Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

15 Maris 2024

12:49:24
1444535

Masanin Iran: Muna Samun Sakonni Da Matsin lamba Don Janye Tallafi Ga Falasdinu

Tsohon mai ba Iran shawara kan al'adu a Qatar, Kuwait da Lebanon kuma mataimakin shugaban jami'ar addini da mazhabobi a al'adu, Dr. Abbas Khameh Yar, ya bayyana cewa "Tehran a ko da yaushe a cikin bayyananniyar siffofi tana karbar saƙonni na matsin lamba da kuma barazanar masu shiga tsakani...

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Abbas Khameh Yar ya yi nuni da cewa, guguwar Al-Aqsa ta haifar da gagarumin sauyi a matakin yanki da duniya.

Tsohon mai ba Iran shawara kan al'adu a Qatar, Kuwait da Lebanon kuma mataimakin shugaban jami'ar addini da mazhabobi a al'adu, Dr. Abbas Khameh Yar, ya bayyana cewa "Tehran a ko da yaushe a cikin bayyananniyar siffofi tana karbar saƙonni na matsin lamba da kuma barazanar masu shiga tsakani, abokai da abokan hulda (wadanda bai ayyana su ba) domin a samu sauyi... Matsayinta na tallafawa al'ummar Palastinu."

Ya fadi hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da tashar "Arabi 21": "Tun daga ranar 7 ga watan Oktoba zuwa yanzu, ana samun cunkoson na masu kaiwa da kawowa sakamakon yawan masu shiga tsakani, ko a Beirut, ko kuma a wasu manyan biranen Larabawa da na Musulunci da suka gwammace tsayawa tare da tsarin turawan mulkin mallaka na goyon bayan sahyoniyawan, Tehran na fuskantar matsin lamba na Wadannan sakonni da suke isa gare mu ta hanyar gwamnatocin hukuma ko kungiyoyin kasa da kasa."

Tsohon jami'in diflomasiyyar na Iran ya kara da cewa: Wannan wasikun suna zuwa da salo daban-daban, kuma mun lura da wani nau'i na sauyi a cikin 'dan lokacin baya bayan nan ba kamar yadda aka saba ganinsu ba. kuma dalili shi ne manyan sauye-sauyen da muke gani suke faruwa. kuma ra’ayin jama’a na duniya yana shaida hakan, wanda da ace ‘yan’uwa dake cikin harkar Hamas sun san girman tasirin.” Abin da suka haifar a ranar 7 ga Oktoba a matakin yankin gabas ta tsakiya da na duniya da sun canja sunan abun daga (Guguwar Al-Aqsa) (Tsunamil Al-Aqsa).

Wannan abun ke kasa bayanin cikakkiyar tattaunawar ta musamman ce da yayi da tashar “Arabi 21” da ke Tehran.

Mai Gudanarwa: Yaya kuke kallon matsayin Iran kan batun Palastinu?

Dr. Abbas: Kusan rabin karni bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, da kuma matsayi na zahiri da Iran ta dauka a kan al'ummar Palastinu, da kuma tsawon shekaru da dama da suka gabata, al'amura sun bayyana ga kowa da kowa, kuma wannan wani abin alfahari ne da Iran ta kasance a kodayaushe dukkanin farashin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta biya a cikin shekaru da dama da suka gabata, ya zo ne a kan farashi mai tsada, bayan bayanan matsayinta kan tabbatar da adalci na Palastinu da al'ummar Palastinu; Sakonnin da suka isa Iran da suka hada da barazana da kakaba takunkumi duk suna cikin wannan tsari, kuma lamarin ya bayyana ga kowa da kowa.

Falasdinawa sun fi cancanta su amsa wannan tambaya, Palasdinawan dake bangaren siyasa da wanda suke bangaren soja. Al'amarin Palastinu shi ne mafi girman tsaro na tsare-tsare kuma matsala ta asasi na duniyar musulmi, kuma wannan shi ne abin da Iran ta yi imani da shi a ko da yaushe.

