Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

26 Maris 2024

11:48:48
1446923

Kwanaki 150 Na Gwabza Yaki: Yadda Isra'ila Ke Tafka Laifukan Yaqi A Gazza.

Wannan makala tana dauke da bayani dangane da irin laifukan yaki da Isra'ila ta tafka a zirin Gazza da kuma kisan kan mai uwa da wabi da ya hada harda 'yan jarida na kasa da kasa, sannan ta kawo jerin sunayen Shahidai na 'yan jarida tun daga farawar yakin har zuwa kwan 150 na yakin.

  Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA –  ya kawo maku wata makala dangane da yakin Gaza da kuma adadin 'Yan Jarida da aka kashe a wannan yakin yayain da suke gudanar da ayyukansu na jarida, wanna makala takaitacciya dan jarida kuma mai baincike malam Yusuf Kabir ne ya rubuta maku asha karatu lafiya:  

Bayan mamayar Isra’ila a Falasdinu da Gazzza na tsawon shekaru dakarun Hamas sun kai harin ramuwar gayyar kisan kare dangin da Isra'ila ke musu: tun daga 7 ga Oktoba ne Isra'ila ta ke aiwatar da kisan kare dangi a kan kasar Palasdinu. Ga jerin laifukan yaki da Isra'ila din ta tafka a zirin Gazza:-

1. A ranar 14 ga watan Oktoba harin Isra'ila ya fada kan motar Agaji ta jami'an Red Crouse tare da tarwatsa motar.Wannan harin karya dokar yaki ne bisa yarjejeniyar Geneva.A yayin da Hukumomi Gazza,da wasu daga cikin Hukumar  lafiya ta Duniya WHO ta bayyana hakan a matsayin karya dokokin yaki.

2. HALAKA 'YAN JARIDA:

'Yan Jarida suna da 'yancin gudanar da ayyukansu ko da kuwa a na cikin yaki ne,amma haka Isra'ila ta kashe 'yan Jarida sama da 20 a farkon yakin.A Daftarin dokokin yaki na Duniya da aka kaddamar a Geneva,an haramta kashe 'yan Jarida.Hare-haren Isra'ila a satin farko na fara wannan yaki ya kashe fitattun 'yan Jarida irin su Barji Hajjiy,Assam bn Abdullahi,Samir Abu Dikka,wadannan 'yan Jaridan galibansu  'yan asalin kasar Palasdinu ne.

3. HALAKA 'YAN SANDA A GAZZA: A ranar Litinin 16/10/2023 jiragen hare-haren Isra'ila ya kai hari kan 'yan Sanda a kasar Palasdinu,a yayin da harin ya kashe 10 daga cikinsu wadanda suke 'yan asalin garuruwan kasar daban-daban.Kai wa 'yan Sanda hari karya dokokin yaki ne na kasa da kasa.A cikin kundin dokokin yaki da aka gabatar a Geneva a shekarar 1949 ya bayyana cewa:"Ya wajaba a kiyaye kai hari kan jami'an tsaron da ke kula da gari,da ma'akatan jinya,da Likitoci,tsaffi,yara da mata,kuma wajibi idan an illata su a dauke su a kai su Asibiti domin karbar taimakon gaggawa."

4. TILASTA YIN HIJIRAR DOLE: A ranar 13/10/2023 yekuwar Isr'aila ta sanya Palasdinawa Miliyan daya da doriya barin muhallansu da yin hijira daga Arewacin Gazza.

5. A ranar 14/10/2023 Hukumar WHO ta fitar da bayanin kauracewa Asibitoci guda 22 da Palasdinawa suka yi:a matsayin hijirar dole.Wannan ya faru ne a sakamakon hare-haren da jiragen Isra'ila ke kaiwa Asibitocin.

6. SHARE IYALI DAGA SAMUWA: A ranar 9/10/2023 a yankin Mukeem aka share dangin Abu Kaudata daga samuwa.Haka an share Iyalin Shihab, Najjar, Ajrumiy, Asibitin Ma'amadaniy, Tarwatsa Cocin Kudais da hari kan iyalan Musa.Bugu da kari a ranar 18/10/2023 aka share iyalan Rashwan, iyalan Mudawwik, da na Abu Wardata.

