Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

23 Maris 2024

09:48:03
1446222

Labarai Cikin Hotuna Na Yadda Aka Gudanar Da Taron Haɗin Kan Musulmi A Ƙasar Saudiyya

Labarin dake biye ya bayyana yadda wata ƙungiya mai suna Rabidhatul Alamil Islami ta shirya taron haɗin kan dukkan ɓangarorin musulmi na duniya a Ƙasar Saudiya.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Kamar yadda kuke gani a cikin hotunan nan, an gayyaci kusan kowane ɓangarorin addinin Musulunci, SHI'A, da QADIRIYYA, da WAHABIYAWA', da IZALA, da TIJJABIYYA, QUR'ANIYYUN, da dai sauran ɓangarori.

An shirya wannan taron ne a kasar Saudiyya, domin tattaunawa yadda za a sa samun haɗin kai tsakanin al'ummar Musulmi domin ƙalubalen da Msulunci da Musulmi ke fuskanta a duniyar yanzu.

Samada shekaru 30 zuwa arba'in, Marigayi Imam Khomaini jagora Juya halin Musulunci na ƙasar Iran shi ne ya fara kira ga dukkan Musulmi da su haɗe kansu wurin guda, domin tunkarar kafircin duniya.

Anan Nijeriya ma haka, Jagora Allama Syed Ibraheem Zakzaky(H) ya ɗauki shekaru sama da 30 ya na kiran al'ummar musulmin wannan Nahiya ta mu da su haɗe kansu domin fuskantar zalunci da kafirci da kuma tabbatar da adalci.

Akwai fuskokin wasu daga cikin Malaman Wahabiya daga Nijeriya da duka halarci taron, muna fatar ya zama sun isar da wannan saƙon na hadin kan musulmin wannan kasa cikin hikima da tausasa lafazi.

Mai nakaltowa: Almujtaba Abubakar