Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

18 Maris 2024

09:55:57
1445306

Ministan Yahudawan Sahyoniya Ya Bukaci A Kashe Haniyah A Qatar

Ministan kudi na gwamnatin sahyoniyawan ya yi kira da a kashe Ismail Haniyah, shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas a Qatar.

Kamfanin dillancin labaran Kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA- ya bayar da rahoton cewa, Betzalel Smotrich ministan kudi na gwamnatin sahyoniyawan ya yi kira da a kashe Ismail Haniyah shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas a kasar Qatar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Khalij Online cewa, a wata hira da ya yi da wata kafar yada labarai ta yahudanci, ya ce kamata ya yi shugaban Mossad David Barnia ya tafi Qatar don kashe Haniyah ne ba wai yaje tattauna da shi ba.

Ministan kudi na gwamnatin Sahayoniya ya jaddada cewa: Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar gaba daya ya gaza a ranar 7 ga watan Oktoba, kuma bai kamata shi ne zai tantance tsarin sojojin mu a nan gaba ba.

A baya dai Smotrich ya bukaci Benjamin Netanyahu firaministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da ya hana tawagar yahudawan sahyuniya zuwa kasar Qatar domin yin shawarwarin tattaunawa na tsagaita wuta da musayar fursunoni da Hamas.

Kafin haka dai kafafen yada labaran yahudawan sun bayar da rahoton jinkirin da aka samu a tafiyar wakilan yahudawan sahyoniyan zuwa Qatar.

....................