Dubi jawabin tarihi na Imam Khumaini a yunkurin juyin-juya-hali na 15 na Khordad (5 da 6 ga Yuni, 1963), lokacin da aka fara boren daga makarantar hauza na addini a birnin Kum bayan shahararren jawabinsa na tsawon kimanin sa'a guda, inda ya yi jawabi a cikinsa ya ambaci "Shah" sau 15. Jawabin dai ya yi nuni ne da adawa da kama-karya da mulkin kama-karya, to amma a cikin jawabinsa ya ambaci Isra'ila har sau 18, sannan ya alakanta aikin 'yan mulkin mallaka na sahyoniyawa da aikin zalunci da kama-karya na Iran, idan har wani abu yana nuni da matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma tsarin mulkin kasar Iran. Muhimmancin batun Falasdinu ga juyin juya hali, wanda Isra'ila ta yi la'akari da shi a lokacin "Girgizar kasa mafi girma da ta girgiza 'yan sahayoniya."

Mai gudanarwa: To amma akwai sukar da ake yi wa Iran, wasu kuma na cewa ba ta da wani tsayayyen mataki na kwarai data dauka wajen tunkarar mamayar, kuma cewa ta yi watsi da gwagwarmayar Palasdinawa ko wani sashe kadan daga ita, a cikin tambayoyin da ke cewa: Ina hadin kan fage... Menene? sharhin ku akai?

Dr. Abbas: Hadin kan fagagen gwagwarmaya da suka dangana tun daga Bagadaza zuwa Sana'a zuwa Beirut zuwa Damascus da kuma Tehran... Shin gwamnatin Larabawa ce ke jagoranta ko kuma tana goyon bayanta?!! Falasdinawa sune kadai su zasu amsa wannan tambaya.

Ina gwamnatin larabawa a hukumance?!! kuma ina dakarun musuluncin da suke karewa da magana (kan Palastinu)?!! Kuma ina dakarun da suke da tushe mai farin jini jama'a a kan lamarin Palastinu, duk da mun san halin da ake ciki, da matsin lamba; dama saman hakan na daga cikin wadannan batutuwa, kuma dole ne kowa ya amsa wannan tambayar da ke cewa: Wanene ke jagoranta da gudanar da yaki a Yemen, Baghdad, Tehran, da Beirut?

Sukar da ake yi wa Iran wani bangare ne na yakin tunani da kafafen yada labarai da daulolin yada labarai ke jagoranta, wadanda suke goyon bayan tsarin Sahyuniyawa kuma suke gudanar da wannan yaki akan Gwagwarmaya da tsayin daka da dukkan nau'o'insu da ma'aunansu, kawai burinsu shi ne su gurgunta hadin kan fagen musulmi ne.

Hadin kan fage a yanzu shi ne mafi mahimmanci, mafi kyau, kuma mafi girma, kuma yana taka wannan jagoranci mara misaltuwa sama da na farko a cikin shekarun da suka gabata. Shin akwai wani da zai iya inkarin Matsayin Yamen akan matsin lambar ta a bangaren tattalin arzikin tsarin Sahyuniyawa ko yayi inkarin matsayin gwagwarmaya a kudancin Lebanon, ko matsayin goyon bayan Tehran, ko matsayin wasu kasashen musulmi a duniya?; to kaga wannan mai suka da magana... Ina matsayinsa yake dangane da batun Palastinu, ina kuma matsayinsa a batun tallafawa da taimakawa al'ummar Gaza?

Ina malaman sarakunan da suke da makirufo da manyan dandali na Musulunci a duniyar Musulunci? Dubi yadda suke magana game da yunkurin Hamas, da kuma yadda suke magana kan sojojin Palasdinawa, da kuma yadda suke zarginsu da tsayawa kyam ga tsayin daka da gwagwarmaya, matsayinsu ya zama abin kunya da kunya matuka, kuma dole ne a yi suka bisa la'akari da matakin da suka dauka mugun shiru da muke gani nan da can.

Matsayin Iran a fili yake kuma har yanzu yana nan a fili da goyon bayansa ta kowace fuska game da lamarin, kuma wannan shi ne abin da Palasdinawa a Gaza da yammacin kogin Jordan suke magana a kai, a fagen yaki, a fagen siyasa, da ma cikin ramukan kasa. Babu wanda zai iya musun wannan matsayi.

Mai gudanarwa: Iran ta sanar fiye da sau daya cewa tana goyon bayan "gwagwarmaya" a Falasdinu da yankin to mai zai faru Idan babu goyon bayan Iran ga dakarun gwagwarmaya?

Dr. Abbas: Wajibi ne wannan tambaya ta kasance ga masu zargin Iran da yin watsi da lamarin Palastinu, kuma wannan tambaya ce mai matukar muhimmanci, idan ba ta zamo mai dafawa ga wadannan dakaru masu goyon bayan al'ummar Palastinu a fagagen Musulunci da na Larabawa wadanda ake kira da yan gwagwarmaya.

