Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

1 Afirilu 2024

15:51:16
1448249

Birgediya Janar Muhammad Reza Zahedi ya yi shahada a harin da sojojin Isra'ila suka kai ofishin jakadancin Iran da ke Damascus.

Cikakkun Bayanai Na Harin Da Yahudawan Sahyoniya Suka Kai Kan Ofishin Jakadancin Iran Da Ke Damascus

Birgediya Janar Muhammad Reza Zahedi ya yi shahada a sakamakon harin da sojojin yahudawan sahyoniya suka kai kan ginin karamin ofishin jakadancin Iran da ke Damascus.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran yana daga cikin wadanda aka nufa da kisan wanda ya kasance a lokacin baya a ofishin jakadancin.

A cewar wasu bayanai, daya daga cikin jami'an Iran ya yi shahada a wannan harin.

Majiyoyin Syria sun ce an lalata ginin da ke kusa da ofishin jakadancin Iran.

Aikin agaji da kwashe gawawwakin shahidai daga ginin da ke daura da ofishin jakadancin Iran a Damascus yana ci gaba da wakana kamar yadda zaku ga hakan a bidiyon dake biye.

Bayan harin da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kai kan ginin da ke kusa da ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Damascus, an fara aikin ceto tare da kwashe gawarwakin shahidan.