Jagoran juyin juya halin Musulunci: Ina hasashen cewa, bullar wata kungiya mai karfi ma za ta faru a kasar Siriya
Matasan Siriya ba abin da ya ke da shi da zai rasashi. Jami’ar su ba ta da aminci, makarantarsu ba ta da aminci, gidan su ba ya da aminci, hanyoyinsu ba da aminci, rayuwarsu ba ta da aminci, me ya kamata su yi kenan? Dole ne su tsaya da karfi da azama a gaban wadanda suka tsara wannan rashin tsaro da wadanda suka aiwatar da shi, kuma in sha Allahu za su ci nasara a kan su.
Goben yankin zai fi na yau kyau da yardar Allah. Sau da yawa sukan ce Jamhuriyar Musulunci ta yi asarar wakilanta a wannan yanki!
Wannan shima wani kuskure ne da suke yi! Jamhuriyar Musulunci ba ta da sojojin haya. Yaman tana yaki ne saboda tana da imani; Hizbullah tana yaki ne saboda karfin imani ya kawo ta fagen; Hamas da Jihad suna yaki ne saboda imaninsu ya tilasta musu yin haka.
Su ba sa wakiltar mu. Idan muna son yin aiki wata rana, ba ma buƙatar sojojin haya...
Shirin Amurka na mamaye kasashe daya ne daga cikin abubuwa biyu: ko dai haifar da zalunci ko kuma hargitsi.
Sun haifar da hargitsi a Siriya kuma yanzu suna ganin sun ci nasara, Wani Ba'amurke a sakaye ya ce za mu taimaki duk wanda ya haddasa fitina a Iran; Wawaye sun ji kamshin tsire!
Al'ummar Iran za su tattake duk wanda ya yarda da 'yan amshin shatan Amurka a wannan fagen. Na ce kimanin makonni biyu ko uku da suka gabata a cikin wani jawabi a nan cewa shirin Amurka na mamaye kasashe daya ne daga cikin abubuwa biyu: ko dai a samar da gwamnatin kama-karya, su je su yi tafiya da iki tare da shi, su tattauna, su raba muradu tsakaninsu. su raba anfanun kasar a tsakaninsu.
Idan hakan bai faru ba, su haifar da hargitsi, tashin hankali. Sun haifar da tashin hankali a Siriya; Sun haifar da hargitsi. Yanzu haka Amurkawa, da gwamnatin Sahayoniya, da wadanda ke tare da su, suna ganin sun yi nasara; Suna jin cewa sun yi nasara' don haka sun fada cikin wuce gona da iri. wanda siffar mutanen Shaiɗan haka ta ke, lokacin da suka ji cewa sun yi nasara, harshensu ya fita daga hannunsu, su yi fadi abunda ya ba haka ba, su yi ta maganar banza. A yau, waɗannan sun fada cikin maganar banza.
Wani Ba’amurke a cikin jami’an Amurka, daya daga cikin wuce gona da iri shi ne cewa ya ya: “Za mu taimaki duk wanda ya tayar da hankali a Iran”; Jimlar maganarsa ita ce; Bai fayyace wannan ba karara ba, amma maganarsa ita ce; Ya fada a cikin kinaya, amma a fili yana fadin haka ne. Wawaye sun ji warin tsire! Batu na farko shi ne cewa al'ummar Iran za su tattaka duk wanda ya yarda da sojojin haya na Amurka a wannan fagen.