Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

13 Afirilu 2024

21:05:04
1451052

Iran Ta Fara Kai Wa Isra’ila Hari Da Jirage Marasa Matuka.

Tashar Al-Arabiya ta rubuta cewa: Bisa kididdigar da aka yi a fannin tsaro, an harba jirage marasa matuka masu yawa daga Iraki da kuma yiwuwar daga Yemen zuwa Isra'ila. Har ila yau, mayakan na Isra'ila sun kara yawan jiragensu a kan iyakar Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Dan jaridar Axios Barak Ravid ya rubuta a shafinsa na twitter cewa: Jami’an Amurka da Isra’ila hudu sun shaida min cewa Iran ta kai wa Isra’ila hari da jirage marasa matuka.

A daya hannun kuma, firaministan kasar Isra'ila ya sanar a cikin wani sako da aka nada cewa, tsarin tsaro na wannan gwamnati a shirye suke don fuskantar kowane irin yanayi, tsaro ko hari.

 Hakan Tashar Isra'ila ta 12 ta ce: Iran ta harba jiragen kunar bakin wake 30 zuwa Qasrin da Safad!

 Tashar talabijin ta Sahayoniyya ta 12 ta sanar a cikin wani labari na gaggawa cewa: A karon farko Iran ta kai wa Isra'ila hari kai tsaye daga kasarta. 

Haka suma Jami'an Isra'ila sun tabbatar da fara kai harin na Iran

Hukumar Gidan Rediyo da Talabijin ta Isra'ila ta rubuta cewa: Mahukuntan Isra'ila sun tabbatar da fara kai harin na Iran inda suka harba jirage marasa matuka zuwa Isra'ila.

 Sannan Gidan rediyon sojojin yahudawan sahyoniya ya ambato wasu majiyoyi: Harin na Iran ya fi yadda muke zato.

Sannan akwai wani sabon harin makami mai linzami kan Al-Jalil

Majiyoyin labarai sun ba da rahoton wani sabon harin makami mai linzami zuwa Isba al-Jalil da ke arewacin Falasdinu da ta mamaye.

Nan da 'yan sa'o'i kadan jiragen Iran marasa matuka za su isa Isra'ila

A cewar tashar talabijin ta gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila 12, jirage marasa matuka na Iran za su isa yankunan Falasdinawa da ta mamaye.

  Jiragen yaki marasa matuka na Iran sun tsallaka sararin samaniyar lardunan Al-Nasiriya da Maysan na kasar Iraki

  Majiyar tsaro ta Al-Arabiya ta sanar da cewa jiragen yakin Iran da aka harba zuwa Isra'ila sun tsallaka sararin samaniyar lardunan Nasiriyya da Maysan na kasar Iraki.

"An harba makamai masu linzami masu cin dogon zango da dama daga Iran zuwa Isra'ila."

Kafofin yada labaran Isra'ila sun sanar da cewa: An harba makamai masu linzami masu cin dogon zango da dama daga Iran zuwa Isra'ila.