Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

30 Afirilu 2024

11:25:22
1455231

Za A Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na "Nazarorin Kur'ani A Wajen Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci" A Birnin Qum.

Shugaban Jami'ar Ilimin Musulunci ya bayyana cewa: A gobe Laraba ne za a gudanar da taron nazarorin kur'ani na kasa da kasa na Ayaullah Khamenei a dakin taro na shahid Sulaimani da ke jami'ar ilmin addinin musulunci ta birnin Qum.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA - ya kawo maku rahoton cewa: babban sakataren kimiyya na taron kasa da kasa kan nazarin kur'ani na Ayatullah Khamenei, Hujjatul-Islam Wal-Muslimeen, Dr. Muhammad Ali Rezaei Isfahani, ya yi ishara a taron manema labarai game da gudanar da wannan taro na kasa da kasa a birnin Qum, ya yi ishara da ranar da taron kasa da kasa kan nazarorin kur'ani na Ayatullah Khamenei ya bayyana cewa: An fara taron ne a shekara ta 2022, kuma a shekara ta 2023 na taron an fara gudanar da ayyuka da muhimmanci Muhimmin burin wannan taro shi ne yada kur'ani mai tsarki.

Ya ce: Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i ya fara tafsirin kur'ani ne a shekara a 1964, kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci yana da mujalladi guda goma na tafsirinsa. wanda matasan zamani ba su san shi ba, kuma taron nazarin kur'ani na Ayatullah Khamenei ya zo ne domin gabatar da ra'ayoyinsa a ciki da wajen Iran. Ana daukar wannan taro a matsayin taro mafi girma a tarihin kasar Iran Sakatariyar taron ta samu makaloli kimanin 1,900, daga cikinsu an amince da 609. Mujallolin kimiyya 50 sun sanar da aniyarsu ta buga makalolin, kuma an gudanar da taron bita na rubuce-rubuce 72 da kujerun tallata kimiyya 18 a gefen taron.

Babban sakataren taron kasa da kasa kula da harkokin ilimin kur'ani ta kasa da kasa Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Ba wai ana gudanar da wannan taro ne a rana daya ko wuri guda ba, a'a taron yana da manufar kafa tubalai na tafsirin kur'ani mai tsarki a kasar. Don haka, an ɗauki matakan gudanar da taruka da yawa don shi, kuma an buga kusan juzu'i 13 na tarin makalolin taron. Nan ba da dadewa ba za a gabatar da wasu makalolin a yaren Istanbul na Turkiyya da Azabaijan don halartar taron nazarorin kur'ani da Ayatullah Khamenei ya yi a taron Tabriz, kuma za a buga tarin makalolin da ba na Farisa ba na wannan taro a juzu'i da dama.

Sha'awar Matasa Ga Tafsirin Alkur'ani Na Jagoran Juyin Juya Hali

Shugaban Jami’ar Ilimin Musulunci ta Hujjatul-Islam Wal-Muslimeen, Dakta Ruhullah Shaakiri, ya yi ishara da manufar wannan jami’a, inda ya yi bayanin cewa: Manufar jami’ar ilmin addinin Musulunci ita ce ta samar da kwararrun jamiai don koyar da darussa ilimin addinin Musulunci a jami'o'i, da kuma rubuta binciken ilimi daga daliban Jami'ar Ilimin Musulunci Jami'ar a matakin digiri na farko.

Ya ci gaba da cewa: Mun shafa’a da sanin waye jagoran juyin na ilimi da gaske, kuma darussan kur'ani na jagoran juyin juya halin Musulunci kafin nasarar juyin juya halin Musulunci sun shahara a wurin matasa, kuma idan har za mu iya fitar da nazarorin kur'ani daga tafsirin Ayatullah Khamenei to daliban jami'a zasu nuna sha’awarsu kan wadannan nazarori wanna zai kasance babu makawa akai. Kafin haka, nazarorin jagoran juyin juya halin Musulunci sun shahara a jami'o'i, kuma nazariyyarsa na iya zama batutuwan bincike da karatun digiri da na uku.

Shugaban Jami'ar Ilimin Musulunci ya bayyana cewa: Malaman ilimin addinin Musulunci suna tattaunawa da dukkan daliban jami'a, kuma idan har malaman suka zurfafa a kan abin da ya shafi tafsirin kur'ani na Ayatullah Khamene'i, za su iya samun nasarar isar da wadannan nazarori ga daliban. Don haka ne aka kafa wani kwamiti na musamman tare da malaman jami'ar ilmin addinin Musulunci don gudanar da wani taro kan rnazarorin kur'ani da Ayatullahi Khamene'i ya yi, kuma a kan haka ne muka gudanar da tarukan da dandali sama da 14 don gabatar da takardun makaloli a wannan taro. Kimanin makala 200 na malaman addinin muslunci na jami'o'in kasar ne suka isa wurin taron, yayin da fiye da 70 daga cikinsu suka samu karbuwa taron, wanda zai kasance cikin mujalladi biyar karkashin taken Gungun makalolin Taron Nazariyar Alkur’ani A cikin Tafsirin sayyid Ali Khamna’ei, Za a gabatar da makalolin ne a ranar da ake gudanar da taron a birnin Qum, kuma za a gudanar da wannan taro a gobe Laraba a matakai biyu na safe da yamma a dakin taro na shahidan Sulaimani da ke Jami'ar Ilimin Musulunci.