Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

14 Afirilu 2024

03:44:47
1451108

Labarai Cikin Hotuna Da Bidiyo Na Yadda Harin Ruwan Makaman Da Iran Ta Kaiwa Isra'ila A Daren Jiya

Kamar yadda kafofin yada labarai suka nuna dumbin jiragen Iran marasa matuka a sararin samaniyar duniya ne jiya suke yawo tare da nufin ƙasar Isra'ila da shalkwatar Tal Aviv wanda wannan harin yana a matsayin maida martani na kaiwa Iran hari da Isra'ila tayi a ofishin Jakadancinta da ke Siriya kwana goma da suka wuce.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: A daidai lokacin da Iran ta kai hare-haren jiragen sama marasa matuka, da kuma harin makami mai linzami da rokoki, anata buga tare da watsa faifan bidiyoyi daga sararin samaniyar Tel Aviv da sauran garuruwan da Isra'ila ta mamaye.

Inda Jiragen yaki marasa matuka sun shiga yankunan da aka mamaye dama kanta cibiyar ta Isra'ila wato Tel Aviv kuma suka yi nasarar samun hadafin da aka harba makaman saboda su.


Kamar yadda Kafofin yada labaran Isra'ila sun sanar tare da tabbatar da cewa jiragen Iran marasa matuka sun shiga sararin samaniyar Isra'ila.

A sa'i daya kuma, masu lura da al'amuran yau da kullum na ganin ko Isra'ila tayi yunkurin sauke tare da kame wasu jiragen ko kuma adadin asarar ta ragu, to lalle Isra'ilawa za su ji raunana matuka.

Dangane da haka, kakakin rundunar sojin Isra'ila ya ce: Muna gargadin cewa ba za mu iya dakatar da dukkan jirage marasa matukan ba.

Sannan kungiyar Hizbullah ta fara nata ruwan rokokin da makamai a yankunan da Isra'ila ta mamaye a yayin da Iran ta fara kai farmakin jiragen yaki marasa matuki, kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ita ma ta fara kai hare-haren makamai masu linzami da rokoki kan gwamnatin sahyoniyawa.

A wannan rahoton zaku iya ganin Guguwar makamai masu linzami da Iran ta harbawa gwamnatin sahyoniyawan a sararin samaniyar kasar Iraki inda suke wuce zuwa Isra'ila.

Har Wala yau rahotan yana dauke da yadda Falasdinawa suka karya katangar da ke tsakanin yankunan Falasdinawa da matsugunan Beit Iel a daren jiya.

Shaban Yizlon, kofar katangar mulkin wariyar launin fata a yankin Beit El wani matsuguni ne a lokacin da suka mamaye mazauna, kusa da sansanin Al-Jalzoon, a arewacin Ramallah.

Inda a yammacin gabar kogin Jordan Falasdinawa sun karya shingen da ke tsakanin yankunan Falasdinawa da garin Beit Iel.

Akwai kuma Hotuna da bidiyo na harin farko jiragen Iran marasa matuka da suka kai Tel Aviv.