Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

25 Maris 2024

11:52:50
1446688

Taya Murna Da Zagayowar Ranar Haihuwar Imam Hasan As Shekara Ta Uku Bayan Hijira

Falaloli da darajojinsa sun zo cikin litattafan Shi’a da Ahlus-sunna, kuma ya kasance ɗaya daga As’habul Kisa (Ma’abota bargo) waɗanda ayar taɗhir ta sauka game da su da ƴan shi’a suke imani da ma’asumancinsu, ayar Iɗ’am, ayar mawadda, da ayar mubahala suna daga cikin ayoyin da sauka game da su, Sau biyu yana kyautar bakiɗayan dukiyarsa akan tafarkin Allah, sannan sau uku yana bada kyautar rabin dukiyarsa ga mabuƙata...

                   Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA –  ya kawo maku takaitaccen wani sashe na bayani rayuwar Ima Hasan As a lokacin tunawa da ranar haihuwarsa mai albarka    

Haihuwarsa:

          Kan asasin ruwayoyin da suka shahara, an haifi Imam Hassan (a.s) sha biyar ga watan Ramadan shekara uku bayan hijira, Kulaini da Shaik Ɗusi sun tafi kan cewa an haife shi ne a shekara ta biyu bayan hijira. an haife shi a garin Madina bayan haihuwarsa Annabi (s.a.w) ya yi kiran sallah a kunnen damansa, ya yi iƙama a na hagu. a kuma rana ta bakwai da haifarsa ya yanka masa ragon suna.

          Imam Hasan ɗan Ali ɗan Abi Ɗalib As wanda ya shahara da suna Hasanul Mujtaba (3-50) Shi Imami ne na biyu a jerin Limaman shiriya da manzon rahama Muhammad (SAWA) ya barwa Al’umma domin su yi koyi da su abayansa wanda ya yi limanci na tsawon shekaru 10 ne bayan shahadar mahaifinsa Imam Ali As, kuma ya kasance kusan watannin bakwai a matsayin Halifan musulmai.

          Ahlus-sunna suna ƙirga shi da sanya shi a matsayin halifa na ƙarshe cikin halifofi shiryayyau na farko. Imam Hassan ɗan Ali ya kasance babban ɗan Imam Ali (a.s) da Fatima (S) kuma Farkon jikan Manzon Allah (s.a.w), bisa riwayoyi da suka zo a tarihi, Annabi (s.a.w) da kansa ya zaɓa masa sunan ”Hasan” kuma yana son sa matuƙar soyayya, ya rayu tare da Annabi (s.a.w) shekaru bakwai, da shi aka yi bai’atul Ridwan da taron mubahala da kiristocin Najran.

          Falaloli da darajojinsa sun zo cikin litattafan Shi’a da Ahlus-sunna, kuma ya kasance ɗaya daga As’habul Kisa (Ma’abota bargo) waɗanda ayar taɗhir ta sauka game da su da ƴan shi’a suke imani da ma’asumancinsu, ayar Iɗ’am, ayar mawadda, da ayar mubahala suna daga cikin ayoyin da sauka game da su, Sau biyu yana kyautar bakiɗayan dukiyarsa akan tafarkin Allah, sannan sau uku yana bada kyautar rabin dukiyarsa ga mabuƙata, an ce sakamakon yawan kyautarsa ne ake kiransa da sunan ”Karimu Ahlil-baiti” sau kusan 20-25 yana zuwa Hajji a ƙafa.

