Kamfanin dillancin labaran
Ahlul-Baiti (a.s) –ABNA- ya nakalto daga majiyoyin yada labarai cewa: wannan
majiyar ta tabbatar da yanayin da aka samu a tattaunawar da aka yi a birnin
Paris a makonnin da suka gabata da kuma ya kai ga tsarin yarjejeniyar tsagaita
bude wuta ya nuna cewa, wannan tsari wani tsari ne na tsagaita bude wuta na
dogon lokaci domin share fagen tsagaita bude wuta na dindindin kamar yadda aka
tsara, amma kamar yadda gwagwarmaya ta yi hasashe a lokacin da makiya suka
fahimci cewa ba su kai ga cimma burinsu ba a Khan Yunus kuma bayan da dakarun makiya
suka dauki matakin yaki a arewacin Gaza makiya sun koma mataki na farko bayan
da suka gaza wajen yin matsin lamba kan mayakan gwagwarmaya tare da samun goyon
bayan Amurka, sai suka shiga wani mataki na matsin lamba kan mazauna Gaza.
Mayakan gwagwarmayar sun dauki matakin ne gaba daya a duk fadin arewacin Gaza kuma akwai gagarumin hadin kai a tsakanin dukkanin kungiyoyin gwagwarmaya, musamman ma dakarun al-Qassam da kuma bataliyoyin Saraya al-Quds a matakin ci gaba na ayyukan fagen daga.