Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

26 Maris 2024

17:39:46
1446981

Jagora: A Ganawarsa Da Isma'il Haniya "Bamayin Ƙasa A Gwiwa Wajen Goyon Bayan Mutanen Gaza".

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa kisan gillar da ake yi wa al'ummar Gaza da kuma kisan gillar da ake yi a wannan yanki yana shafar duk wani mai hankali, sannan ya kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ba da goyon baya ga al'ummar Palastinu da kuma al'ummar masu da ake zalunta da masu gwagwarmaya a Gaza.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: A yammacin yau Jagoran juyin juya halin Musulunci a ganawarsa da shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Isma'il Haniyyah da tawagar da suke tare da shi, ya yaba da matakin mara misaltuwa na dakarun gwagwarmayar Palastinu da kuma al'ummar Gaza tare da jaddada cewa: hakurin tarihi na Al'ummar Gaza dangane da laifuffuka da zaluncin da gwamnatin sahyoniyawan take aiwatarwa akansu tare da cikakken goyon bayan kasashen yammacin duniya cewa wannan lamari ne mai girma da ya girmama addinin Musulunci da gaske, ya kuma mai da batun Palastinu a matsayin batu na farko duniya duk da nufin makiya.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa kisan gillar da ake yi wa al'ummar Gaza da kuma kisan gillar da ake yi a wannan yanki yana shafar duk wani mai hankali, sannan ya kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ba da goyon baya ga al'ummar Palastinu da kuma al'ummar da ake zalunta da masu gwagwarmaya a Gaza.

Ayatullah Khamenei ya kimanta batun goyon bayan ra'ayin al'ummar kasa da kasa da kuma ra'ayin al'ummar musulmi musamman na kasashen Larabawa ga al'ummar Gaza da cewa: Fadakarwa da matakan watsa labarai na gwagwarmayar Palastinawa sun kasance masu matukar muhimmanci da kyau zuwa yanzu kuma suna gaba dana abokan gaba na sahyoniyawan, kuma dangane da wannan, ya kamata a ɗaukar matakai a gaba da suka fi na baya.

Haka nan kuma ya karrama shahidi "Al-Arouri" daya daga cikin jagororin kungiyar Hamas, wanda gwamnatin sahyoniya ta shahadantar, ya kuma yi nuni da cewa: wannan shahidi mai daraja ya kasance fitaccen mutum ne wanda karshen shahadarsa cikin farin ciki ya kasance sakamakon da Allah ya ba shi bisa kokarin mujahadarsa.

A cikin wannan taro, Malam Ismail Haniyeh, shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas, yayin da yake godiya da jinjinawa goyon bayan al'umma da gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan batun Palastinu, musamman al'ummar Gaza, ya gabatar da rahoton dangane da abinda yake faruwa fage a baya-bayan nan da kuma ci gaban siyasa na yakin Gaza yana mai cewa: Hakuri da tsayin dakan al'ummar Gaza da dakarun gwagwarmaya a cikin wadannan watanni shida, ya samu ne sakamakon tsayuwar imani da suke da shi, ya sanya makiya yahudawan sahyoniya ba su cimma wata manufarsu ba a yakin Gaza.

Shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas ya jaddada cewa, hare-haren " guguwar Al-Aqsa" ta ruguza tatsuniyar gwamnatin sahyoniyawan na cewa ba za a iya cin galaba a kansu ba, kuma a halin yanzu bayan watanni shida makiya yahudawan sahyoniya sun gamu da asara mai yawa tare da kashe dubban sojojin wannan gwamnatin tare da raunata wasu, ya kara da cewa: Yakin Gaza yakin duniya ne kuma hukumar da ke mulkin Amurka ita ce babbar mai hannu a cikin laifukan yahudawan sahyoniya saboda ita ce ke jagorantar yakin gwamnatin sahyoniyawan.

A karshen jawabin da ya yi wa Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Ina tabbatar wa mai Mai Martaba cewa duk da irin zalunci da laifuka da kisan kare dangi da ake tafkawa a zirin Gaza, al'ummar Gaza da dakarun 'yan gwagwarmaya sun tsaya tsayin daka kuma ba zasu bari makiya yahudawan sahyoniya su cimma burinsu ba.