Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

1 Afirilu 2024

13:55:35
1448187

Kamfanin Dillancin Labarai Na ABNA Na Ta Ɗaukacin Al'ummar Duniya Juyayin Shahadar Shugaban Wasiyyai Imam Ali As

Amincin Allah ya tabbata ga jarumin musulunci shugaban waliyyai da wasiyyai shahidin hubbaren ubangijinmu Amirul muminin Imam Ali As

A yau ne ake gudanar da taron jajantawa da juyayin shahadar Amirul Muminina Imam Ali bin Abi Talib (a.s) dan'uwan manzon Allah kuma majibincinsa kuma magajinsa a bayansa ga dukkan halittu a ranar 21 ga watan Ramadan shekara ta 40 bayan hijira.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya kawo maku bayanin Ta'aziyyarsa ga al'umma na shahadar Imam Ali As.

Imam Ali bin Abi Talib shi ne babban mutumi wanda yake misalta addinin musulunci mai wakiltar musulunci a duniya bayan Annabin Rahama Sawa, wanda Imam Ali tun farko an haife shi a cikin dakin Ka'aba mai alfarma, wannan tsohon dadadden gida na Allah Ta'ala, wanda ake ganin shine Mafakar mutane da shimfiɗar sanyin zukata, wannan gida shine gurin farko da wannan babban mutum ya bayyana wato daga wurin da jama'a tattaruwa wato daki mai tsarki.


Allah madaukakin sarki ya so ya girmama wannan bawa nasa tun farko, don haka haihuwarsa ta kasance cikin dakin Ka’aba mai daraja, kuma girmama shi bai tsaya nan ba, domin shi ne cikakkiyar shaksiyyarsa ita ce ta Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), Allah madaukakin sarki yans kewaye da tarihin dan Adam tun daga lokacin Adam har zuwa tsayuwar kiyama, don haka ya danganta rayuwar Ali binu Abi Talib da wadannan al’amura da lokuta, an haife shi ne a dakin Ka’aba, kuma ya kasance an aurar da shi a sama, kamar yadda aka ambata a cikin ziyarar girmamawa, kuma ya yi shahada a daya daga cikin gidajen Allah madaukaki. Bai tsaya a wadannan marhaloli guda uku kadai ba, wadanda suka hada da haihuwa a dakin Ka'aba, daurin aure a sama, da shahada a dakin Allah Ta'ala ba ya yi rayuwa mai cike da bayarwa da kyauta da baiwa.

Ya rayu shekara sittin da uku kacal, amma girmansa ya fi haka, sararin samaniya tana raka shi a duk motsinsa, ku lura da kiraye-kirayen da suka sauko daga sama: “Babu takobi sai Zul-Fiqar, babu Saurayin Jarumi Sai Ali,” wanda shi ne kira na farko daga Jibrilu, dangane da kira na biyu da ya sauko daga sama, da kuma shahadarsa (amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa: “Wallahi an ruguza rukunan shiriya,” wanda yake shi ne kira daga sama wanda ya labarta girman alfarma ta wannan babban mutumi.

Bayan saran la'ananne Ibn Muljim da kuma raunata Amirul Muminin, Imam Ali (a.s), bayan wasu an kwana sai Imam As yana kara jin shigar dafin cikin jikinsa mai martaba, yana kara tsumama lokaci bayan lokaci bayan ya farka, sai ya dubi da idanunsa ga daukacin mutanen gidansa, ya ce: “ina maku bankwana na bar ku amanar Allah baki daya, Allah ya saka muku da alheri, Allah ya tsare ku baki daya. Na barki cikin kulawar Allah , kuma Allah Ya isa ya zama kulawa”.

Sai ya ce: “Aminci ya tabbata a gare ku ya manzanni Ubangijina,” sai ya ce: 

"لِمِثْلِ هذَا فَلْيعْمَلِ الْعَامِلُونَ"، "إِنّ اللّهَ مَعَ الّذِينَ اتّقَوْا وَالّذِينَ هُم مُحْسِنُونَ".

Sai guminsa ya karu dayawa yayin da yake ta ambaton Allah da yawa, bai gushe ba yana ambaton Allah da yawa yana na fadin kalmar Shahada, sannan ya fuskanci alkibla ya rufe idanunsa, ya mike kafafunsa da hannayensa ya ce:

"أشهد أن لا إله إلاّ الله، وحده لا شريك له، وأشهد أن محمداً عبده ورسوله"

 Sai ruhinsa mai tsarki (saw) ya cika, wannan kuma ya kasance a daren Lailatul kadari. ashirin da daya ga watan ramadan, wato dare na biyu bayan an sare shi.


 Allah Ta'ala ya tsinewa makashinsa Ibn Muljim.


Da haka rayuwar fiyayyen halittun Allah gaba dayansu bayan Manzon Allah (SAW) ta kare bayan rayuwarsa ta jihadi don neman yardar Allah, da zuhudu da tabbatar da adalci, ya kasance abin koyi na daukaka, jarumtaka, tsarki, adalci, da nagarta, kuma alama ce ta kamalar dan Adam a tsawon tarihi.

السلام على بطل الاسلام سيد الوصيين وقائد الغر المحجلين شهيد المحراب مولانا امير المؤمنين الإمام علي (ع)، عظم الله أجورنا وأجوركم.