          Akwai cikakken bayani dangane da rayuwarsa a lokacin halifancin Abubakar da Umar cikin littafan tarihi, ƙarƙashin umarnin Umar an zaɓe shi memba cikin kwamitin shura ta mutum shida da za su zaɓo halifa na uku, akwai rahotanni game da tarayyarsa cikin yaƙe-yaƙen da aka yi a zamanin halifancin Usman. Kuma da Umarnin Imam Ali (a.s) yana daga cikin waɗanda suka bada kariya ga Usman lokacin da aka yi masa tawaye, zamanin halifancin Imam Ali (a.s) ya tafi tare da shi zuwa Kufa, kuma ya yi tarayya cikin yaƙoƙin Jamal da Siffin tare da kasancewa layin Kwamandojin yaƙi. Imam Hasan ɗan Ali As ya zama Imami jagora a ranar 21 ga watan Ramadan shekara ta 40 bayan hijira bayan shahadar Imam Ali (a.s), a cikin wannan rana fiye da mutum dubu arba’in ne suka yi masa bai’ar halifanci. Sai dai cewa Mu’awiya da bai karɓi halifancinsa ba, ya tara sojojin yaƙi daga Sham ya nufo Iraƙi, Imam Hasan Mujtaba (a.s) shima ya aika da sojoji da Kwamandancin Ubaidullahi ɗan Abbas don yaƙar rundunar Mu’awiya, shi kuma ya tafi garin Sabaɗ tare da wasu gungun Jama’a, Mu’awiya ya yi amfani da yaudarar yaɗa jita-jita cikin sojojin Imam Hasan (a.s) domin samar da yanayin da zai tilasta shi yin sulhu, cikin wannan yanayi ne aka samu wasu suka nufin cutar da Imam Hasan (a.s) ta hannun wani mutum Bakawarije ta kai ga kaiwa Imam hari har ya ji masa ciwo, bayan nan sai a kai Imam garin Mada’in domin yi masa magani, daidai wannan lokaci ne aka samu wasu jama’a daga shugabannin Kufa suka aikawa Mu’awiya wasiƙa tare da yi wa Mu’awiya alƙawarin za su kawo masa Imam Hasan (a.s) ko kuma su kashe shi, sai Mu’awiya ya aika da wannan wasiƙa ta su zuwa ga Imam Hasan (a.s) tare da yi masa tayin yin sulhu, sai Imam Hasan (a.s) ya yarda da sulhu tare da miƙa halifanci ga Mu’awiya kan sharaɗin cewa zai yi aiki da littafin Allah da sunnar Annabi (a.s) kuma ka da ya ayyana halifansa a bayansa, sannan kuma dukkanin mutane su kasance cikin aminci cikin su kuwa har da ƴan shi’ar Imam Ali. Bayan wannan sulhu sai Mu’awiya ya yi watsi da waɗannan sharuɗɗa da yarjejeniya da aka yi da shi. Wanda haƙiƙa wannan sulhu da aka yi da Mu’awiya ya haifar da rashin yardar wasu daga sahabban Imam Hasan (a.s), lamarin da ya kai wasu ba’ari suna kiransa da sunan ”Muzilllul muminin” ma’ana wanda ya ƙasƙantar da muminai. Bayan waƙi’ar sulhu da ta kasance shekara ta 41 bayan hijira sai ya koma Madina ya zauna a can har ƙarshen rayuwarsa, ya jagorancin marja’iyyar ilimi a Madina, bisa wasu riwayoyi Imam Hasan (a.s) ya samu maɗaukakin matsayin a al’umma Lokacin da Mu’awiya ya yanke shawarar ayyana ɗansa Yazid matsayin mai jiran gado, ya aika da dinare dubu ɗari zuwa ga Ja’adatu matar Imam Hasan (a.s) domin ta shayar da shi guba, an ce Imam Hasan (a.s) ya yi jinyar kwanaki arba’in bayan shayar da shi guba daga baya ya yi shahada, a wani naƙali, an ce ya yi wasiyya da a binne shi kusa da ƙabarin Annabi (s.a.w) sai dai cewa Marwan ɗan Hakam da wasu adadin mutane daga Bani Umayyawa sun hana binne shi kusa da Annabi (s.a.w) daga ƙarshe an kaishi maƙabartar Baki’a aka binne shi a can. Akwai wasu adadin zantuka da wasiƙun Imam Hassan Mujtaba (a.s) da kuma sunayen mutane 138 da suka rawaici hadisi daga gare shi da aka tattaro su cikin littafin Musnadul Imam Hasan Mujtaba (a.s).

Rayuwarsa Lokacin Yarinta

          Babu kammlallen bayani dangane da shi game da lokacin yarinta da samartakar Imam Hassan, haƙiƙa ya rayu tare da Manzon Allah (s.a.w) ƙasa da shekaru takwas, da wannan dalili ne sunansa ya kasance cikin ayarin ɗabaƙa ta ƙarshe ta Sahabbai. ruwayoyi game da tsananin alaƙa da soyayyar da Annabi (s.a.w) yake masa da ɗan’uwansa sun zo cikin madogarai na littafan Shi’a da Ahlus-sunna. Daga mafi muhimmancin abubuwan da suka faru a wannan lokacin sun hada da cewa Imam Hasan As ya halarci taron Mubahala tare da mahaifinsa da ɗan’uwansa, shi da ɗan’uwansa sun kasance misdaƙin kalmar ”‘ya’yayenmu” dake cikin ayar mubahala. a cewar Sayyid Jafar Murtada Amili Imam Hasan da ɗan’uwansa (a.s) sun halarci bai’atul Ridwan sun yi bai’a ga Annabi (s.a.w). sannan kuma ayoyin Kur’ani sun sauka game da shi da sauran As’habul Kisa’i. Yazo a ruyawa cewa ya kasance yana halartar majalisin Annabi (s.a.w) yana ɗan shekara bakwai yana yi wa mahaifiyarsa bayanin abin da aka yi wahayi. An naƙalto daga Sulaim ɗan Ƙaisi wanda ya rasu ƙarshe-ƙarshen ƙarni na farko, bayan wafatin Annabi (s.a.w) lokacin da Abubakar ya karɓi halifanci, Imam Hasan ɗan Ali tare da mahaifinsa da mahaifiyarsa da ɗan’uwansa sun kasance suna zuwa gidajen mutanen Madina da daddare suna kiran mutanen Madina zuwa ga taimakawa Imam Ali (a.s). haka nan kuma malamai sun ce ya nuna rashin amincewarsa kan halifancin Abubakar.

