Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

11 Afirilu 2024

17:04:47
1450649

Matanin Wani Saurayi A Yayin Zaman Majalisar Dattawan Amurka

Bidiyo: Hannuwanku Sun Yi Dumu-Dumu Da Jinin Al'ummar Palastinu

Ikirarin da sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin ya yi a zaman kwamitin majalisar dattawan kasar game da rashin samun hujjoji kan kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Gaza ya kawo cikas ga taron.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Daya daga cikin masu zanga-zangar da suka halarci taron ya yi kira da babbar murya cewa Kai da gwamnatin Amurka kun yi dumu-dumu da hannayenku da jinin al'ummar Gaza. 

A wani bangare na taron, wani mai goyon bayan Falasdinu ya katse jawabin Austin, ya kuma ce wa gwamnatin Amurka: “Ku Kawo Karshen Kashe Mutanen Gaza. Ya Isa Hakanan, 'ya'ya nawa ne za su mutu don ku gamsu"?.