosan gaske masu kyau dangane da Buhari kuma ya soki Jonathan,to wannan jawabin da yayi din wanda na karanta shi gabaki daya wato daga farkon shi har karshen shi kuma ya kamata kowa ya zama,to ya SANNAFA wato ya siffata yan Hamas da Hizbullah a matsayin  kungiyoyin yan ta’adda,an gane me nake nufi a nan?Mutumin da yake da wannan Nazra din dangane da duniya da kungiyoyi da sauransu, kuma yana ganin Hizbullah da Hamas a matsayin yan ta’adda me kake tsammani in ya zama daya daga cikin masu ba Buhari shawara?wanda clearly abinda yake nufi shine shi ra’ayin sahayonan Isra’ila da kuma America akan Hamas da Hizbullah wanda wannan yana daga cikin matsalolin Jonathan.Jonathan na gaya maku shine mutum na farko shugaban kasa wanda ya tafi ziyara ta addini a Isra’ila,wannan akan shi ba laifi bane amma abinda wannan yake nufi shine cewa yana goyon bayan Netanyahu sannan Netanyahu ya kira Jonathan da FRIEND wato aboki,yaushe? a lokacin da Nigeria ta zama itace sababin kada Palastine ta zama kasa wanda wannan ba karamin ko ince gaggarimin canji ne na manufofi na kasashen waje a gomnatin Nigeria tunda aka yi ta zuwa yau.Kila wannan yasa Buhari yace gomnatin sa za ta zama PROACTIVE ba kamar yanda ta kasance a da da yanzu ba amma Jonathan ya kunyatar ya fusata ya bada mamaki ga mutanen Palastinu da Ambassador Palastinu a Nigeria wanda har lokacin karshe yana masu alkawari zasu yi voting YES ne a wurin Palastinu ta zama kasa amma a karshe lokaci,a lokacin da Netanyaho yayi ma Obama waya,Obama kuma yasa John Kerry ya kira Jonathan kawai sai aka canja,kira a waya ya sanya Jonathan ya canja Foreign Policy din Nigeria wanda yake gudana tunda Nigeria take har zuwa yanzu saboda ya hana Palastinu ta zama kasa.Wannan kila bai damu mutane ba ko?Sannan lokacin da aka kashe mutane a Baga wanda masu bincike na kasashen duniya  sun ce an kashe mutum kamar dubu 2 a Baga,Jonathan kwata kwata bai yi komai ba alal hakika ma Olukolode abinda yace wadanda aka kashe ba wuce mutum dari biyu ba amma lokacin da aka yi CHARLIE HEBDO a Faransa Jonathan ya taya mutanen Faransa bakin ciki.To in zama mutane irin su Jonathan,irin su Tunde Bakare wadanda suke da wannan ra’ayin dangane da addinin musulunci ko dangane da kungiyoyin addinin musulunci masu turjiya dangane da zalunci su suke kusa da Buhari,zaka ji tsoro ko ba zaka ji tsoro ba?wannan Empirical Evidence ne ko Emotion ko Theory?Abinda yake faruwa shine akwai yan PENTECOSTAL CHURCHES wanda wannan bai da dangantaka da gaba da addini,ina so in maku bayani tun tuni ina da wannan ra’ayin ban samu daman fadin sa ba sai yanzu.Akwai wadannan yan Pentacostal Churches din wadanda su ba ORTHODOX,CONVENTIONAL,TRADITIONAL,CONSERVATIVE ,CLASSICAL EVERYDAY CHURCHES bane,a takaice abinda nake nufi su ba cocin Katolika ba kuma cocin Anglican su ba wadannan manyan cocinan bane domin su wadannan suna da dokoki da ka’idoji haka rannan ONAYIEKAN ya taba fadi kwanan nan lokacin da PDP suka ce Buhari ya kusa ya mutu sai ya zo yace bai kamata ayi haka ba wato Cardinal Onayiekan yace a daina fadin wannan abin kuma yace PDP tayi kuskure da take wannan abin saboda ni ma shekara na saba’in da wani abu kuma na san mutumin day a kai irin wannan shekarun yana bukatan ya dinga zuwa wajen likita yana duba shi,yace zan yi mamaki ya zama Buhari ya je England ba amma bai je ya ga likita ya duba shi ba saboda shekarun mu haka suke bukata,kun ga wannan ai ra’ayi ne mai kyau.A lokacin da Pastor Mbaka wanda shi ma dan Katolika ne ya zargi Jonathan kuma yace ba zai ci zabe ba wato tamtabarar shi ba ta tashi ba,to lokacin shi Onayiekan yace abinda ya fadi