Tsawon tsayin daka a yanzu ya zama mai daidaitawa da dunkulewa, yana da dabara mai ma'ana, kuma yana shiga fagen fama da karfi, amma hakan ba zai ba Netanyahu damar ba da hujjar fadada wannan yaki da kuma ba shi dalilai ba.

Fagen gwagwarmaya shi ne kashin baya, shi ne ginshikin tantuna, kana iya tunanin yadda lamarin Palastinu zai kasance idan babu goyon bayan Iran? Kuma ina sake maimaitawa, ina masu suka? Ina gwamnatin Larabawa a hukumance suke. Ina kasashen da suke makwabtaka da Falasdinu da aka mamaye, kuma me yasa wannan mummunan shiru, da wannan hadin kai wajen yin shiru, me yasa wannan makirci na goyin bayan mamaya?

Wannan wata dama ce mai cike da tarihi ta bude iyakokin kasa, bude sararin sama da mashigin ruwa, da kuma bayar da babban taimakon da ake samu a kan iyakokin, wanda ke zuwa daga ko wane bangare, kuma a bawa tare samarwa da wadannan al'ummomi masu sadaukarwa izini don tallafa wa al'amuran Palasdinawa, da kuma ganin masu rige-rige da masu gasa don tallafawa waɗannan ayyuka masu kyau, kuma goyon bayan dole ne ya kasance ba mai ƙarewa ga mutanenmu na Falasdinu.

Mai gudanarwa: Yaya za ku mayar da martani ga masu cewa gwagwarmaya ta zama makami ce kawai a hannun Iran?

Dr. Abbas: Mutanen da ke nesa da batun Falasdinu da goyon bayan al'ummar Palastinu ne ke gabatar da wadannan kalamai, kuma suna iya yin wadannan tambayoyi don hana samun damar sanin hakikanin abin da ke faruwa a kasa. Idan Iran ta shiga tsakani kuma ta goyi bayan gwagwarmaya, sai su ce wannan lamari ne na Iran, sannan sai suna zargin Falasdinawa da kasancewa wani bangare na shirin Iran da take aiwatar da shi, kuma idan Iran ta dauki wasu matakai na dabara a cikin wannan yanayi, kuma ba ta bayyana zurfin goyon bayan da aka bayar ba. Sai kaji Tambayoyi sun taso: "Me yasa wannan shiru da keɓancewa, kuma me ya sa rashin goyon bayan Iran?" ".. Ko yaya ta aikita za ku tarar da na'urar hira ta kafofin watsa labaru tana gudanar da aikinta na musamman na surutai tare da shirin soja na mulkin mallaka na sahyoniyawan da kuma tsaro. dukkansu al'amura ne da ba shi gaba ba da juna kuma ba su jinkirtuwa, kuma suna yunƙurin sharranta gwagwarmaya ta kowace hanya ta ƙeta.

Iraniyawa tun bayan bayyanar juyinsu da kuma kafin wannan lokacin, sun kuduri aniyar goyon bayan al'ummar Palastinu, kuma a ko da yaushe suna biyan farashi mai yawa, kuma dukkanin sakonnin da suke isowa Iran can da can, a boye da a bayyane, suna bukatar Iran ta sauya matsayinta kan batun Falasdinu, domin kawo karshen harin kawanya da aka yi mata.

To amma Iran tana tafiya a kan wannan al'amari bisa ka'idoji da dokoki, kuma ba za ta yi watsi da manufofinta ba, kuma wannan lamari ya bayyana a fili ga kowa da kowa.

Mai gudanarwa: Shin Tehran ta samu wasu sakonnin da ba a sanar da su ba a lokutan baya don sauya matsayinta kan lamarin Palastinu?

Dr. Khameh: Na'am, lalle an samu, kuma wadannan "wasiku" ko in ce matsin lamba da barazana suna ci gaba da wanzuwa daga abokai da kawayenta, kuma matsin lamba na ci gaba da gudana, kuma Iran ta san cewa makiya suna son mayar da manyan bangarorin Musulunci a yankin saniyar ware.