Zamanin Samartaka:

Har ila yau ruwayoyi game da samartakarsa sun kasance ƙidigaggu, daga jumlarsu akwai abin da ya zo cikin littafin Al-Imama wa Al-Siyasa cewa yana cikin kwamitin Shura mai mutum shida domin zaɓar halifa, ƙarƙashin umarnin Umar ɗan Khaɗɗab. Cikin ba’arin riwayoyi daga madogaran Ahlus-sunna ya zo cewa Imam Hasan da Husaini sun halarci yaƙin Afrika a shekara 26 bayan hijira. da kuma yaƙin ɗabaristan a shekara ta 29 ko 30 bayan hijira, an samu saɓani kan waɗannan riwayoyi, Jafar Murtada Amili tare da la’akari da Ishkalan da suke tare da waɗannan riwayoyi daga sanadinsu ƙari kan haka Imamai (a.s) basu yarda su tsarin waɗannan yaƙe-yaƙe da futuhat ba suna ma ganin su matsayin ƙagaggun riwayoyi, tare kuma da cewa Imam Ali (a.s) bai yarda Hasnaini sun shiga fagen yaƙin Siffaini yin hakan kuwa kamar shaida ne da zai tabbatar da hakan. Yana mai cewa a cikin amsar da ya bawa Muhammad Ibn al-Hanafiyyah: Ya dana. Kai dana ne, kuma wadannan biyun ‘ya’yan Manzo ne, Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) shin ba zan kare su daga kashe su ba?.

          Wilfred Madelong yana ganin cewa tabbas Imam Ali (a.s.) yana son koyar da ɗansa Hasan a kan al'amuran yaƙi tun yana ƙarami kuma ya ƙara masa kwarewa a fagen yaƙin. daga cikin sauran riwayoyin da suke da dangantaka da wannan lokaci shi ne cewa duk sanda mutane suka kawo ƙarar Usman wurin Imam Ali (a.s) ɗansa Hasan yake aikawa wurin Usman, kan asasin naƙalin Bulazari dangane da waƙi’ar tawayen da boren da mutane suka yi kan Usman a ƙarshen halifancinsa lamarin da ya kai ga sun kewaye gidansa da toshe masa ruwa daga ƙarshe kuma suka kashe shi, haƙiƙa Imam Hasan ɗan Ali tare da ɗan’uwansa Husaini bisa umarnin Imam Imam Ali (a.s) sun je sun bada kariya ga gidan Usman, a cewar Khadi Nu’uman Magribi wanda ya rasu shekara ta 363 hijira ƙamari, kuma marubucin Dala’ilul Imama, bayan ƴan tawaye sun toshewa Usman ruwa, Hasan Mujtaba bisa umarnin mahaifinsa ya kaiwa Usman ruwan sha. an bada rahotannin cewa Imam Hasan ɗan Ali sai da ya ji ciwo a wannan waki’a. amma wasu malaman shi’a kamar misalin Allama Amini sun ƙaryata waɗannan riwayoyi. Sayyid Murtada bayan ya yi shakku da kokwanto kan cewa Imam Ali (a.s) ya aika da Hasanaini (a.s) domin bada kariya ga Usman, ya bayyana cewa dalilin da ya sa shi aika su shi ne hana kisan gilla da kuma kai masa abin ci da ruwa, ba wai hana cire shi daga kujerar halifanci ba, saboda ai ya cancanci a cire shi sakamakon irin ayyukansa da yake yi.

 

Zuriyar Imam Hassan (a.s).

          Zuriyar Imam Hassan (amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun ci gaba ta hanyar Al-Hassan Al-Muthanna, Zaid, Umar, da Al-Husain Al-Athram, zuriyarsa ta yanke daga Husaini da Umar bayan wani lokaci, sannan nasabarsa ta kasance ta hanyar Al-Hassan Al-Muthanna da Zaid, kuma ana kiran ‘ya’yansa da Assadatul Hasaniyah, kuma galibin wadannan Sadat din Suna da harkar siyasa da ayyukan zamantakewa a karni na biyu da na uku bayan hijira. da kuma hannu wajen juyin-juya-halin da aka yi kafin mulkin Abbasiyawa, sun kuma kafa daular Musulunci a kasashen Musulunci daban-daban, a wasu wurare kuma ana kiransu da sunan Shurafa’u.