gaskiya ne cocin mu daya abinda yake fadi gaskiya ne saidai kuskuren da yayi shine hukuncin da yayi day ace ka da ku zabi wannan ku zabi wannan amma zargi da gyara da sauransu duk cocin mu na yin haka.Wadanda suke ba yan katolika ba kuma ba yan Angilankan ba wato Pentecostal Churches irin NEW GENERATIONS CHURCHES  wadanda yawanci sun fi karfi ne akan asasin HEALING da sauransu su yawancin sub a sun karanta addinin kirista na asali ba a makarantu na SEMINARIES wato kana iya cewa a HAUZA a istilahin mu,kuma muna da irin wadannan a cikin addinin musulunci sune WAHABIYYAWA wadanda ba su karanta addini a Zaure ba,ba su san TRADITION ma’ana al’ada na malamta da dalibta ba da dangantaka tsakanin malami da dalibi da kuma romon da dadin dalibtaka da karatu da sanin matakai na karatu da kiman kowanne mataki bayan mataki.Sun yi kama a kiristanci da kuma a Musulunci a SULUK dinsu da APPROACH dinsu dangane da al’amura kuma su din suke haddasa masifu a cikin al’umma a duniyan mu ta yau,kuma abin takaici a yau sun fi kowa murya sannan an fi daukan su akan cewa sune malaman addini na gaskiya,a kirista suna cewa sune kirista na gaskiya sannan a musulunci suna cewa sune musulmi na gaskiya sannan a tsarin hukuma da gomnati suma sun dauke su sune masu addini na gaskiya ba wajen mutane ba.To yawancin wadannan yan Pentecostal Churches din da New Generation Churches din a cikin kirista ba duka kirista gaba daya ba suna goyon bayan akidan ZION,abinda ya kamata mutane su fahimta shine da yawa daga cikin Yahudawa ba sahayona bane sannan da yawa daga cikin Sahayona ba Yahudawa bane wato akwai mutane da yawa wadanda su ba Yahudawa bane amma suna da akidan Sahayona kamar David Cammeron da sauransu,su ba Yahudawa bane amma Zionist ne,kamar Tony Blair,kamar Bush.Kila su yi maka da’awan su kirista ne amma a akidan su zion ne sun hadu da zayoniyawa a wurin gaugauta abinda ake ce ma AMAL DEGON suna son duniya ta kare da sauri ayi yaki a tattaru a wannan wurin ayi  yaki duniya ta kare saboda su tafi aljanna wanda aljanna ta su tana cikin wannan duniyan ne wato a lokacin da duniyan ta gabaki daya sai Allah ya sake tado da zababbu su tashi a maida duniyan aljanna sai su rayu har abada.Wadannan irin cocin suna da cibiyoyin su a America kuma suna haddasa rigingimu masu yawa a cikin America din na addini yawanci yan Republican wannan Conservative suna da alaka da irin wadannan cocin na goyon bayan wannan addinin amma ba addini Traditional ban a kirista wato ba Katolika ba Angalikan ba to idan muka samu irin wadannan wadanda suke da irin wannan ra’ayin kenan yaya makomar kasar mu zata kasance a hannun General Buhari ?wannan Mulahaza ta biyu kenan. Mulahaza ta uku itace kamar su ODIMEGU da nayi magana akanshi wanda shine shugaban Nigerian Breweries Limited a da wanda yana tare da Obasanjo su suka yiwa Yar’aduwa kamfen kuma ya shiga cikin gomnatin Jonathan daga karshe da suka saba da Jonathan akan mas’alan kidaya ya fita daga cikin gomnatin ya zama mai sukan Jonathan ya zama mai goyon bayan Buhari.Shi Odimegu yana da ra’ayi akan dukkan kidaye kidaye da aka yi a Nigeria ba wanda ya inganta sannan a lokacin da yake bada UNEDITED HISTORY  na Nigeria ya nuna cewa su yan Arewa jahilai ne wadanda basu yi karatu ba kuma kauyawa sannan suna da ra’ayin BORN TO RULE ma’ana suna ganin an haife su ne don suyi shugabanci saboda haka ba zasu iya CONCEDING shugabanci ba ga mutumin da yake ba dan Arewa bane a gefe daya.A daya gefen yana ganin cewa Igbo sun girmi Nigeria sannan sun fi Nigeria muhimmanci sannan babu kabilan da ta kai Igbo a cikin Nigeria gabaki daya ilimi da wayewa da kima