Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

11 Afirilu 2024

16:28:38
1450646

Adadin Shahidai A Gaza Ya Kai Mutane Dubu 33 Da 545

Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa a cikin sa'o'i 24 da suka gabata sojojin mamaya na yahudawan sahyoniya sun aikata kisan kiyashi a yankuna daban-daban na Gaza, wanda a sakamakon haka wasu Palastinawa da dama suka yi shahada.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: A cikin sa'o'i 24 da suka gabata an kai shahidai 63 da kuma wasu 45 da suka samu raunuka zuwa asibitoci sakamakon ci gaba da hare-haren da gwamnatin Sahayoniyya ke yi a zirin Gaza. Ya kamata a lura cewa har yanzu wasu daga cikin shahidai da wadanda abin ya shafa suna karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna kuma ‘yan mamaya na hana a ba su agaji.