Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

17 Maris 2024

17:05:41
1445117

Nijar Ta Yanke Duk Wata Alakar Yarjejeniyar Soji Da Amurka + Bidiyo

Gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar ta sanar a daren ranar Asabar da ta gabata cewa ta dakatar da duk wasu yarjejeniyoyin soja da hadin gwiwa da ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, wanda hakan ya kawo karshen zaman sojojin Amurka a wannan kasa da ke yammacin Afirka

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya nakalto maku daga tashar labarai ta Iran Press cewa: Matakin soke yarjejeniyar ya zo ne bayan wata ziyara da jami'an Amurka suka kai, ciki har da mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka Molly Phee da Janar Michael Langley, kwamandan rundunar sojin Amurka a Afirka. 

Kanar Amadou Abdramane ne ya sanar da hakan ta gidan Talabijin na kasa a madadin Janar Abdourahamane Tchiani, shugaban majalisar tsaron kasar.

Kanar Abdramane ya bayyana cewa, ba a sanar da Nijar game da batu da ranar da jerin tawagar Amurka za su zo ba, kai harma da ajandar ziyarar ba a sanar ba. Ya bayyana nadamarsa kan abin da ya dauka a matsayin yunkurin tawagar Amurka na yin katsalandan ga ‘yancin kasar Nijar wajen zabar abokan huldar ta wajen yakar ta’addanci.

Tattaunawar da aka yi a yayin ziyarar ta bayyana cewa, ta mayar da hankali ne kan hadin gwiwar soji a tsakanin kasashen biyu da kuma zabin kasar Nijar na kawancen yaki da mayakan da ke da alaka da al-Qaida da IS. Gwamnatin Nijar ta yi Allah wadai da abin da ta bayyana a matsayin wani hali da kuma barazanar da shugaban tawagar Amurka ke yi wa gwamnati da al'ummar Najeriya.

Sakamakon haka, Nijar ta soke duk wasu yarjejeniyoyin da suka shafi matsayin jami'an sojan Amurka da ma'aikatan farar hula a yankinta ba tare da bata lokaci ba. Wannan matakin dai ya kawo karshen kasancewar kusan sojojin Amurka 1,100 a Nijar, wadanda suka yi aiki daga sansanoni biyu da suka hada da Airbase 201 kusa da Agadez.

Wannan matsayin hukunci ya zo ne bayan da Faransa ta janye gaba daya sojojinta daga Nijar a watan Disambar 2023 bayan zanga-zangar kin jinin Faransa a Yamai. Jama'a da dama a Nijar sun yi bikin wannan a matsayin wani mataki na samun 'yancin kai na gaskiya ga kasarsu.