Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

4 Afirilu 2024

17:54:03
1449098

Tarihin Imam Amirul Muminin (A.S.) Daga Wilaya Zuwa Shahada

"Ya Manzon Allah ka isar da abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, idan kuma ba ka aikata ba, to baka isar da sakonsa ba Allah zai kareka daga mutane domin Allah baya shiriyar da mutanen da suke kafirai".

Imam Ali (a.s) yana da laƙubba da dama, wanda ya fi shahara a cikinsu shine "Abul Hasan". Sauran laƙubbansa kuwa su ne Abu al-Hussein, Abus -Subtain, Abul-Raihantain da Abu Turab.

                Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya kawo maku tarihin Imam Ali As. Amirul Muminina Ali bin Abi Talib (a.s) shi ne limamin ‘yan Shi’a na farko, dan uwan Annabi Muhammad (SAW), mijin Sayyidah  Zahra (A.S) kuma baban Imam Hasan da Imam Husaini (a.s) Shine mutum na farko da ya yi Imani da Annabin Musulunci, kuma ya kasance masoyi kuma mai taimakon Manzon Allah (sawa). Kuma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya nada Sayyidina Ali As a matsayin magajinsa da umurnin Allah, ya karba masa mubaya’a daga mutane; Amma bayan wafatin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) a shekara ta 11 bayan hijira, wasu daga cikin Muhajirai da Ansar sun bijire wa wannan umurni a wani lamari da aka fi sani da waki’ar Saqifa, inda suka yi mubaya’a ga Abubakar a matsayin halifan Musulmi. Wannan lamari ya sa Imam ya kai ga halifanci a shekara ta 35 bayan Uthman. Zamanin Imamancinsa gaba daya ya kasance cikin rikici da Mu'awiya da Ma’abuta Jamal da Khawarij daga karshe ya yi shahada a shekara ta 40 bayan hijira yana da shekaru 63 a hannun wani Bakhawarijeh mai suna Ibn Muljam Muradi.

Haihuwarsa:

                Mahaifinsa shi ne Abu Talib, baffan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) kuma mahaifiyarsa ita ce Fatima bint Asad, dukkansu sun fito daga tsatson Bani Hashim ta kabilar Quraishawa a Makka. An haifi Ali dan Abi Talib shekara 10 kafin aiko Manzon Allah, ranar Juma’a 13 ga watan Rajab(1) a cikin dakin Ka’aba(2).

                Lokacin da aka haifi Imam (a.s) mahaifiyarsa Sayyidah Fatima bint Asad ta sanya masa suna "Haidara" (ma'ana zaki). Sannan ita da Abu Talib, bisa wahayin Allah, suka amince a kira sa da “Ali”.

                An samu ruwaya daga Fadima bint Asad ta ce: Na shiga cikin dakin Ka’aba na ci ‘ya’yan itatuwa da kayan marmari na gidan Aljannah. Da na so fitowa sai wani ya kira ni: “Ya Fatima! Ki kiransa da “Ali” saboda shi ne Ali (Mai girma da daraja) kuma Allah Ta’ala yana cewa: “Na ciro sunansa daga sunana, na kuma rene shi da ladabina, na kuma sanar da shi ilimomina masu wahala, Shi ne zai karya gumaka a cikin dakina, kuma shi ne zai kira sallah a kan rufin dakina ya tsarkake ni, ya girmama ni. Don haka albarka ta tabbata ga wanda ya so shi kuma ya yi masa biyayya, kuma bone ya tabbata ga wanda ya saba masa kuma ya zamo makiyinsa (3).

Lakubbansa:

                Imam Ali (a.s) yana da laƙabi da dama, wanda ya fi shahara a cikinsu shine "Abul Hasan". Sauran laƙabinsa kuwa su ne Abu al-Hussein, Abul-Sabdain(4), Abul-Raihanatain da Abu Turab. A cikin ruwayoyi, ya zo cewa lafazin “Abu Turab” shi ne mafi shaharar lafuzza a wurin Imam, kuma a duk lokacin da aka kira shi da shi yana jin dadi(5).

Lokacin Yarinta Na Imam Ali (a.s)

                Lokacin da Imam Ali (amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana karami, Quraishawa sun sha fama da farin yunwa. Wannan ya sa Annabi (SAW) ya nema daga Abu Talib wanda yana da ‘ya’ya da yawa kuma da wuya kulawa da su a lokacin farin yunwa, ya ba shi amanar rikon Imam Ali (a.s) sai Abu Talib ya karbi wannan tayin, sa Imam Ali (a.s) ya koma gidan Annabi Sawa (6).

                Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yana tsananin son Imam Ali (a.s) kuma ya kasance mai taka-tsan-tsan da himma wajen tarbiyarsa da rainonsa da koyon karatunsa. Amirul Muminin (a.s) yana cewa game da iliminsa a wajen Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) a cikin hudubar Qasi’ah: “Kun san matsayina a wajen Manzon Allah saboda kusancina na dangantaka a da matsayi na na musamman. Lokaci zuwa lokaci ina karami yakan dora ni a cinyarsa ya rungume ni a kirjinsa, ya dora ni a kan gadonsa, ya rika rungume ni a jikinsa, kuma daddadan kamshinsa yana shiga cikin [hancina]. kuma yana tauna abinci, sai ya sanyamin a bakina. Bai ji wata karya daga gareni ba, bai ga wani laifi kuskure ba. Babu shakka tun daga lokacin da aka yaye Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Allah ya sanya Mala’ika mafi girma daga cikin Mala’ikunsa ya yi masa rakiya dare da rana domin tafiya tafarkin daraja da kyawawan dabi’u a duniya, ni kuma ina binsa sau da kafa kamar rakumin yaye yana bin mahaifiyarsa. A kullum sai ya sanya nunamin wata alama ta halayensa, kuma ya sanya ni in bi shi akai”(7).

Imam Ali (a.s) a lokacin aiko Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa’alihi Wasallam)

                Mutumin farko da nan da nan bayan aiko Manzon Allah (saww) kuma ya karbi manzancinsa shi ne Imam Ali (a.s) Manzon Allah (s.a.w) dangane da haka. sai ya ce wa Sahabbai: "Wanda zai fara haduwa da ni ranar kiyama a kan tafki (Kausar) shi ne mafi girmanku a Musulunci, Ali bin Abi Talib"(9).

Ceton rayuwar Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) a Sha’abi Abi Talib.

                A cikin shekaru ukun da Musulman Makka suka kasance karkashin takunkumin tattalin arziki na Kuraishawa kuma suke zaune killace a wurin da ke cewa Sha’abi Abi Talib, Imam Ali (a.s) yana matashi yana kwana a gadon Annabi bisa umarnin mahaifinsa. Abu Talib don kada a cutar da shi idan kuraishawa suka kai masa hari cikin dare (10).

Lailat al-Mabbit

                A shekara ta 13 ta Annabci, tare da tsananin matsin lamba da mushrikan Makka suka yi wa musulmi, da kuma gayyatar da mutanen Yathrib (Madina) suka yiwa Manzon Allah (SAW). Hakan ya samar da damar hijirar musulmi zuwa Yathrib. Ana cikin wanna yanayi sai mushrikan kuraishawa suka yanke shawarar kashe Annabi (saw). Sai suka zabi mutum 40 daga kabilu daban-daban domin su kai farmaki gidan Manzon Allah da dare, su kashe shi a kan gado. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya sami labarin wannan shiri ta hanyar wahayin Allah, sai ya ce wa Ali (a.s) da ya kwana a kan shimfidarsa don ya yaudare masu kisan kai domin Annabi ya yi tafiya zuwa Yathrib da daddare. Ta haka ne a cikin daren da aka fi sani da Lailatul-Mabit. Imam Ali (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya kwana a gadon Annabi. Shi kuma Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi hijira zuwa Madina bisa gafalar mushrikai (11). Aya t 207 daga surar Baqara tyi Magana dangne da wannan lamari cikin lamari Imam Ali As:

»وَ مِنَ النَّاسِ مَن یشْرِی نَفْسَهُ ابْتِغَاءَ مَرْضَاتِ اللَّهِ وَاللَّهُ رَءُوفٌ بِالْعِبَادِ«

“Kuma a cikin mutane akwai wanda ya sayar da ransa domin neman yardar Allah, kuma Allah Ya kasance Mai tausayi ga bayi”.

Imam Ali (A.S) Da Khalifancinsa A Annabi (Saw).

A cikin shekaru 23 na aikensa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya sha jaddada halifancin Imam Ali (a.s) da magajintakarsa.

Yaumul Al-Dar ranar da Annabi (SAWA) ya ayyana Imam Ali (a.s) a matsayin magajinsa.