da komai da komai amma a lokaci guda yana da ra’ayi mai kyau kamar ya zo da shawara yanda za a iya habbaka tattalin arzikin Nigeria ba tare da an sai da digo daya na gurbataccen bakin mai ba,wannan yana da kyau wato wannan hanyar sai ya zama cewa wannan barazana na yan  Niger Delta an gama da ita.Sannan ya kawo shawarwari masu yawa kuma yana ganin ya kamata Buhari yayi shugaban kasa na shekara 8 maimakon hudu.To ya zaka iya balancing tsakanin fahimtar ra’ayin nashi mai kyau da wannan ra’ayin nashi wanda yake akan asasin TA’ASSUBANCI na kabila da kuma kila boyayyen ra’ayi na addini,ya zaka yi da wannan?kila ya zama an san inda za a tantance a warware irin su Odimegu da ire irensu masu yawa wadanda sun taimaka sosai a wurin nasaran General Buhari? Sannan kuma lokacin da yake magana akan cewa tsaro wato tabbatar da tsaron Nigeria da iyakokin Nigeria da sauransu wannan din yana nufin cewa shi Buhari a yakin da yake so yayi dangane da ta’addanci sai shiga cikin gungun silsilan kasashen da suke yaki da ta’addanci a duniya gabaki daya ya zama cewa bay a takaita kansa a Nigeria kawai ba?a wata IBARA daban gomnatin Nigeria da kuma rundunar sojan Nigeria karkashin Buhari za ta zama cikin jerin sojojin America ne a Africa wato AFRICA  COMMAND wanda America ta kafa cikin Africa domin ta yi yaki da yan ta’adda,to Buhari zai sanya General din sojan Nigeria a karkashin General din da yake tafiyar da wannan rundunar ta America ne?Sannan wata rana zai aika da rundunonin Nigeria Libya su yi yaki ko Somaliya su yi yaki?suna yakan Shabab ko suna yakan Al-ka’ida ko abinda yayi kama da wannan ko ba zai yi ba wato zai INTERNATIONALIZING din sojojin Nigeria ko ba zai yi ba a wurin yakin da America take yi da abinda take ce ma  ta’addanci ko bai zai yi ba?wadannan sune tambayoyi ba kawai murna don Buhari ya ci zabe,murna yana da kyau saboda Buhari an kwada shi an gani kuma a cikin PACK din gabaki daya ba wanda ya kaishi inganci da mutumci,to amma wadannan eriyoyin ya yake so yayi mu’amala dasu. RA’AYOYIN MU KO SHAWARA Kamar yana da muhimmancin gaske ya cewa da gaggawa idan suka amshi mulki kuma tabbas zasu amsa to ya kamata ya zama cewa dukkan wadanda suka taba yin alaka da gomnatin yanzu ta Jonathan tare da INTIQALI da irin abinda da Jonathan yayi ko yaudaran mutane ya zama kwata-kwata babu daya cikin su da zai tafi tare dasu a gomnatinsa,wannan zai nuna kila da gaske ake ba siyasa ake bad a sauransu. Bai kamata mutane su yaudari kansu da yadda da kayi da Jonathan yayi ba,yana da kyau abinda Jonathan yayi sannan yana da kyau day a zama bai ja ba amma wannan bai warware dukkan ababen da yayi kafin wannan ba.Sannan kuma me yasa ya yarda ya amshi kayi?wannan yana bukatan bincike,ya yarda ya sha kayi saboda ba inda zai yi ne  kuma zai yiwu haka saboda kila ya tabbatar da abinda zai iya yi ne domin zaben kiri-kiri yake kowa ya gani a faifai aka sa shi,sakamakon na hannayen kowa kuma canja shi zai wahala idan bamu ce ba zai yiwu ba,kila wannan ne yasa yace yarda an kada shin a daya kenan.Na biyu kuma shine ya yarda ya sha kayi ne saboda dabarun da suka so suyi amfani dasu ta bayyana masu basu iya amfani dasu ba kamar juyin mulki,kila sunyi ma rundunonin sojojin tayi na suyi juyin mulki amma suka ki da dalilin cewa kila duniyan yanzu ba duniyar juyin mulki bace,idan aka yi juyin mulki a Nigeria sai zama wadanda zasu amshi mulkin kamar sun rike garwashin wuta ne saboda haka suka ji tsoro ba su yi juyin mulki ba kuma mutanen Nigeria ba  zasu yarda ba,anan wurin kila in dan matsa kadan in yi magana akan Dimokradiyya kamar babu kyau ko Aqida ce ko Addini ce ko