Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

17 Maris 2024

17:17:56
1445118

Martanin Netanyahu Kan Sukar Amurka:

Netanyahu: Ta Yaya Kuka Manta Da Ranar 7 Ga Oktoba? /Maimakon Ku Matsa Mana Lamba Ku Matsa Iran da Hamas Mana.

Netanyahu ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ko mika wuya wajen matsin lamba da Amurka ke yi na dakatar da yakin Gaza, domin a halin da ake ciki, dakatar da yakin na nufin nasarar Hamas.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Kafofin yada labaran yahudawan sahyoniya sun ce: bangaren cikin gida ba a shirye yake ba wajen ballewar yakin yanki a gabas ta tsakiya wanda matsalar da zai haifar ta fi sau dubunnan wahala da hadari fiye da yakin zirin Gaza ya haifar.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun ruwaito cewa: Abin da ya faru a zirin Gaza da kuma kan kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon zai cutar da mu ko ba dade.

Bangaren cikin gida ba ya shirye ga bullar yakin yankin da ya fi sau dubunnan wahala da hadari fiye da yakin zirin Gaza.

Babban Hafsan Sojoji (Gwamnatin sahyoniya) ya ware kuma ya yi shiru ya rasa iko a filin na tsawon lokaci, muna cikin badakalar mafi hadari tun kafa rundunar soji da gazawa mafi hadari tun kafa rundunar sojojin "Isra'ila".