                A Shekara ta uku ta Annabci tare da saukar ayar:  (12) «وَأَنذِرْ عَشِيرَتَكَ الْأَقْرَبِينَ» "Kuma ka yi gargadi ga danginka makusantanka". an umarci wa Manzon Allah da ya isar da sakonsa ga danginsa da makusantansa. Ya shirya taro da ‘ya’yan Abd al-Muddalib ya ce da su: “Ya Bani Abd al-Muddalib! Na rantse da Allah, ban san wani saurayi a Balarabe da ya kawo wa jama’arsa abin da ya fi wanda na kawo muku ba. Na zo muku da alherin duniya da lahira, kuma Allah Ta’ala ya umarce ni da in kira ku zuwa gare shi. To, a cikinku wane ne zai taimake ni a cikin wannan al'amari har ya zamo dan'uwana, waliyyina, kuma magajina ya kasance a cikinku? Babu wanda ya bayar da amsar yarda da gamsuwa da amsa mai kyau sai Imam Ali bin Abi Talib, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya dora hannunsa a wuyan Ali, ya ce: "Wannan shi ne dan'uwana, waliyyina, kuma magajina a cikinku." Sabõda haka ku yi biyayya ga uamrnisa, kuma ku yi ɗã'a gare shi" (13).

Ranar Ghadir

                A shekara ta 10 bayan hijira, Manzon Allah (SAW) ya umurci musulmi da su halarci aikin Hajjin karshe na Manzon Allah tare da shi. A hanyar dawowa ne aka saukar da aya a wani yanki da ake kira Ghadir (inda ayari suke rabewa zuwa garuruwansu).

»ي يَأَيهُّا الرَّسُولُ بَلِّغْ مَا أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ وَ إِن لَّمْ تَفْعَلْ فَمَا بَلَّغْتَ رِسَالَتَهُ وَاللَّهُ يَعْصِمُكَ مِنَ النَّاسِ إِنَّ اللَّهَ لَايهَدِى الْقَوْمَ الْكَافِرِين» (14).

 "Ya Manzon Allah ka isar da abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, idan kuma ba ka aikata ba, to baka isar da sakonsa ba Allah zai kareka daga mutane domin Allah baya shiriyar da mutanen da suke kafirai".

                Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ba da umurnin da a dakata, a nan ne ya karanta fitacciyar hudubarsa ta Ghadir, ya gabatar da Sayyidina Ali (a.s) a matsayin halifansa kuma magajinsa. Sayyiduna da kansa yana cewa dangane da haka: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya fito da niyyar Hajjin bankwana. Sannan (a kan hanyarsa ta dawowa) ya isa Ghadir Khum. Da umarninsa suka shirya masa wani abu kamar mimbari. Bayan nan sai ya hau abun ya riki hannuna (ya daga shi sama), har sai da aka ga wani fari a karkashin gefensa, ya ce da babbar murya a cikin wannan wuri: “duk wanda na zamo shugabansa to Ali ma shugabansa ne. Ya ubangiji kaso wanda ya so ka ki wanda ya ki shi”. A wannan rana ne Allah Ta’ala ya saukar da ayar da ke cewa:

»الْيَوْمَ يَئِسَ الَّذِينَ كَفَرُواْ مِن دِينِكُمْ فَلاَ تَخْشَوْهُمْ وَاخْشَوْنِ الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَ أَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَ رَضِيتُ لَكُمُ الإِسْلاَمَ دِينًا« (15).

 “A wannan rana wadanda suka kafirta suka yanke tsammani daga addininku, kada ku ji tsoronsu, ku ji tsorona, a wannan rana nake cika muku addininku, kuma nake cika ni’imata a gareku kuma na yarde maku da da musulunci a matsayin Addini”. don haka, waliyyata. shi ne tushen cikar addini da gamsuwar Ubangiji madaukaki (16).

Hadisin Manzilah

                Hadisin Manzilah shi ne ingantaccen hadisin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) a wajen Ahlus-Sunnah da Shi’a, wanda ya ce wa Imam Ali (a.s):

»أنتَ مِنّى بِمَنزلةِ هارونَ مِنْ مُوسى، اِلّاأنـّه لانَبىَّ بَعدى (17) «

“Kai awajena kamar Haruna ne a wajen Musa sai dai babu Annabi a bayana”.