Isra'ila aikin mulkin mallaka ce ƙarara, ba wai kawai matsayin mayaye ne da ita ba- kamar yadda mai tunani dan Aljeriya Malek Bennabi ya ce -; A karon farko mun ga jiragen yakin Amurka da na yammacin turai sun shigo yankin tare da shugabanninsu, kuma a karon farko mun ga jami’an diflomasiyyar Amurka da na yammacin Turai, da shugabanni, da jami’ai na shiga dakin aikin sojan Isra’ila kai tsaye, sanye da kakin soja maimakon rigar diflomasiyya da suka kasance suna sawa, kuma wannan yana nuna mahimmancin wannan aikin, da mahimmancin aiwatar da sanarwar Balfour, 1917, da mahimmancin kiyaye yarjejeniyar Sykes-Picot, don haka shirin mulkin mallaka ne kawai, ba wai kawai wani tsarin mamata ba.

Wannan shirin aikin mulkin mallaka ya shafi dukkan kasashen musulmi ne, kuma takensa shi ne "daga kogin Nilu zuwa Kogin Furat", kuma wani shiri ne mai ma'ana ga kasashen yamma, kuma mun ga yadda ake tafiyar da lamarin Ukraine a fili, da yadda aka ajiye shi a gefe Lokacin da ayyukan intifada ya barke a Gaza da yankunan Falasdinawa, da yadda Ukraine ta zama wani batu na baya-bayan nan a lokacin da aka kulla wannan shirin mulkin mallaka a duniyar Musulunci a Palastinu.

Don haka dole ne a kalli lamarin ta wannan bangare, kuma kada mu bi munanan matakan kuskure wanda makiyanmu da mamaya suke nunawa.

Mai gudanarwa: Su wane ne masu shiga tsakani da suka shawarci Tehran da ta sauya matsayinta na tallafawa al'ummar Palastinu? Wanene ya ce su yi haka?

Dr. Khameh: Masu shiga tsakani suna da yawa kuma sun bambanta, kuma tun daga abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoba zuwa yanzu an sami "yawan kaiwa da komowa na zirga-zirga" wanda yawancin masu shiga tsakani ya haifar da hakan, a Beirut, ko kuma a wasu manyan biranen Larabawa da na Islama waɗanda suka gwammace su goyi bayan mulkin mallaka. Tehran tana fuskantar matsin lamba, kuma a wasu lokuta ana ba ta shawarwari dangane da wannan matsin lamba, kuma wannan nasihar tana zuwa ta hanyar gwamnatocin hukuma ko kungiyoyin kasa da kasa.

Wannan shawarwari suna zo da salo daban-daban, kuma mun lura da wani irin sauyi a salon wannan wasikun a cikin ‘yan kwanakin nan, da kuma sauyin yanayin da aka saba, dalili kuwa shi ne manyan sauye-sauyen da muka shaida da kuma abinda al’ummar duniya suka shaida.

A koyaushe ina cewa: Idan da 'yan'uwa a Hamas, da Palasdinawa gaba daya, sun san girman tasirin da suka yi a ranar 7 ga Oktoba kan matakin ra'ayin jama'a na duniya, a matakin hukumomin yada labarai, kan matakin yammacin Turai ra'ayoyin falsafar siyasa, da kuma ra'ayoyin juyin juya halin Faransanci da sauran juyin juya halin da suka yi kira ga 'yancin ɗan adam, 'yancin mata, 'yancin yara, da cibiyoyi bisa ra'ayi, da sun san girman canjin da suka haifar a tsakanin matasa a kasashen yammacin duniya, da sun maye gurbin sunan yukunrinsu na "Guguwar Al-Aqsa" da "Tsunami Al-Aqsa." Wannan wani muhimmin batu ne ga Palasdinawa da yunkurin "Hamas" da kuma sauran masu jihadi. ƙungiyoyi da gwagwarmaya na ƙasa da na Musulunci a Falasdinu.

Mai gudanarwa: Yaya Tehran ta mayar da martani ga wadannan sakonni?

Dr. Khameh: Wadannan sakwannin ba sabbi ba ne, domin kuwa an fara su ne tun lokacin da Iraniyawa suka daga taken "Yau Iran gobe Falasdinu" a shekarar 1979, kuma tun da dan Imam Khumaini a wancan lokacin Sayyid Ahmad Khumaini ya mika ofishin jakadancin Isra'ila da ke Tehran ga hannun Sayyid Yasir Arafat, “Abu Ammar,” tun daga wannan lokacin har zuwa yanzu wadannan sakonni, takunkumi, da matsin lamba suna ci gaba da gudana, kuma martanin ya kasance a sarari ya kasance a fili wanda shine: ku Dakatar da wuce gona da iri, ku dakatar da mamaya, dakatar da aikin sahyoniyawan, shikenan sai al’amura za su kare. yayin da wani sabon abu shi ne cewa waɗannan saƙonnin sun kasance masu ƙarfi kuma ana lura da su tun lokacin da aka yi guguwar Al-Aqsa.

