Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

13 Maris 2024

06:43:24
1444095

Palasdinawa Hudu Sun YI Shahada A Birnin Kudus Da Gabar Kogin Jodan.

Sojojin Sahyuniya sun kasha Falasdinawa hudu abirnin Kudus da gabar kogin Jodan.

 Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) – ABNA- ya bayar da rahoton cewa: majiyoyin labarai a safiya laraba, sun bada labarin cewa sojojin yahudawan sahyuniya sun bindige Falasdinawa 4 a birnin Kudus da ma gabar yammacin kogin Jordan.

Falasdinawa 2 ne suka yi shahada yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon harbin da sojojin yahudawan sahyoniya suka yi a shingen binciken ababan hawa na Al-Jeib da ke arewa maso yammacin birnin Kudus.

Sojojin yahudawan sahyoniya sun yi harbin kan mai uwa da wabi a yankin asibitin Jenin, sakamakon haka Palasdinawa 2 ne suka yi shahada, wasu uku kuma suka jikkata.

A 'yan sa'o'i kadan da suka gabata ne sojojin yahudawan sahyuniya suka harbe wani matashin Bafalasdine a shingen bincike na sansanin Shuafat da ke birnin Kudus.

A cikin kwanakin da suka gabata, da shigowar watan Ramadan, dubban sojojin yahudawan sahyoniya sun jibge a yankuna daban-daban na birnin Kudus.

Tun da farko tashar 12 ta gwamnatin sahyoniyawan da ke ishara da matakin da firaminista Benjamin Netanyahu ya dauka na hana Falasdinawa shiga masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan, ya ba da labarin wata takarda ta sirri cewa "Haron Halifa" shugaban hukumar leken asirin sojojin ya aike ga mahukuntan wannan gwamnati kuma takardar ta kai ga Netanyahu

.................................