Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

26 Maris 2024

11:39:41
1446922

Adadin Shahidai A Gaza Ya Kai 32,333 Bayan Shahadar Wasu Falasdinawa 107 Wadanda Suka Jikkata Ya Kai 74,694

Adadin shahidan yaki a Gaza ya kai 32,333 sannan adadin wadanda suka jikkata ya kai 74,694 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA –  ya habarta cewa: ma'aikatar lafiya ta kasar Falasdinu ta sanar a yankin zirin Gaza cewa sojojin yahudawan sahyuniya sun aikata kisan gilla da wasu laifuka guda 11 kan fararen hula a zirin Gaza cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

  Ma'aikatar ta kara da cewa an kashe Falasdinawa 107 tare da jikkata wasu 176 a wadannan hare-haren.

Adadin shahidan yaki a Gaza ya kai 32,333 sannan adadin wadanda suka jikkata ya kai 74,694 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

Kusan mutane 8,000 ne suka bace suke a karkashin baraguzan ginin.

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta sanar da cewa kashi 73% na adadin wadanda suka yi shahada da kuma jikkata a yakin Gaza mata ne da kananan yara.