Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

23 Maris 2024

17:55:56
1446332

Manzon Allah (S.A.W) Ya Ce: “Mafificin Aiki A Cikin Watan Ramadan Shi Ne Nisantar Aikata Sabo”.

Manzon Allah (saww) yana cewa: "Akwai yawa daga masu azumi, wadanda kawai basu da wani kasu na lada daga azuminsu sai ta yunwa da kishirwa".

Wani bangaren na hudubobin sallar Juma'a na wannan mako a birnin Aalishahr a ranar 22/03/2024 daga Hujatul Islam Hamidinejad limamin birnin Jumashahr.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA –  ya kawo maku takaitaccen wani sashe na bayani hudubar juma’ah daga birnin AliShahri kamar haka don anfanuwar Al’ummah: A bangaren karshe ta hudubar Shaba’aniyya, Sayyidina Ali (a.s) ya yi wa Manzon Allah (s.a.w) wata tambaya da dukkanmu muke son yin wannan tambayar, wacce wannan tambayar ita ce shin wane aiki ne mafificin ayyuka a cikin watan Ramadan?, dukkanmu muna jira da shaukin jin Amsar mai matukar muhimmanci da ya kamata mu lura da bada hankalinmu gareta, sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “mafificin aiki a cikin watan Ramadan shi ne nisantar aikata sabo”, mu lura alhali yazo a ruwayoyi an kawo akan yawan ladar da ake cikin karatun Alkur'ani da yin sallah da ayin Addu’ah dama taimakon mabukata da ciyarda mai azumin na buda baki, amma dukansu ba’a anbace su ba a sai annabi ya anbaci “rashin yin zunubi ya fi duk waxannan ayyuka domin zunubi yana sa a kore azuminmu yaki karbuwa, kuma ya sanya a kore mu daga bakuncin Allah, kuma a hana mu falalar samun rahama da gafarar Allah.

A cikin wata ruwaya da aka ruwaito daga Manzon Allah (saww) yana cewa: "Akwai yawa daga masu azumi, wadanda kawai basu da wani kasu na lada daga azuminsu sai ta yunwa da kishirwa, a yau, abin takaici, an shirya tare da shimfada fagage na aikata manyan laifuka a cikin sararin samaniya ta sada zumunci, wanda suka hada da bugawa tare da yada abubuwan da suka shafi zage-zage, karya, ko tuhume-tuhume, wanda ke zubar da martaba da mutuncin mumini, wanda wadannan ayyukan sun hana mu samun falalar Allah a cikin watan Ramadan, kuma hakan yana sanyamu  koma baya maras misaltuwa.

Me ya sa ba tare da tabbatarwa ba muke buga tare da yada duk labarin da ya zo mana ba tare da bincike ba, alhali yana saurin yaɗuwa tsakanin miliyoyin mutane kamar saurin yaduwar haske, kuma ta hakan muna zubar da mutuncin mumini, wanda ya fi Ka'aba daraja a wurin Allah.

Makiya Musulunci suna neman mafi kankantar kafa da kyamarorin leken asirinsu don aukawa al'umma da kuma yanke tsammaninsu da fatansu da hakan tare da bata musu suna da kawar da martabar manyan mutane da manyan jami'an kasar nan domin samun amfanin kansu da cimma burinsu na rugujewar tsari mai tsarki na Jamhuriyar Musulunci, saboda haka mu me zai san ya mu yi sakaci da shi, Musulunci ya hana mu bayyanar da aibobin wasu, domin lalle musulunci ya hana mu yada laifi ko kuskure idan muka ga kuskure ko aibi ko gibi ga mumini wanda ko shakka babu ya aikata wannan kuskuren, kuma hakan yana ganinsa a matsayin babban zunubi, kuma kamar yadda aya ta 19 a cikin suratul Nur, ta fada akwai narkon azaba mai radadi za ta riski wadanda suke aikata hakan a duniya da lahira, ma’ana masu son yada zunubai da muminai suka aikata ga wasu, don haka 'yan'uwa maza da mata, mu kiyaye kada Shaidan ya yi galaba a kanmu, harya kai ga shigar da mu wuta.