yaki da Musulunci ce,to ya danganta da yanda mutum ya dauke ta ko ya kalle Dimokradiyya dinne.Kuskure babba da mutane suke yi shine dangane da mas’alan Kalmar Dimokradiyya shine dauki Dimokradiyya a matsayin akida basu kalle ta a matsayin wasila zuwa ga akida ba.Dimokradiyya ba tsarin mulki bane tsari ne na kaiwa ga shugabanci wato mun yarda akan cewa shugabannin mu zasu zama ta hanyar kada kuri’a shine Dimokradiyya amma ta ayyana maka ya gomnatin zata kasance?Dimokradiyya tana yi ko bata yi?ba tayi saboda cewa take yi ra’ayin wadanda suka fi rinjaye shine yake tafiyar da kasa sannan a kiyaye hakkokin wadanda ba sune suka fi rinjaye ba,to wadannan wadanda suka fi rinjaye menene ra’ayinsu?shine ke tafiyar da kasa,ina fatan an gane? Wato abinda ake cema NATIONAL WILL ma’an kudurin kasa shine Dimokradiyya ta yanda zai tafiyar da kasa,to kudurin kasar menene shi?shine al’adun mutanen kasan,addinin su da sauransu,in da gaske suka taso su mutanen kasan wato Majority din suka ce kaza za a yi shi za a yi ko bashi za a yi ba wannan in an fitar da doka daya yanda aka yi da’awa take akan asasin kaddarawa dimokradiyyan ana aiwatar da ita yanda aka yi da’awan take,kuma wannan shike muhimmanci  akan cewa kuri’a ke da tasiri kuma idan ya zama da gaske mutane suna da tasiri to lokacin zai iya yiwuwa kudurin kasa ya zama kudurin kasa ya zama kudurin wadanda suka fi yawa,suma wadanda suka fi yawan ya danganta shi yasa ita Dimokradiyya ake ce mata NOUN wato Ismi ne amma tana da KAIDOJI masu yawa,shi wannan KAIDIN ya zuwa ne akan asasin menene kudurin mutanen kasan.Idan kana magana akan LIBERAL DEMOCRACY ne,sai muce wannan tana da matsala saboda ita akida ce,ta tafi akan fifita ra’ayin mutum SHAKSI akan mutanen kasa gabaki daya.Sannan akwai masu cewa Dimokradiyya itace tunanin mafi inganci da dan Adam ya taba yi kuma ta zo ne saboda ta kashe addini kai ta ma yi maganin addini akwai masu wannan ra’ayin kaman FRANCIS  FUKUYOMA a cikin littafinsa mai suna THE END OF HISTORY ko IDEALOGY yana da wannan ra’ayin amma way ace ma Francis Kukuyoma shine kawai ra’ayi a cikin duniya.Dimokradiyya tana kaidoji masu yawa,akwai CHRISTIAN DEMOCRATS,da SOCIAL DEMOCRATS,da LIBERAL DEMOCRATS,akwai Democrat kala daban daban sannan akwai ISLAMIC ko MUSLIM DEMOCRATS kamar abinda yake faruwa jamhuriyyar musulunci ta Iran da wasu kasashe wanda mutum zai iya bada misali.A takaice Dimokradiyya ba akida bace wasila ce zuwa ga Akida da tafiyar da kasa,yana da kyau a bambamce tsakanin wadannan guda biyun. To yana da muhimmanci a gane haka cewa dukkan wadanda suka yi tarayya a wancan gomnatin dole ya zama cewa ba daya daga cikin su wanda yayi saura wato ya rage saboda mutane suna da hankali kuma suna da wayau,wannan raina mutane da aka yi a da ya bayyana akan cewa rainin yana da farashi kuma yana da tsada sosai musamman idan kuri’an zata yi aiki saboda haka idan ya zama babu kowa daga cikin su mutane zasu ga da gaske ne. Sannan ban da haka kuma yana da muhimmancin gaske wadanda za a sa wato sababbi su zama mutane wadanda suke masu mutumci.Akwai tattaunawa da ake yi a tsakanin al’umma akan cewa matasa ya kamata su zo suyi shugabanci ko tsofoffi na da,wannan bai da muhimmanci sosai ya danganta da matasan me zasu yi sannan na dan me zasu yi saboda haka ba zaka jefar da wadanda suke da gogayya a da amma abinda yake da muhimmanci shine ya zama cewa akwai wani tsari wanda za a dinga tarbiyyantar da matasa su zama suna tafiya mataki mataki har su kai inda ake so su kai a matakan gogayya wato ya zama akwai tsari na gadon tafiyar da kasa wanda babu shi a Nigeria,abinda yake akwai a Nigeria