Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

30 Afirilu 2024

07:31:42
1455194

Annabi Muhammad Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A Gare Shi Da Alayensa: Mafi Kyamar Halittu Ga Allah Guda Su Uku Ne:

Annabi Muhammad Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A Gare Shi Da Alayensa: “Mafi kyamar Halittu ga Allah guda uku ne: Mutumin da yake yawan yin barci da rana, ba tare da yayi salla ko yaya take ba da dare, da mutumi mai yawan cin abinci ba tare da yana anbaton sunan Allah ko gode masa a abincinsa ba, da mutum mai yawan Dariya da yawa ba tare da wani abun mamaki ba; domin Yawan dariya yana kashe zuciya kuma yana haifar da talauci’’. Riwayar Al-Dailami’ Kanzul-Ummal: 7/791/21431.