Ayah Wilayah:

                Aya ta 55 a cikin suratul Ma’ida, wadda ta sauka domin girmama Imam Ali (a.s) tana cewa:

»إِنّما وَلیکُمُ اللهُ و رَسولُهُ والّذینَ ءَامَنوا الَّذینَ یقِیمُونَ الصَّلوةَ و یؤتُونَ الزَّکوة و هُم راکِعونَ«

                “Lallai shugabanku shine Allah da Manzonsa, da wadanda suka yi imani, wadanda suke tsayar da salla, suke bayar da zakka suna masu yin ruku’i”. Allah Manzonsa Kawai sune Shugabanku da muminin da ya tsayar da salla kuma yake bayar da sadaka a halin yana ruku’u. kuma wannan ya faru ne a lokacin da wani mabukaci ya zo masallaci Imam Ali (a.s) ya ba shi zobensa yana ruku'u. Wannan daraja ta wahayi ta zo a cikin madogaran hadisi da dama na Shi'a da Sunna, kuma dukkan malaman tafsirin Shi'a da masu tafsirin Sunna da dama sun yi la'akari da saukar wannan ayar akan darajar Imam Ali (a.s).

Ayar Ulul Al-Amr

                Aya ta 59 a cikin suratun Nisa’i, wacce kuma ake kiranta da ayar biyayya, ta umurci muminai da su yi da’a ga Allah, Annabi mai tsira da amincin Allah da alayensa, da kuma shugabanni:

«يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ أَطِيعُواْ اللّهَ وَ أَطِيعُواْ الرَّسُولَ وَ أُوْلِي الأَمْرِ مِنكُمْ فَإِن تَنَازَعْتُمْ فِي شَيْءٍ فَرُدُّوهُ إِلَى اللّهِ وَالرَّسُولِ...»

 “Ya ku wadanda kuka yi imani, ku yi da’a ga Allah, kuma ku yi da'a ga Manzo, da shugabannin cikinku, idan kun samu jayayya, Tom ku koma da lamari zuwa ga Allah da Manzo..." wanda a ruwayoyi da dama suna nuna ma'anar shugabanni anan su ne Imamai As.

Imam Ali (As) A Zamanin Halifofi

                Hanyar da Amirul Muminin ya bi wajen mu’amala da halifofi abu biyu ne: idan wani hadari ya kasance barazana ga Musulunci da Musulmi, ko kuma wani kuskure da halifofi suka yi ya haifar da sabani a cikin addini, sai ya tuntubi halifofi ne kawai a matsayin mashawarci, domin kar Musulunci ya rushe sama da haka. Misali shawarar soji da Imam ya bayar game da yadda za a tinkari sojojin Iran a yakin Nahawand ko kuma taimaka wa halifofi wajen gyara wasu hukunce-hukuncen addini da suka zartar ba daidai ba. idan ya zamo taimakon da Imam zai yi wa halifofi zai daga darajar wadannan mutane a idon musulmi ko kuma don tabbatar da maslaharsu, to yan kin aikata hakan. Kamar rashin raka Umar a tafiyarsa zuwa Sham, wanda hakan ya sa Umar ya kai kararsa wajen Ibn Abbas.

                Tabbas wadannan shawarwarin sun takaita ne a tsawon shekaru 25 na Imam da yake zaune a gida [18] kuma galibi suna da alaka da zamanin Umar bin Khaddab. A lokuta da dama, a lokacin da halifofi suka gagara wajen bayar da hukunce-hukuncen fiquhi da shari’a, ko kuma suka kasa amsa tambayoyin mutane, wani lokaci kuma ga tambayoyin ma’abuta littafi ne, sai su tura su wurin Amirul Muminin (As).

Halifancin Imam Ali (a.s)

                Bayan an kashe Halifa Uthman, abokan hamayyarsa da suka hada da Ansaru da Muhajirai na Kuraishawa da Masarawa da Kufawa duk sun yi ittifaqi a kan halifancin Amirul Muminina (As). Imam Ali As da kansa yana cewa game da haka: “To, ba abin da ya bani tsoro shi ne yadda mutane suka yo kaina kamar garken kuraye, suka far mini ta kowane bangare, har gab suke su murkushe ’ya’yana biyu a ko ‘yan yatsuna a cikin wannan taron, har kuma mayafina ya tsage ta bangare biyu, mutne kamar garken tumaki haka suka baibayeni. [19]

Mutane sun yi mubaya'a ga Imam a ranar Juma'a 18 ga watan Zul-Hijjah al-Haram shekara ta 35 Hijira. [20] Da farko Imam ya ki yarda da karbar halifancin. Ya ce wa mutane: Ku bar ni ku nemi wani. Lalle ne a gabanmu akwai al’amura masu rikitarwa iri-iri, waxanda zukata ba za su tabbata a kansu ba, kuma tunani ba zai tabbata a cikinsa ba” [21].

