Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: yahudawan sahyuniya sun kai hari kai Damascus/ ginin da ke kusa da ofishin jakadancin Iran ya lalace gaba daya
Shaidun gani da ido sun ce daya daga cikin rokokin da aka harba ya fada yankin filin jirgin saman sojojin da ke yankin Al-Mezeh a birnin Damascus.
Shima ginin da ke kusa da ofishin jakadancin Iran an kai masa hari tare da lalata gaba daya.
A cewar rahotannin farko mutane 6 ne suka yi shahada.