Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

22 Maris 2024

17:01:38
1446148

Kudurin Son Zuciya Na Amurka Kan Gaza Bai Samu Karbuwa Ba

Kwamitin Tsaro Na Majalisar Dinkin Duniya Na Kada Kuri'a Kan Kudirin Tsagaita Bude Wuta A Gaza

Kwamitin Sulhu ya kada kuri'a kan kudurin da Amurka ta gabatar' amma kudirin bai kaiga gaci ba saboda ya goyi bayan tseratar da gwamnatin Yahudawa daga hukuntawa daga dukka ayyuakn ta'addancin data gudanar a Gaza.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA –  ya habarta cewa: Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yana gudanar da wani taro domin kada kuri'a kan kudurin da Amurka ta gabatar na tsagaita wuta a Gaza.

Kudurin da aka gabatar ya hada da tsagaita bude wuta nan take na tsawon makonni 6 domin kare fararen hula da kuma samar da yanayin isar kayan agajin.

Kudirin ya kuma goyi bayan yunkurin diflomasiyya na kasa da kasa na samar da tsagaita bude wuta don kubutar da dukkan fursunonin da suka rage, wanda ke nufin yin shawarwari tare da shiga tsakani na Amurka, Masar, da Qatar.

Kudirin bai bukaci a tsagaita wuta kadai ba ne,  aha ah sai dai ya jaddada bukatar tsagaita bude wuta cikin gaggawa domin kare fararen hula daga kowane bangare da kuma bukatar ba da damar isar kayan agaji na yau da kullun don rage radadin al'ummar kasar.

Har ila yau, kudurin da aka gabatar ya nuna adawa da matakin tilasta yin hijira na fararen hula daga Gaza, yana mai kallonsa ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Ita ma Faransa ta yi taruka a bayan fage a cikin makonni biyun da suka gabata tare da halartar mambobin kwamitin sulhu, na shirin wani kuduri da aka gabatar, wanda mai yiwuwa ya mayar da hankali kan tsagaita wuta na dindindin a wani lokaci.

Domin samun amincewar komitin sulhun, kudurin na bukatar kyakykyawan kuri'ar kasashe tara daga cikin kasashe 15 na wannan majalisar da kuma rashin amfani da matakin na veto daga Amurka, Faransa, Ingila, Rasha ko China.

Amfani Da Hakkin Veto

Tun farkon yakin da ake yi da Gaza, daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, Washington ta yi amfani da ikonta na veto ga kudurori uku da aka gabatar dangane da yakin Gaza, wadanda biyu daga cikinsu suka bukaci a tsagaita bude wuta nan take.

Adadin shahidai da kuma wadanda suka jikkata a Zirin Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023 ya kai shahidai dubu 32, yayin da wasu 74,188 suka jikkata, wadanda akasarinsu mata da kananan yara ne, baya ga wasu dubban wadanda abin ya shafa suna karkashin baraguzan gine-ginen da aka lalata a zirin Gazan.

Kudurin Son Zuciya Na Amurka Kan Gaza Bai Samu Karbuwa Ba

Yayin da Amurka ta yi watsi da kudurin da dukkan kasashen kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya suka amince da shi na tsagaita bude wuta a Gaza sau da dama, amma a wannan karon ba a amince da kudirin da Washington ta gabatar ba, wanda ta gabatar da shi domin goyon bayan gwamnatin sahyoniyawa.

Rahotanni sun ce, kasashen Sin da Rasha sun ki amincewa da daftarin kudurin da Amurka ta gabatar wa kwamitin sulhu na MDD domin tsagaita bude wuta a Gaza.

Wakilin kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa an gabatar da daftarin kudurin na Amurka ne a daidai lokacin yazo ne domin kokarin ceto Isra'ila daga hukuntawa kan ayyuakn ta’addanci da ta aikata a Gaza.