                Daga cikin dalilan rashin karbuwarsa ga halifanci, ana iya ambaton wadannan lamurra: Idan Imam ya karbi ragamar al’amura zai yi yaki da abubuwan da aka gurbataa addini, kuma ya yi kokarin nuna hakikanin fuskar addini a bayan an gurbata ta, kuma duk wannan zai kasance ya haifar da tashin hankali mai yawa na siyasa da zamantakewa. Rashin kulawar Iman ga maslahar jiga-jigan siyasar wancan lokacin, musamman na kuraishawa kamar Dalha da Zubair, da Fito na futon da suka yi da Iman, da sanin yanayin zamantakewar wannan lokacin da kuma cewa mutane ba za su taimaka mashi ba akan tafarkin Alawiyancinsa.

                Bayan da Imam ya karbi halifanci sai ya ce: “tunda hakane karbar (mubaya’a) a cikin masallaci za’ayi; Domin mubaya'ata ba za ta kasance a boye ba kuma ba za a yi ta ba sai a masallaci. Daga nan sai mutane suka tafi masallacin Annabi (SAW) domin yin mubaya'a. Dalha bin Ubaidullah shi ne mutum na farko da ya yi mubaya’a ga Imam.[22] Daga nan sai mutane suka taho da yawa suka yi mubaya’a ga Amirul Muminina, kuma shi ne halifa na farko a Musulunci wanda dukkan mutane suka halarci zabensa.

Siyasar Imam Ali (as)

                A zamanin halifofi kafin Imam (As) sun aikata munanan ayyuka da yawa wadanda suka sa addinin Musulunci ya kauce daga tafarkinsa na asali. Don haka ne ma Imam ya fara aiwatar da gyare-gyare da dama don hana ci gaba da karkacewa da mayar da Musulunci kan tafarkinsa na asali.[23] An gudanar da waɗannan gyare-gyare a sassa da yawa, waɗanda za a iya ambata kamar haka: gyare-gyare bangaren gudanarwa, zabar wakilai masu cancanta da korar wakilai marasa cancanta da rashin dukar masu cin amana da marasa ikon yin aikin [24], zabar masu tsaro don kula da Wakilai da za su kama hannusu wajen ciyar da su gaba: Imam a cikin wasiƙarsa zuwa ga Malik ya ce: "Sa'an nan kuma ka yalwata su (wakilai) daga arziki; Domin yin hakan karfi ne na gyara rayukansu, kuma dalili ne da bai wajaba a gare su ba su taba dukiyar -jamaa’a- da take a hannunsu ba, kuma hujja ce a kansu idan ba su karbi umarninka ba, ko kuma suka ci amanar ka” [25]. Manufofin siyasayar tattalin arziki da gyare-gyare kamar ci gaban birane: Imam ya ce wa gwamnoninsa: “Mafi girman masu mulki yana cikin raya garuruwa ne”. [26], Ci gaban Noma: An karbo daga Imam Baqir (a.s) cewa Ali (a.s) ya rubuta wa kwamandojin sojoji cewa, “Ina hadaku da da Allah kan cewa ba za ku zalunci manoma ba". [27]

                Haɓaka masana'antu da kasuwanci: Imam Ali As ya yi jawabi ga jama'a yana ce: "Ku shiga yin kasuwanci, saboda kasuwanci shine dalilin da ya sa ba za ku buƙaci abin da ke hannun wasu". (28) Ko kuma inda yake cewa: "Lalle ne sana’ar mutum wata taska ce." [29] Manufofi da gyare-gyaren Al’adu: inganta ilimi: Sayyidina Ali As yayi magana ga Khas’am dan Abbas, gwamnan Makkah ya ce: “Ku zauna domin saurarensu safe da yamma, ku yi fatawa ga mabuqata, ku karantar da jahilai, ku tattauna tare da malamai”. [30] Kuma ya zo a cikin littafan tarihi cewa, a duk lokacin da Annabi ya samu dama da sarari a yaqi, ya kan ilmantar da mutane, kuma ya yi hukunci a tsakaninsu. Hana wargaza hadisai masu kyau da fada da hadisan da ba su dace ba, da kula da suka da watsi da yabo [31].

