Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

28 Maris 2024

08:00:30
1447351

Isra'i Da Mi'iraji DA Yakin Badar Suna Daga Manyan Munasabobin Da Suka Faru A Ranar 17 Ga Watan Ramadan A Tarihin Musulunci

Yazo A Ruwayoyi Akwai Sabanin Shekara Da Wata Da Akayi Isra’i Da Manzon Rahama Sawa Amma Akwai Ruwayar Da Aka Samo Daga Imam Sadik Yana Cewa Allah Ta’ala Yayi Isra’i Da Manzon Rahama Sawa Sau Dari Da Ashirin Ne Kuma Babu Daya Daga Cikinsu Da Allah Ta’ala Baiwa Annabi (SAWA) Wasiya Da Wilayar Ali Da A’imman Bayansa Ba Fiye Da Adda Yayi Masa Wasiyya Da Fairllan Ayyuka.

17/Ramadan/2h

            A safiyar irin wannan ranar ne yakin Badar wato Gazwatul Badarul Kubraa ya wakana a shekara ta 2 bayan Hijra, wanda wannan rana bisa ruwaya mafi shahara ta kasance ranar juma’ah ce, Kuma shine farkon yaki da ya wakana bisa Jagorancin Annabin Rahama sawa da kansa, yakin ya faru a wani waje da ake kira da Badar tsakanin makka da Madina, yakin ya faru Tsakanin Musulmai da Mushirkan larabawa bayan Hijirar Annabi Muhammad sawa zuwa madina da shekara biyu.

            A wannan yakin duk da karancin Musulmai da yawan Mushrikai amma musulami sun samu nasara inda acikinsa aka kashe tare da kama da yawa daga cikin manyan Mushrikai. Lalle Musulmai sun jajurce tare da dakewa musamman Imam  Ali as da Sayyiduna Hamza as. Wanda wannan yakin yana daya daga cikin yakokin da aka anbace su acikin Alkur’ani mai girma.  Dalilin aukuwar wannan yaki shine bayan shan wahalhalu da azabtarwa da mushrikai suka yi ga Musulmai a Makka tare da hanasu gudanar da ayyukansu na addini har takai sunyi hijra zuwa madina ga kuma wawushe da kwashe dukiyar musulmai da mushrikai su kai a makka bayan yin hijararsu. Hardai musulmai suka samu izinin yakar Mushrikai wanda kafin wannan yakin na Badar akwai wadansu gungu yakoki da akayi wanda Annabi sawa bai halarta ba ya tura Sahabban sa bayan samun umarnin yin yaki.

            Bayan Musulmai sun kai wani farmaki kan Ayarin kasuwanci da ya taso daga Makka zuwa Sham wanda Abu sufyan ke shugabanta, duk da musulmai basu samu kama wannan Ayarin ba amma hakan ya taka rawa wajen aukuwar wannan yakin. Inda Abu sufyan ya tura dan sako zuwa Makka kan cewa mushrikai fa su yunkuro wajen kare dukiyarsu, nan da nan mushrikan Makkah suka tattaro hadakar Kabilolin da suke da kason dukiya cikin wannan Ayari domin kare dukiyoyinsu  inda suka kai kusan mutum 950.

            Inda akarshe dai yakin ya fara da fito na fito inda mutane uku uku suka fito daga bangarorin guda biyu aka kwama bangaren Musulmai akwai Sayyiduna Hamza, Imam Ali, Ubaidah As bangaren Mushrikai kuma Utbah, Walid, Shaibah ne suka fito. 

17 Ga Ramadan Ta Dace Da Ranar Da Akai Mi'iraji Da Manzon Allah SAWA.

Kamar yadda hadisai da ruwayoyi na littafan Shi'a da Sunna suka nuna, Manzon Allah (SAW) yayi tafiyar Mi'iraji daga masallacin Aqsa a daren 17 ga watan Ramadan ne.

Tsawon Lokacin tafiyarsa daga Makka zuwa kasar Baitul-maqdis da Masallacin Aqsa daga nan kuma zuwa sama da dawowa daga Mi'iraji bai wuce dare daya ba, kamar yadda tafsirin Ayashi ya kawo daga Imam Sadik (AS) ya ce: Manzon Allah (SAWA) ya sallaci sallar Isha’i da asuba a Makka ne.

Tafiya ta ruhi ta mi'iraji itace ɗayan abubuwan al'ajabi a farkon musulunci data faru ga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) wanda tana ɗaya daga cikin mu'ujizozin Annabi mai tsira da amincin Allah.

            Labarin Mi'irajin Manzon Allah SAWA ya kunshi sassa biyu, na farkonsu shi ne tafiyar da Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) kan Abin hawa wanda ake kira "Buraqah" daga Masallacin Haram zuwa Masallacin Aqsa a cikin dan kankanin lokaci’ ya ziyarci sassa daban-daban na masallacin da "Bai'talahmi", wanda nan ne mahaifar Annabi Isa (AS), ya kuma ziyaci gidajen annabawa da kayayyakin tarihinsu da wurarensu, inda a wasu gidajen ya yi sallah raka biyu.

            Kashi na biyu na labarin shine; hawansa zuwa sama shi ne tafiyar sa daga Masallacin Aqsa zuwa sama, inda yaga taurari da tsarin duniya ta sama, kuma yayi magana da ruhohin annabawa da mala'iku na sama, ya ziyarci Aljannah da gidan Wuta wanda labarin yana da tsawon gaske, Wannan bangare na tafiyar sama ana kiran sa da "Mi’iraj".

            Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya samu cikakkiyar masaniya game da asirtattun abubuwa na rayuwa da sirrin tsarin halitta da kuma fadin sararin samaniya.

Wanda Kamar Yadda Yazo A Ruwayoyi Akwai Sabanin Shekara Da Wata Da Akayi Isra’i Da Manzon Rahama Sawa Amma Akwai Ruwayar Da Aka Samo Daga Imam Sadik Yana Cewa Allah Ta’ala Yayi Isra’i Da Manzon Rahama Sawa Sau Dari Da Ashirin Ne Kuma Babu Daya Daga Cikinsu Da Allah Ta’ala Baiwa Annabi (SAWA) Wasiya Da Wilayar Ali Da A’imman Bayansa Ba Fiye Da Adda Yayi Masa Wasiyya Da Fairllan Ayyuka.