Idan da Iran tana son daukar wadannan nasihohi, da juyin juya halin Musulunci ya bi wani tafarki kamar sauran juyin juya halin da suka gabata, alhali kuwa al'ummar Iran da gwamnatin Iran a yau, da dukkanin yunkurin da suka yi imani da yakar mulkin mallaka da girman kai, sun fi tsayin daka, da dakewa, da jajircewa da gwagwarmaya, kuma abin da muke gani yana cikin hadin kan fage ne, kuma a cikin wannan sabon salon da ya shiga adabin gwagwarmaya a fage shi ne sakamakon wadannan matsayin, kuma ya samo asali ne daga tsayin daka da kuma matsayin Iran da ta dage akai na tsawon rabin karni.

Mai gudanarwa: Shin Iran na neman kafa sansanonin soji a tekun Bahar Ahmar ta hanyar Sudan, kamar yadda jaridar Wall Street Journal ta ruwaito kwanan nan?

Dr. Khameh: Ban san dalilin da ya sa Iran za ta mayar da martani ga kowace kalma, kowane matsayi, da duk wata magana da kafofin watsa labarai ke yadawa a fadin kasa ba.

Tambayar da ya wajaba a yi wa wadannan mutane: Shin kafa sansanonin soji ya takaita ne kawai ga kasashen da ke da nisan dubban kilomita, wadanda suke sarrafa su da sunan muradun kasa - in har labarin gaskiya ne?

Sansanin Amurka da na kasashen Yamma da suke a duk faɗin duniya, a nasu ra'ayi, sansanoni ne masu inganci kuma masu mahimmanci waɗanda ke da ma'auni mai mahimmanci da dabaru, amma idan akwai wasu sansanoni ga wasu ƙasashe, to haramun ne kuma basu inganta ba.


Sansanonin soji da aka kafa a kasashen yankin ta hannun jami’an yanki ke suna tafiyar da dangantakar da ke tsakanin kasashen yankin ne, to wadannan kasashen sun san yadda za su yi mu’amala da yadda za su tsara dangantakarsu da abokansu ai.

Sudan sun kasance kuma har yanzu suna nan - kuma kowa ya san haka, musamman masu kishin Islama a cikin shekaru da dama da suka gabata - sun san abin da Iran ta samar wa Sudan, kuma al'ummar Sudan sun sani sarai irin hidimomin da har yanzu hukumar Sudan ke ci gaba da yi, kuma Iran ba ta taba tambayi ko nema wani abu ga 'yan Sudan ko sauran al'ummomin yankin sakamakon wadannan ayyuka, a madadin wannan tallafi mara iyaka.

Mai gudanarwa: Shin zai yiwu ko kuma Iran za ta iya shiga yakin kai tsaye da Isra'ila a cikin lokaci mai zuwa? Idan Iran ta shiga yaƙi da Isra'ila mai Ai faru?

Dr. Khameh: yanayi da ci gaban da aka samu su ne ke tafiyar da wannan lamari, kuma yahudawan sahyoniya sun san girman karfi Iran, sun kuma san irin karfin da ake da shi na gwagwarmaya kuma sun san hadin kan da ya shiga adabin soji da mai taken "hadin kan fage" ba za su kuskura su shiga yakin da ba a karance shi ba kai tsaye tare da gwagwarmayar Musulunci a Labanon da Hizbullah ba; To yaya game da su idan sun shiga yaki da runduna mai yawa, kuma mai taka rawa a yankin da ke da karfin soja da tsaro, da kuma farin jini a cikin dimbin jama'a da ɗimbin masu sa kai da ke jiran wannan lokacin?

Iraniyawa da kawayenta a yankin suna da masaniya kan yadda za a tunkari duk wani rikici, ko wani yaki na gaba, da duk wani shiri na mulkin mallaka. Suna da matakin kaifin basira wanda zai sa su tafi akan wannan hanyar, amma tarkon ba zai tsorata su ba, kuma ba za su canza hanyarsu ba. Suna taka tsantsan kuma suna da cikakken shiri, kuma wannan shine abin da turawan mulkin mallaka suka sani sosai sarai.