Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

13 Maris 2024

08:24:34
1444124

Gwamnatin Indiya Ta Aiwatar Da Dokar Zamowa Dan Kasa Inda Ta Kebance Musulmi

Dokar zama dan kasa, wacce aka yi wa kwaskwarima a shekarar 2019, ta ba da damar ba da izinin zama dan kasar Indiya ga bakin haure da ke rike da kasashen Bangladesh, Pakistan, da Afghanistan...

Kamfanin dillancin labaran Kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA- ya habarto maku cewa: gwamnatin firaministan kasar Indiya Narendra Modi ta yanke shawarar fara aiwatar da dokar zama dan kasa da ta ware musulmi, makonni kafin shugaban masu kishin addinin Hindu ya sake neman wa'adi na uku.

Dokar zama dan kasa, wacce aka yi wa kwaskwarima a shekarar 2019, ta ba da damar ba da izinin zama dan kasar Indiya ga bakin haure da ke rike da kasashen Bangladesh, Pakistan, da Afghanistan, matukar ba musulmi ba ne, kuma suna fuskantar tsanantawa saboda addininsu a kasashensu na musulmi.

Gwamnatin Modi ba ta fitar da ka'idojin aiwatar da dokar ba tun lokacin da aka zartar da ita bayan zanga-zangar da rikicin kabilanci da ya barke a New Delhi da sauran wurare a cikin makonnin da aka amince da dokar a watan Disamba na 2019. Wanda an kashe mutane da dama tare da jikkata daruruwan kwanaki a fadan.

Zanga-zangar da ta mamaye Indiya a shekara ta 2019 ta ja hankalin jama'a daga kowane bangare da suka ce dokar ta lalata tushen Indiya a matsayinta na kasa mai bin addini.

Rijistar 'yan kasa na daga cikin kokarin gwamnatin Modi na gano tare da kawar da mutanen da ta ce sun shigo Indiya ba bisa ka'ida ba, an fara aiwatar da rijistar ne kawai a jihar Assam da ke arewa maso gabashin kasar, kuma jam'iyyar Bharatiya Janata mai mulki ta yi alkawarin kaddamar da wata sabuwar doka irin wannan shirin tabbatar da zama dan kasa a duk fadin kasar.

Gwamnatin Modi ta kare dokar zama dan kasa ta 2019 a matsayin nuna jin kai, kuma ta ce dokar an yi niyya ne kawai don ba da izinin zama dan kasa ga tsirarun addinai da ke gujewa tsanantawa kuma ba za a yi amfani da su ga 'yan Indiya ba.

Akwai musulmi miliyan 200 da ke zaune a Indiya, wadanda ke zama ‘yan tsiraru masu yawa a kasar da ke da mutane sama da biliyan 1.4. kuma sun bazu a kusan dukkan sassan kasar Indiya, kuma an kai musu hare-hare a wasu hare-hare da suka faru tun lokacin da Modi ya fara mulki a shekarar 2014.