shine FAVOURITISM,da GODFATHERISM da sauransu wanda wannan shine ya rusa dukkan tsare tsaren da hana kasa ta zama kasa ba wai tsofoffi ko yara ba domin ko yaran ka sa idan suka zama yaran wadancan lalattattun me kake tsammani?za suyi lalattattun abubuwa ne saboda ba shine yake da muhimmanci ba abinda yake da muhimmanci shine bin ka’idoji da tsaren tsaren da suke an yarda dasu. Akwai ababe masu yawa wadanda mun bar su ko mun kai da kai daga barin su saboda dalilai amma zamu cigaba da bibiyan ababen da suke faruwa din kuma ya kamata mutanen mu su san wannan ya zama cewa su ma suna kallon kome da kome saboda irin wannan mustawa din ta tunani sannan su zama cewa abubuwan da suke faruwa a cikin kasan sun dame su kuma suna bincike akan su,sannan su daukan akan cewa suna da ra’ayi akan al’amarin kasa sannan za su iya canja wa,mutanen da ake ganin suna da ra’ayi akan kasa kuma suna da tasiri a cikin kasan bas u fiku komai ba a wasu lokuta kun fi su tunani da tsari da sanin abin day a kamata kawai yanayin ne ya dankofar da mutane yasa suke tsammanin sub a kowa bane wato yanayi ne ISTIKHAFFA QAUMAHU FA ADA’UH ….ma’ana sai Fir’auna ya raina mutanen sa ya wulakanta su da suka ji wannan INFERIORITY a cikin zuciyar su,wannan yanayin ya kamata ya canja mutane su ji su INFERIOR suke ba sannan makomar kasa na hannunsu ne. Wadannan abubuwan da muke yi ko da muka faro su yanzu mun ce sune tsare tsare da muke yin a gine gine da sauransu su suka sanya mu muka zo mataki na matsakancin zango a shirin da muke dashi a wannan al’umman da muke cikin ta,akwai ababe masu yawa da zamu yi a wannan zango fiye da da wato a lokacin da muke mataki na gajeren zango sannan wannan matakin shine zai tafiyar damu zuwa ga mataki na dogon zango,muka ce akwai  short term da medium term da kuma long term akwai ma longer term wato bayan long term wanda bamu taba fadi ba akwai longer term saboda haka mutane su dinga bude idanunsu kuma su dinga bincike suna TAHLIL wato warware abubuwa ,kada ku dinga bin yarima domin ku sha kida,ka da ku dinga bin wadanda basu cancanta suna maku tasiri a ra’ayi ko a mataki wanda kuka dauka ko kuke dauka ko zaku dauka,sannan ayyukan da kuke yi na tattaro ma’alumat da bamu su da abubuwa masu yawan gaske wadanda kuke yi masu amfani saboda haka ku daina yadda wasu su yaudare ku ko su ja ku ko kuma su dinga yi ma ku tunani,ku dinga yin tunani da kanku domin ba abin da ba zaku iya yi da kanku ba a lokacin rayuwanku na yau da kullum mutane na kallon ka amma kuma kai kadai ka san abinda kake yi,kana farin ciki kana bakin ciki tare dasu a lokacin kai kadai kuma akwai abinda kake yi wanda su kuma basu sani ba wato BACKGROUND ayyuka,wannan shi ke gina mutum da tarbiyantar dashi ya Saqqafa mutum,da a ce haka mutane suke yi da abubuwa basu zama yanda suke ba,zaka ga mutane abinda suke yi suna shiga social network amma don ababen da suke da kyau ba sannan sun gommace a wajen social network su karatar da rayuwar su a waqa da kida da drama.Akwai abubuwa masu yawan gaske basu da amfani a cikin wannan duniyan da aka samu amma sai in kana so ko kuma in ka bi ta hanyar da ta dace. Allah subhanahu wa ta’ala ya taimake mu ya kuma sa mu dace ya taimake ita kasar ya sa ta akan shiriya sannan  Allah yak are mu daga masifu da fitun tinu da makirce makirce wadanda muka sani da wadanda bamu sani ba wadanda ake kullawa dangane da mu.Muna fata Allah subhanahu wa ta’ala ya cigaba da tunkude mana irin wadannan ababen wadanda wani lokacin sukan fi karfin mu kamar yanda ya tunkude mana wadancan bad a karfin mu ba. WASAL-LAHU ALA MUHAMMADIN WA ALIHID DAYYIBINAD DAHIRIN.ABNA