7. HALAKA MUTANE SAMA DA DUBU 3 A RANA GUDA: A dai ranar 18/10/2023 ne jirage marassa matuki na Isra'ila ya kai munanan hare-hare a Gazza in da aka kashe mutane 3300 tare da raunata 1200 a ranar guda.

8. KAI HARI KAN KASUWAR MUKIMU-JIBAL: A ranar 9/10/2023 Isra'ila ta kai hari kan kasuwar Mukimu-Jibal in da ta kashe mutum 60 tattare da raunata 100+ hade da lalata kasuwar. A dai wannan ranar ne Harin Isra'ila ya halaka dimbin mutanen da ke Masallacin Gabashi, Masallacin Yaseen, Masallacin Susiy. Bayan kaddamar da harin Hukumar kula da lafiya ta siffanta harin a matsayin wanda ya lalata yankin gaba daya.

9. KAI HARI KAN MAKARANTAR URINI-TU'UY:A ranar 17/10/2023 ne dai Isra'ila ta kai hari kan Makarantar URINI in da mutane sama dubu 4 ke fakewa, a cikin wannan harin mutum 6 suka rasu, a yayin da gomomi suka ji rauni.

10. HANA KAYAN AGAJI ISA GAZZA: Akwai kasashe mabambanta da suka kudiri niyyar isar da kayan agaji ga zirin Gazza,amma kasar Isra'ila ta hana isar wadannan kayan ga Palasdinawan wannan ma yana cikin karya dokokin yaki na Duniya.

11. YANKE WUTA DA RUWA: A yayin da makiyi yake son yin galaba a kan makiyinsa,yanke ruwa da wuta yana cikin hanyoyin galabaita makiyi.Hakika Isra'ila sun yanke wuta da ruwa daga zirin na Gazza wanda hakan ya sabbaba mummunar illa ga yan kasar Palasdinu.Shugaban   masu kula da Likitoci na Duniya Cristiano Cristee yana cewa:" Hakika miliyoyi a Gazza na fuskantar kisan mummuke a sakamakon yanke wuta da ruwa,hakam kuma karya dokar yaki ne da aka sanyawa hannu a Geneva.

12. WULAKANTA FURSUNONIN YAKI: Dalilai masu yawan gaske sun bayyana a kan yadda Sojojin Isra'ila ke wulakanta Fursunoni Palasdinawa da suka kama. Da yawan Palasdinawan da aka kama an cire musu Rigunansu, sannan an rika bugunsu da bakin Bindiga, sannan an rika taka kawunansu.

13. AMFANI DA GIDAJEN MUTANE BA IZINI: A ranar 13/11/2023 Hukumar kai agajin gaggawa ta Duniya ta shaidi yadda Sojojin Isra'ila ke amfani da gidajen mutane domin ayyukan Soja.

14. RUSA MAKABARTU: A ranar 14/12/2023 Duniya ta shaidi yada Isra'ila ta rika kai munanan hare-hare a kan Makabartu a Gazza, sannan Sojojin Isra'ila sun kasa musa zargin aikata hakan da aka musu. A ranar 21/12/2023 harin Isra'ila ya rusa daya daga cikin makabartun da ke gabanshin Gazza.

