Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

5 Afirilu 2024

15:08:06
1449269

Rahoton Yana Ɗauke Da Hotuna Da Bidiyon Yadda Sojoji Suka Harbo Masu Muzahar

Sojojin Najeriya Sun Buɗe Wuta Akan Masu Muzahar Nuna Goyon Bayan Falasdinawa A Ranar Qudus Ta Duniya

Yau Juma'ar karshe a watan Ramadan sananniyar rana ce da ake gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan al'ummar Palasdinawa a duk fa'din duniya.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa kamar kowace shekara, bana ma a Nijeriya, an yi a birane sama da 20 da safiyar Juma'a, koina an yi lafiya an tashi lafiya, Amma banda cikin kwaryar garin Kaduna, inda jami'an tsaro suka bude wa masu zanga zangar Muzahar nuna goyon bayansu ga al'ummar Palasdinawan wuta. 

Rahotonni sun tabbatar da sun harbi gomomi, yayin da wasu da suka kai kimanin mutum hudu zuwa biyar sukai shahada, sauran kuma sunanan rai a hannun Allah. 

Bayan sallar Juma'a ma anci gaba da gudanar da gangamin goyon bayan Palasdinawa da Allah wadai da Isra'ila a sauran biranen Nijeriya, ciki har da babban birnin Tarayya, Abuja.