Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

13 Maris 2024

08:09:02
1444121

Imam Khamenei: Gwagwarmayar Palastinu Tana Tsaye Kyam Da Karfi...Goyon Bayan Makiyan Falasdinu Haramun Ne Kuma Laifi Ne.

Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Sayyid Ali Khamenei ya fitar da fatawa da cewa goyon bayan kasashen duniyar musulmi ga makiya Palastinu haramun ne kuma yana matsayin babban laifi na

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) – ABNA- ya habarto maku cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ali Khamenei ya tabbatar da hakan a jiya talata cewa har yanzu gwagwarmayar Palastinawa tana nan daram  a tsaye da ƙarfi, kuma sai ta turmuza hancin sahyoniyawa a kasa.

A lokacin da yake tarbar masu karatun kur'ani mai tsarki, Sayyid Khamenei ya ce, "Dole ne dukkanin kasashen duniyar musulmi su goyi bayan Falasdinu,"yana mai jaddada cewa goyon bayan makiya gwagwarmaya haramun ne, kuma yana a matsayin babban laifi.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya yi ishara da cewa a duniyar musulmi akwai sojoji da gwamnatoci da suke goyon bayan makiyan al'ummar Palastinu da ake zalunta, yana mai cewa wadannan mutane za su yi nadama wata rana, kuma za su ga sakamakonsu cin amanarsu.”

Sayyid  Khamenei ya yaba da faifan bidiyo da aka nuna na yara maza daga zirin Gaza suna karatun kur’ani mai tsarki, inda ya kara da cewa “kololuwar tsayin daka da muke gani a Gaza a yau ya samo asali ne daga fahimtar kur’ani da kuma aiki da shi”.

Jagoran juyin juya halin Musulunci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana halin da ake ciki a zirin Gaza a matsayin kololuwa ta bangarori biyu: kololuwar wajen aikata laifuka, zalunci da rashin adalci a bangare guda, a daya bangaren kuma muna shaida kololuwar tsayin daka jajircewa.

Sayyid Khamenei ya bayyana laifuffukan da ba a taba ganin irinsu ba a Gaza, kamar kisan yara da jarirai da yunwa da kishirwa, a matsayin abin kunya ga wayewar kasashen yamma, ya kara da cewa duk da mallakar makamai da taimakon da Isra'ilawa suke da shi daga Amurka da kasashen yamma. Amma Hakuri mara misaltuwa na al'ummar Gaza, da kuma tsayin daka na mayakan gwagwarmaya, bai baiwa makiya damar cimma manufofinsu ba, yana mai jaddada cewa, gwagwarmaya ta kiyaye kusan kashi 90% na kwarewa da karfinta ya zuwa yanzu.

A watan Oktoban da ya gabata, Sayyid Khamenei ya sanar da cewa abin da ya faru a ranar 7 ga Oktoba (Guguwar Al-Aqsa) "Shak aye ne ga tsarin Isra'ila, ta fuskar soji da kuma leken asiri, wanda ba za a iya maido da shi (gyara shi) ba."

A 'yan kwanakin da suka gabata, kwamandan dakarun Quds a dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ismail Qaani ya tabbatar da cewa "fagen dagar Gwagwarmaya tana hade da dukkan sashenta’ kuma tana da karfin iko mai yalwa," ya kara da cewa fagen gwagwarmaya "har yanzu ba ta yi amfani da dukkan ikonta da iyawarta ba, amma ta tabbatar da cewa babu wanda ya isa ya jahilce ta”.

A lokacin daya gabata shima kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran, Manjo Janar Husain Salami, ya tabbatar da cewa "Isra'ila" ba za ta iya yin rikon sakainar kashi ba kamar da, yana mai jaddada cewa lokacin girmanta kai ya kare.