Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

10 Afirilu 2024

18:12:11
1450512

‘Ya’yan Shugaban Hamas Uku Da Jikokinsa Sun Yi Shahada َA Harin Da Isra'ila Tai Kaiwa Motar Da Suke Ciki

Sa'a guda da ta wuce, uku daga cikin 'ya'yan Ismail Haniyeh, shugaban ofishin siyasa na Hamas, da wasu jikokinsa sun mutu a wani harin da Isra'ila ta kai kan motarsu a yammacin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: "Mohammed", "Amir" da "Hazem" sune sunayen 'ya'yan Haniyeh da suka yi shahada a wannan aika-aika tare da jikokinsa da dama.

Ismail Haniyeh: Ina alfahari da shahadar 'ya'yana

A nasa martanin farko game da shahadar ‘ya’yansa da jikokinsa a Gaza, Ismail Haniyeh shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas ya ce: “Ina godiya ga Allah Madaukakin Sarki da wannan karamci da daukakar da ya yi mana, da ya ba mu ni’imar shahadar ‘ya’yana da jikokina."

Da irin wadannan jini da radadi ne muke gina makoma da 'yancin al'ummar Palastinu da manufar Palastinu da al'ummar musulmi.