Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

1 Afirilu 2024

11:12:50
1448159

Sojojin Gwamnatin Sahyoniyawan Sun Janye Daga Kewayen Asibitin Al-Shafa

Majiyoyin Falasdinawa sun sanar da janyewar dakarun yahudawan sahyuniya baki daya daga kusa da asibitin al-Shafa da ke yammacin birnin Gaza bayan shafe kusan makonni 2 suna killace da shi.

  Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA –  ya habarta cewa:  majiyoyin Falasdinawa sun sanar da janyewar dakarun yahudawan sahyoniya baki daya daga kusa da asibitin al-Shafa da ke yammacin birnin Gaza bayan shafe kusan makonni 2 suna killace da shi.

Yayin da yakin Gaza ya shiga rana ta 178 a yau (Litinin), majiyoyin Falasdinawa sun ba da rahoton cewa, motocin dakarun yahudawan sahyoniya sun fice gaba daya daga kusa da asibitin al-Shafa da ke yammacin birnin Gaza zuwa kudu maso yammacin wannan birni.

Kamfanin dillancin labaran Al-Mayadeen ya habarta cewa, janyewar sojojin yahudawan sahyuniya ya biyo bayan mummunan hare-haren da dakarun gwagwarmayar Palastinawa suka yi wa wadannan dakarun da kuma yin wani kazamin fada da sojojin mamaya a kusa da asibitin Al-Shafa.

Dakarun Al-Qassam, reshen soja na kungiyar Hamas, sun kai hari kan motoci da dakarun yahudawan sahyuniya a kusa da asibitin Al-Shafa a jiya Lahadi.

Jaridar New York Times, ta nakalto cibiyar nazarin yaki, ta bayar da rahoton cewa, a tsakanin ranakun 18 zuwa 28 a watan Maris, kungiyar Hamas da sauran kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa, sun kai wani hari  sau 70 kan dakarun yahudawan sahyoniya a cibiyar kiwon lafiya ta Al-Shafa, kuma hakan ya nuna cewa; wadannan hare-haren sun yi karfi da inganci.

Sojojin yahudawan sahyoniya sun shafe sama da makwanni 2 suna kewaye wannan asibiti tare da aiwatar da kashe-kashe da dama a kan Palasdinawa a ciki da kewaye, lamarin da ya kai ga shahada da raunata daruruwan mutane.

Bayanai sun ce mazauna yankin da ke kusa da asibitin al-Shafa sun ciro gawarwakin shahidai akalla 50 daga wannan asibiti bayan janyewa da dakarun yahudawan sahyuniya suka yi.

Dukkanin majiyoyin kiwon lafiya sun ruwaito cewa dakarun yahudawan sahyuniya sun kona gine-ginen al-Shafa kuma an dakatar da aikin wannan asibiti gaba daya.

Wadannan majiyoyin sun ba da rahoton barna mai yawa a cikin wannan hadadden gine-gine da kewayensa.

Majiyoyin lafiya sun jaddada cewa akwai daruruwan gawarwakin shahidai a rukunin Al-Shafa da kuma tituna da hanyoyin da ke kewaye da shi.

Kakakin hukumar tsaron farar hula a Gaza ya kuma sanar da cewa, akwai gawarwakin shahidai kusan 300 a rukunin al-Shafa da kewayensa.

A gefe guda kuma gidan rediyon yahudawan sahyoniya ya bayar da rahoton cewa: Sojojin kasar sun kashe mutane 200 tare da kame mutane 500 a yayin farmakin da suka kai a rukunin kiwon lafiya na Al-Shafa sun kuma gayyaci mutane 900 domin yi musu tambayoyi.