Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

18 Maris 2024

05:03:30
1445258

Rundunar Sojan Yaman Sun Gudanar Da Atisayen Tunkarar Yiwuwar Kai Hari Ta Kasa Daga Bangaren Kawancen Amurka

Sassan Cibiyar rundunar sojan Yaman sun gudanar da atisayen tunkarar yiwuwar kai hari ta kasa daga bangaren kawancen Amurka.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (a.s) – ABNA –  ya habarta cewa: An gudanar da wannan atisayen ne tare da halartar sojoji 1,000 na injiniyoyi, da tankokin yaki, da maharba, da na'urorin yaki da manyan bindigogi, da kuma dukkanin motocin yaki iri-iri.

A wannan atisayen da aka yi a karkashin taken "Ranar Alkawari" an kwaikwayi tsarin tunkarar hare-haren jiragen sama na kawancen Amurka da Birtaniya da kuma kutsawa wasu yankuna tare da taimakon sojojin gwamnatin da ta yi murabus.