A yau (Alhamis) ne majalisar dokokin kasar Lebanon ta kasa
zaben shugaban kasa, inda babu wani dan takara da zai iya samun kashi biyu bisa
uku na kuri'un wakilan.
Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na AhlulBaiti (As) -ABNA- ya habarto maku bisa nakaltowa daga shafin labaran ISNA cewa: a taron na yau, babu ko daya daga cikin sunayen da wakilan suka gabatar da ya samu kuri’u 86, adadin kuri’un da ake bukata ga kowane dan takara domin shiga fadar Baabda a zagayen farko.
A zaben na yau, Kwamandan Sojin kasar Joseph Aoun ya samu kuri’u 71 shi kuma Shibli El-Mallat ya samu kuri’u 2. Har ila yau, an jefa kuri'u 37 da ba komai aciki, an samu kuma kuri'u 4 marasa inganci, yayin da wakilai 14 suka jefa takarda mai dauke da rubutun "Hukuncin Doka" a cikin akwatin zabe.
Shugaban majalisar dokokin Lebanon Nabih Berri ya dage zaman zaben shugaban kasar na tsawon sa'o'i biyu.
Taron na yau na majalisar dokokin Lebanon ya gudana ne a karkashin jagorancin shugaban majalisar Nabih Berri, tare da halartar wakilai 128 da jakadu daga kasashen Larabawa da na kasashen waje.
A ranar 1 ga watan Satumban shekarar 2022 ne dai wa'adin doka na zaben sabon shugaban kasar Lebanon ya fara, kuma ya ci gaba har zuwa ranar 31 ga watan Oktoba na wannan shekarar, amma kasar ta Lebanon ta shiga cikin wani hali na shugaban kasa sakamakon rashin cimma yarjejeniyar siyasa ta zaben shugaban kasa kafin karshen wa'adin mulki na shari'a, kuma wannan rashin shugabanci ya ci gaba har inda yau ta ke.
A bisa doka, za a gudanar da zaben shugaban kasa da kashi biyu bisa uku na daukacin 'yan majalisar, wanda ya kunshi wakilai 128, wato wakilai 86 a zagayen farko na jefa kuri'a, kuma da gagarumin rinjaye na 65 na wakilai a zagaye na biyu.