Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

26 Maris 2024

11:16:01
1446917

Akwai Bama-Bamai 3,000 Na Yahudawan Sahyuniya Da Ba A Tayar Da Su Ba A Gaza

Rohotanni sun nuna cewa akwai sauran bama-bamai 3,000 da ba’a kaiga tashin su ba inda Yahudawan Sahyuniya ke yin barazana da su ga rayuwar al'ummar Gaza da aka yi wa kawanya.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA –  ya habarta cewa: Wata kungiyar kasa da kasa ta ce ya zuwa yanzu sojojin Isra'ila sun jefa bama-bamai 45,000 a zirin Gaza, inda akalla akwai sauran bama-bamai 3,000 ba ba’a kaiga tashin su ba tare da yin barazana da su ga rayuwar al'ummar Gaza da aka yi wa kawanya tare da mamayeta.