Shahadar Imam Ali (as)

                Bayan fatattakar Khawarij daga rundunar Imam Ali (a.s) a yakin Nahrwan, wasu gungun mutum uku daga cikinsu sun yanke shawarar kashe Mu’awiya, Umar dan As da Amirul Muminina Ali (a.s) a lokaci guda. Wanda suna ganin su wadanna mutanen guda uku sune dalilin rarrabuwa da fitinar musulimi , Ibn Muljam Muradi shine wanda ya dauki kashe Imam Ali As, tare da taimakon Wardan Ibn Majalid, da Ash’ath Ibn Qais, da Shabib Ibn Bajrah, wanda Bakhawarijen Nahrwan ne, ya aiwatar da aikinsa. A safiyar ranar Laraba 19 ga watan Ramadan shekara ta 40 bayan hijira, a mihrabin masallacin Kufa Ibn Muljam ya sari Imam da takobi mai guba a lokacin da yake sallah. Imam Ali (a.s) ya yi shahada ne a daren 21 ga watan Ramadan sakamakon wanna saran.

Madogara:

[1] Al-Irshad, Al-Mufid, juzu'i na 1, shafi: 5; Al-Tabarsi, juzu'i na 1, shafi: 306

[2] Bihar al-Anwar, juzu'i na 35, shafi na 17 da 36, da Kasf al-Ghamma, juzu'i na 1, shafi na 125

[3] Ma’ani Al-Akhbar shafi na 62 da 63 da Raudatul Waazin shafi na 77.

[4] Raudatul Al-Waezin: shafi na 87

[5] Al-Maajm al-Kabir, juzu'i na 6, shafi na 167 da 149.

 [6] Dalaelun Nubuwwa na Bayhaqi: Mujalladi na 2 shafi na 162, al-Munaqib na al-Khwarizmi: shafi na 51 h 14.

[7] Nahj al-Balaghah: Khuduba 192

[8] Marigayi Allameh Amini ya bayar da nassoshi na hadisai da lafuzzan muhadisai da dama da malaman tarihin musulunci dangane da cewa Ali (a.s) shi ne farkon wanda ya yi imani da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam). a juzu'i na uku na Al-Ghadir, shafi na 191 zuwa 213 (bugu na Najaf).

[9] Amali Lil Saduq shafi na 274 da Maani al-Akhbar shafi na 402.

[10] Tfasir Namuneh C: 5 p.: 198

[11] Bihar al-Anwar (I - Beirut), juzu'i na 19, shafi na 60

[12] Suratul Shaara.

[13] Al-Amali Laltasi: shafi na 582 AH 1206

[14] Suratul Ma’ida, aya ta 67

[15] Suratul Maedah, aya ta 3

[16] Kafi, Mujalladi na 4, shafi na 27, shafi na 8

[17] Littafin Al-Manaqib, Babi na 21 Hadisi na 3731, shafi na 981.

[18] littafin encyclopedic na dangantakar siyasa na Sayyidina Ali a kan Musulunci tare da halifofin da Ali Labaf ya rubuta.

[19] Nahj al-Balagha, fassarar Seyyed Razi/Hussein Ansarian, hadisi mai lamba 3.

[20] Tazkiratul Khawas Al-Khass: 56

[21] Ansab al-Ashraf, juzu'i na 2, shafi na 219

[22] Al-Kamil Fit Tarikh: 2/302,

[23] Siyasar Imam Ali (a.s)/Mohammed Mohammadi Ray Shahri, Publications of Publishing Organisation.

[24] Nahj al-Balaghah: Harafi na 53, Tohf al-Aqol: 143 da 147.

[25] Nahjul Balaghah: harafi na 53

[26] Gharar al-Hakm: 6562,

[27] Samtun al-Nujum al-Awali, juzu'i na 2, shafi na 440

[28] Man La Yahdrah al-Faqih: 3/193/3723

[29] Mawa’izul Adadiyyah: 55

[30] Nahjul-Balaghah: Harafi 67

[31] Siyasat Nameh Imam Ali (As), Mohammad Mohammadi Ray Shahri, kungiyar bugun Dar al-Hadith.