Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

13 Disamba 2024

18:34:51
1513489

Salon Rayuwar Ahlul Baiti Bayyana Soyayya Ga Yara A Cikin Tarihin Imam Husaini As

Soyayyar 'ya'ya abu ne na boye wanda Allah ya ajiye shi a cikin zukatan iyaye, amma abin da yake da muhimmanci a cikin wannan lamari kuma yake da tasiri a cikin tarbiyya shi ne bayyana soyayya.

Soyayyar 'ya'ya abu ne na boye wanda Allah ya ajiye shi a cikin zukatan iyaye, amma abin da yake da muhimmanci a cikin wannan lamari kuma yake da tasiri a cikin tarbiyya shi ne bayyana soyayya.

Imam Husaini (a.s.) a matsayin abin koyi kuma cikakken abin dogaro, yana daukar soyayya ga yara a matsayin daya daga cikin muhimman bukatu kuma yana bayyana ta ta fuskoki daban-daban. Wani lokaci ta hanyar rungume ko daukar yara da rungume su kirjinsa, wani lokaci ta hanyar sumbata, wani lokacin kuma ta hanyar fadin kalmomi masu dadi da soyayya.

Ubaidullah bin Utbah yana cewa: “Ina kusa da Husaini bn Ali (a.s) sai daya daga cikin ‘ya’yansa ya shigo. Imam Hussain (a.s.) ya rungume shi ya manne shi a kirjinsa ya sumbace shi a tsakanin idanuwa biyu.

Majma' Al-Bahrain fi Manaqib al-Sabbatain, shafi na 404.