Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

5 Afirilu 2024

08:29:30
1449159

Al-Houthi: Batun Falasdinu Ba Batun Ne Da Ba A Sassauci Akan Shi Ba...

Za A Gudanar Da Ranar Qudus Ta Duniya A Wannan Shekara A Yanayi Na Musamman

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: A karshen jawabin nasa, Sayyid Abdulmalik al-Houthi ya ce: Ba za a iya sassautawa ko tattaunawa akan batun Palastinu ba, domin kuwa masallacin Al-Aqsa shi ne kan gaba wajen wannan batu. Al'ummar musulmin Palastinu da ake zalunta, wadanda ke cikin wannan al'ummar, sun shafe shekaru da dama suna fama da Ta'addancin da Isra'ila ke yi akansu.

Haka nan kuma ya ce ya kamata al'ummar musulmi su sauke nauyin da ke kansu na addini a kan Palastinu, tare da hana wasu mutane yin watsi da batun Palastinu da kaucewa hakan. Abokan sahyoniya-Yahudawa makiyin dukan al'ummai ne.