Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

20 Maris 2024

02:29:25
1445645

Hujjojin Ilimi Kan Tasirin Karatun Kur'ani Da Haddarsa Wajen Inganta Lafiyar Jiki Da Kwakwalwar Musulmi.

Lalle ne Musulmin da suka haddace Al-Qur'ani suna da ingancin rayuwa da rashin damuwa da fargaba.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya kawo maku cewa: sakamakon wani bincike da aka gudanar kan tasirin karatun kur’ani da saurare da kuma haddar kur’ani a kan lafiyar kwakwalwa da jikin musulmi, wanda aka buga a shafin yanar gizo na Pubmed mai alaka da Dakin karatu na likitanci na Amurka, ya tabbatar da cewa musulmin da suka haddace Al-Qur'ani suna da ingancin rayuwa da rashin damuwa da fargaba.

Sakamakon bincike ya nuna cewa saurare, karantawa ko haddar Al-Qur'ani yana da tasiri mai kyau a kan damuwa, fargaba, yanayin lafiyat jiki, ingancin rayuwa, ingancin barci ga mai aikata hakan.

Shaidu a cikin wannan bincike na nuni da cewa saurare ko karantawa ko haddar Al-Qur'ani na iya zama da amfani a matsayin kariya don inganta lafiyar jiki da ta hankali.

...................................