Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

17 Maris 2024

08:01:56
1445016

Mataimakin Shugaban Kungiyar Shi'a Na Balochistan Ya Yi Shahada

Haji Ramzan Ali ya kasance daya daga cikin fitattun jagororin yankin Hazara na kasar Pakistan, wanda ya kasance mai himma wajen gudanar da harkokin addini, siyasa da zamantakewa, ya yi shahada a wani hari da wasu 'yan ta'adda suka kai masa.

Kamfanin dillancin labaran Kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA- ya habarto maku cewa: Haji Ramzan Ali mataimakin shugaban kungiyar shi'a ya yi shahada a wani harin ta'addanci da aka kai a birnin Quetta fadar gwamnatin lardin Baluchistan na kasar Pakistan.

 A cewar labarin da aka buga, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba ne suka harbe Haji Ramzan Ali a gidansa da ke yankin Hazara.

A cewar dan uwansa, wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai masa hari bayan sun ziyarci kofar gidan Haji Ramzan Ali inda a wannan harin ya samu rauni kuma nan take aka kai shi asibiti.

   Sai a yau kuma aka wallafa wani sako a shafukan sada zumunta cewa Haji Ramzan Ali ya rasu sakamakon raunukan da ya samu.

   Ya kamata a lura da cewa, Haji Ramadan Ali ya kasance yana shirya muzahara ta Muharram da sauran tarukan addini a yankin Hazara na Quetta.

Bugu da kari, ya gudanar da wasu ayyuka na taron Shi'a na Baluchistan.

  Rundunar ‘yan sanda dai na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin kuma kawo yanzu babu wata sanarwa da ta fitar.

Hujjatul-Islam Dr. Shabir Hasan Maithami, babban sakataren majalisar malaman Shi'a na Pakistan, ya yi kakkausar suka kan shahadar Haji Ramzan Ali tare da nuna matukar takaici, ya kuma bukaci gwamnati da ta gaggauta kamo wadanda suka kashe wannan fitaccen dan kabilar Hazara.

Ya bayyana cewa Haji Ramzan Ali na daya daga cikin fitattun jagororin birnin Hazara da ke da hannu a harkokin addini da siyasa da zamantakewa inda ya ce: Idan da a ce an kewaye da yiwa 'yan ta'adda kofar rago a duk fadin kasar nan, da ba a taba faruwa ba.

Shabir Hasan Maithami ya jaddada cewa: Domin hana afkuwar irin lamarin, ya kamata a gano masu aikata laifukan dake da hannau aciki, sannan a lalata ‘yan ta’adda da suka hada da masu horas da su tare da masu tsare-tsare da tsara aikin ta’addanci don hana asarar rayuka masu daraja.