Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

21 Maris 2024

13:21:22
1445925

Juyayin Wafatin Ummul Mu'uminina Sayyidah Khadijah As

A Irin Wannan Ranar Ne dai Sayyadah Khadijah As Tayi Wafati A Shekara Ta Goma Bayan Aiko Manzon Allah Sawa.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya kawo maku takaitaccen bayani dangane da wafatin Sayyadah Ummul Muaminin Khadijah Yar Khuwailid A's Mahaifiya ag Sayyidah Fadimah As ta shahara da sunan Alkubrah, itace matar Annabi ta farko wacce ya aureta tun kafin a aiko da Annabi kuma itace wacce tafara Imani da annabi Muhammad sawa bayan imam Ali as takasance daga shugabannin Kuraishawa daga madaukakansu ana kiranta da Dahira tun alokacin jahiliyya kuma Annabi yayi mata lakabi da Alkubraa kamar yadda Littafan tarihi suka kawo cewa An haifeta a shekara 68 kafin Hijira .

 Manzon Allah ya aureta yana dan shekara 25 inda tahaifasa ya da suka hada da Sayyid Alkasim, Abdullah, Sayyidah Zainab, Ruqayyah, Ummu kulsum da Sayyidah fadimah AS. Wanda har tai wafati manzon Allah bai auri wata mace ba banda ita, ta tsaya akan gefen manzon Allah tana mai taimakon sad a Addainin da yazo dashi da dukkan abinda ta mallaka, inda tabayara dad a dukiyar wajen aganin wannan kira da Annabi sawa yazo yayi nasara kuma dukkan burin da Annabi yakek dashi da Addinisa ya tabbata. 

 Manzon Allah yakasanace yana mai tsananin sonta inda bai gusheba har bayan wafatinta yana mai anbatonta da yabonta yana mai jimamin rashinta inda yasanyawa shekara da tayi wafati ita da Sayyid Abu dalib da shekara bakinciki .

 Sayyidah Khadijah as tayi wafati ne a garin Makka tana da shekaru 65 A shekara ta uku bayan Manzo da muminai sun shiga wannan yanayin qunci Wato cikin wannan kurkukun, sai Allah (swt) ya yi wa Nana Khadija (as) rasuwa, wanda wannan ya fi girgiza su fiye da halin da suke ciki, Musamman ma shi Manzo Allah (as) da diyarsa Fatima (as).

 A cikin wannan lokacin ne rashin lafiya mai tsanani ya kama Nana Khadija (as) har ta samu shu'urin cewa za ta koma ne ga Ubangijinta Madaukaki

Takan kira Nana Fatima (as) ta zaunar da ita kusa da ita tana kallonta kallo na tausayi da bankwana. tana kuka ita ma Fatima (as) tana kuka.

 Har sai da Asma'u binti Umais ta ce mata "Ya Khadija me ke sa ki kuka ne, Ashe ba ke ce Shugabar matan Aljanna ba. Ba ke ce matar Shugaban Ma'aika ba'? Ashe Manzo bai yi miki albishir da Aljanna ba? To me ya sa kike yawaita kuka"

Sayyed khadeeja Sai ta budi baki ta ce mata 'Ba wani abu ke sa ni kuka ba, sai dai zan yi wafati in bar Fatima (as) tana karama wanda nan gaba in ta yi aure ba wacce za ta dinga gaya mata al amuranta na sirri.

 Kin san 'ya mace kuwa tana bukatar wacce za ta dinga gaya mata sirrinta bayan ta yi aure.

Daga nan sai Asma'u binti Umais ta ce mata "Na yi miki alkawari matukar ina raye zan wakilce ki a wannan lokacin.

Kuma Gaskiya Asmau ta cancanci yabo, domin ta cika alkawan Duk haihuwar da sayyeda Fatima (as) take yi Asma'u ce ke yi mata unguwar zoma kuma ta yi ruwa ta yi tsaki cikin al amuran Fatima (as) har zuwa wafatinta.

Wannan rasuwa ta Khadijah dai ya kasance babban rashi ga Ma'aikin Allah da kuma 'yarsa Fatima (a.s) inda har tazo tana kuka tana ce Wa Mahaifinta (s) ina mahaifiyata? Abunda ke Kada zuciyar Manzon Allah ( s ) Akan Haka Allah ( s.w.a ) Ya aiko Mala'ika Jibril (a.s) ya sauko ya ce wa Annabi (s) Ka ce wa Fatima cewa Allah Madaukaki Sarki Ya gina wa ma haifiyarta gida a aljanna da zinari.