Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

12 Maris 2024

07:49:55
1443852

Ayatullah Dari NajafAbadi: Watan Ramadan Wata Nw Watsuwar Rahamar Ubangiji Da Buɗe Ƙofofin Gafara.

Mataimakin shugaban majalisar koli ta majalisar Ahlul-baiti (AS) ya fitar da sako tare da taya daukacin al'ummar musulmin duniya musamman ma al'ummar wannan yanki masu imani na zuwan watan mai alfarma watan Ramadan.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: mataimakin shugaban majalisar koli ta majalisar duniya ta Ahlul-baiti (AS) kuma wakilin malaman fikihu a lardin cibiyar kasar Iran ya fitar da sakon taya murna ga daukacin al'ummar musulmin duniya musamman ma'abota imani da addini na wannan yanki dangane da shigowar watan Ramadan.

Ayatullah Qurban Ali Dari Najafabadi yana cewa a cikin wannan sakon: Watan Ramadan wata ne mai girma na Allah, wata ne wanda ranakunsa da dararensa suke da matukar kyau da sanyaya zuciya sannan iskarsa ke kaɗa ruhi da rai da nitsuwa cikin jin dadin ruhi. Girma da daukaka da daraja ta wannan wata ta kai matuƙa ta yadda Manzon Allah (SAW) da Ahlul Baiti (SAW) suka suke daukar tsawon lokaci suna jiran sa, kuma sun shirya tsaf wajen shiga shiga sararinsa mai tsarki da sarauta wanda wani shauki na musamman ya ya baibaye su. Cikin Farin ciki da sha'awa Suna shirya kansu don su riski kyawawan lokutan sa.

A wani bangare na wannan sakon yana cewa: Watan Ramadan wata ne na numfasawar dausayin Ubangiji da bude kofofin rahama da gafarar Ubangiji, wanda da zuwansa ake busa sabuwar rayuwa a jikin masu azumi, a cikin wannan wata ne Allah mai girma ba ya hana su wata falala da kulawa ta hanyar kiran bayinsa zuwa ga faffadan bakuncinsa.

A wani bangare na wannan sakon, wakilin Wali-e-Faqih a lardin cibiyar kasar ya ce: watan Ramadan shi ne watan da aka saukar da Alkur'ani a cikinsa, kuma ya kunshi mafifitan darare wadanda hatta mala'ikun gungu-gungu suke sauka a cikinsa ga ƙasa domin su samu shimfiɗar alheri kuma su ɗaukaka ayyukan salihai da muminai zuwa sama. Watan Ramadan wata ne da aka ambaci sunansa sau da dama a cikin Alkur'ani, wanda shi ne dalilin daukaka da kimar wannan wata mai daraja, kuma duk wanda da da gaske ya iya daidaita kansa da wannan wata, to zai samu farin ciki da dukkan jin dadi.

A cikin wannan sakon, mataimakin shugaban majalisar koli ta majalisar duniya ta Ahlulbaiti (AS) ya jaddada kiyaye alfarmar watan Ramadan inda ya kara da cewa: Wasu ‘yan kasar ba sa iya yin azumi saboda tafiye-tafiye, rashin lafiya ko wani dalili, kuma ana buqatar su da su guji duk wani aiki da xabi’u da ke nuni da rashin yin azumi, kamar ci, sha, da shan taba a cikin jama’a, da kiyaye haqqin wasu tare da kiyaye alfarmar wannan wata.

A wani bangare na wannan sakon yana cewa: Yayin da yake taya jagoran musulmi, Ayatullahi Imam Khamenei da al'ummar musulmin Iran mai girma da kuma muminai na lardin tsakiya murnar shigowar watan Ramadan mai alfarma. Ina rokon Allah ya ba mu nasara a cikin wannan wata mai albarka da fahimta, da ilimi ina yi wa kaina da kowa fatan alheri.


...................................