Sunayen 'Yan Jarida 92 Da Isra'ila Ta Kashe A Gazza

A ranar Alhamis 16/12/ Sashen Kungiyar 'yan Jarida ta kasar Palasdinu ta bayyana jerin sunayen 'yan Jarida 92 da Isra'ila ta kashe.Ga sunayen na su daki-daki:-

1. Salihi Muhammad,Lafiy Ibrahim.

2. Wanjarag Ibrahim.

3. Shamlak As'ad.

4. Daweel Sa'ed.

5. Nawwajatu Hisham.

6. Zarku Abu Muhammad

7. Najjar A'id.

8. Madar Abu Muhammad.

9. Nakeeb Rajab.

10. Shihab Ahmad

11. Shihab Abdur Rahman.

12. Mubarak Hassam.

13. Madhun Haniy.

14. Bahhar Assam.

15. Ba'alusha Muhammad.

16. Habibi Abdul Hadiy.

17. Zark Abu Muhammad.

18. Nassam Aliy.

19. Shammalata Abu Anas.

20. Nadiy Samih.

21. A'zarrata Abu Khalil.

22. Zarifa Abu Muhammad.

23. Aliyu Muhammad.

24. Akili Imaniy.

25. Labad Muhammad.

26. Shurbijiy Muhammad.

27. Siraaj Rushdiy.

28. Hasaniy Muhammad.

29. Halbiy Sa'id.

30. Fakkawiy Jamal.

31. Mahhadi Abu Ahmad.

32. Namus Abu Yassar.

33. Mukaimar Salma.

34. Sharfu Du'a.

35. Maimata Salam.

36. Kashku Majid.

37. Wahidi Ammad.

38. Najjar Huzaifata

39. Nadeem Nazmi

40. Arnadas Majeed.

41. Maddar Ayyad.

42. Bayyar Muhammad.

43. Hadab Abu Muhammad.

44. Afganiy Ra-Zahih.

45. Nakeeb Musdafa.

46. Hararatu Haisam.

47. Hajat Muhammad.

48. Mani'i Abu Yahya.

49. Hasira Abu Muhammad.

50. Madar Mahmud.

51. Kurra'a Ahmad.

52. Barsh Musa.

53. Fadima Ahmad.

54. Barshi Ya'akub.

55. Hayyata Abu Amru.

56. Sawwaf Musdafa.

57. Awwad AbdulHalim.

58. Mansur Sariy.

59. Islim Hasunat.

60. Jaad Bilal.

61. Namar Ala'a.

62. Khadurat Ayat.

63. Ziik Muhammad.

64. Barsh Assam.

65. Ayyash Muhammad.

66. Bukair Musdafa.

67. Zahhad Amal.

68. Ashur Mus'ab.

69. Nazeel Nadeer.

70. Haniyya Jamal

71. Durwish Abdullahi.

72. Sawwaf Muntasar.

73. Hasunat Adham.

74. Muhammad.

75. Lu'u'lu'u Huzaifa.

76. Hassan

77. Jazzar Shaima'a.

78. Salim Mahmud.

79. Salim Mahmud.

80. Kairawaniy Abdul Hameed.

81. Yazijiy Hammada.

82. Ammar Hassam.

83. Ada'-Allah Ula.

84. Jabuur Du'a.

85. Kawwas Nirmaini.

86. Samrata Abu Muhammad.

87. AbdulKareem Awwada

89. Abbasatu Abu Ahmad.

90. Ayyan Hannan.

91. Dikka Abu Samir.

92. Musa Kammal Aseem.                     

'Yan Jarida Da Isra'ila Ke Tsare Da Su

                A ranar 28/11/2023 Kungiyar 'yan Jaridar kasar Palasdinu, suka bayyana cewa: "Duk da waccan adadin na 'yan Jaridar da Isra'ila ta kashe, a gefe guda kuma akwai sama da 40 wadanda ta ke tsare da su a wurare mabambanta’ Bayanan sun ci gaba da bayyana cewa; adadin 'Yan Jaridar da hare-haren Isra'ila ya rutsa da su a Gazza ya zarta na yakin Duniya na biyu da aka yi a tsakanin shekaru 1945-1939. Haka ya zarce adadi na yakin Koriya da aka yi a shekarar 1953-1950. An kiyasta a kalla kwanaki sama da 100 na yakin da ke gudana tsakanin Hamas da Isra'ila, kullum Isra'ila na kashe Dan Jarida daya a zirin na Gazza a yayin da yake gudanar da aikinsa.

  DAGA YUSUF KABIR: 09063281016.