Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

10 Maris 2024

08:02:07
1443391

Ku Ji Tsoron Wuta Ko Da Ciyar Da Rabin Dabino Ne, Ku Ji Tsoron Wuta Ko Da Shayar Da Makwarwar Ruwan Sha Ne.

“Ya Abal-Hasan! Mafi alherin ayyukan wannan wata su ne nisantar abunda Allah Ta’ala ya haramta.” Sai ya fashe da kuka, na ce: Ya Manzon Allah, me ya sa ka kuka? Ya ce: “Ya Ali, ina kuka ga abin zai faru a gare ka a cikin wannan wata, kamar ina tare da kai alhali kana sallah ga Ubangijinka, kuma mafi sharrin mutanen farko da na karshe, dan’uwan wanda ya soke Rakumar Samudawa, ya zo ta sare ka a a goshinka, har jinin jike muka gemu.”

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (a.s) –ABNA- ya kawo maku takaitccen hudubar Manzon Rahama Amincin Alla Ta’a Su Kara Tabbata A Gareshi Iyalansa Tsarkaka wacce yayi ta ga sahabbansa bias munasabar gabatowar watan Ramadan Mai Alfarma.

  An karbo daga Amirul Muminin, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa ya yi mana huduba wata rana ya ce:  

Ya ku mutane! Lallai watan Allah ya zo gabato maku da albarka da rahama da gafara. Wata ne da yake a wurin Allah shine mafificin watanni, kwanakinsa sune mafifitan kwanaki, dararensa sune mafifitan darare, sa'o'i sune mafifitan sa'o'i. Wata ne da a cikinsa aka gayyace ku zuwa ga liyafar Ubangiji, kuma a cikinsa aka sanya ku cikin ma’abota girma na Allah. Numfashinku a cikinsa tasbihi ne, barcinku a cikinsa ibada ne, kuma aikinku a cikinsa karbabbe ne, kuma addu'arku a cikinsa karbabbiya ce, saboda haka ku roki Allah Ubangijinku da niyya ta gaskiya da tsarkakakkiyar zukata, Ya ba ku babban rabo na dacewa da azumtarsa da karatun littafinsa, domin ya zamoi tabebbe duk wanda aka hana masa gafarar Allah a cikin wannan wata mai girma. Kuma ku tuna da yunwa da kishirwar ranar kiyama da yunwarku da kishirwarku a cikinsa.

Kuma ku yi sadaka ga miskinai da mabuqatanku, kuma ku girmama manyanku, kuma ku ji tausayin ‘ya’yanku, kuma ku kyautata wa ‘yan’uwanku, kuma ku tsare harsunanku, kuma ku rufe ido ga abin da bai halatta a yi duba gare shi da ganin ku, kuma ku kame daga barin jin abin da bai halatta ku ji ba. Kuma ku kyautata wa marayun mutane, za’a kyautatawa marayunku, kuma ku tuba zuwa ga Allah daga zunubanku, kuma ku daga hannayenku zuwa gare Shi, a cikin lokutan sallolinku, domin wadannan su ne mafifitan sa’o’in da Allah mabuwayi da daukaka a cikinsu da rahama ga bayinsa, yana amsa musu idan sun roqe shi (sun gana da shi a cikin ibadarsu), yana amsa musu idan suka kira shi, yana ba su idan sun roqe shi, kuma idan suka roqe shi yana amsa musu gayyata.

Ya ku mutane! rãyukanku sun dõgara a kan ayyukanku, sabõda haka ku sauƙaƙa musu da nẽman gãfara, kuma bãyanku sun yi nauyi da zunubanku, sai ku sauƙaƙa musu da yin sujadarku mai tsawo. Kuma ku sani cewa lalle ne Allah Ya yi rantsuwa da daukakarsa cewa ba zai azabtar da masu sallah da sujada ba, kuma ba zai tsora ta su da wuta ba a ranar da mutane za su tashi zuwa ga Ubangijin talikai ba.

Ya ku mutane! Wanda a cikinku ya yi buda-baki ma mai azumi mumini a cikin wannan wata zai sami ‘yancin rai daga Allah da gafarar zunubansa da ya gabata. Sai aka ce: Ya Manzon Allah! Ba dukkanmu ba ne ke da ikon hakan, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa’alihi Wasallama ya ce: Ku ji tsoron wuta ko da rabin dabino ne, ku ji tsoron wuta ko da ruwan sha ne.

Ya ku mutane! Wanda ya kyautata halayensa daga cikinku a cikin wannan wata, yana da sanadin tsallake siradi a ranar da qafafu suke zamewa, kuma wanda ya saukaka a cikin wannan wata ga abin da hannun damansa ya mallaka, (dukkan wanda suke karkashinsa) Allah zai sauqaqe masa nauyin hisabinsa, kuma wanda ya kauracewa aikata sharri a cikinsa, Allah zai nisantar masa da fushinsa a ranar da zai hadu da shi, kuma wanda ya girmama maraya a cikinsa, Allah zai girmama shi a ranar da zai hadu da shi, kuma wanda ya kiyaye sada zumuncinsa, Allah zai sada shi da rahamarsa a ranar haduwa da shi, kuma wanda ya yanke zumunta acikinsa, Allah zai yanke masa rahamarsa a ranar da zai hadu da shi, wanda yayi wata sallar nafila a cikinsa, Allah ya rubuta masa kubuta daga wuta, da wanda ya yi sallar farilla a cikinsa, yana da ladan wanda ya yi sallolin farilla saba'in a wasu salloli na wasu watanni, kuma wanda ya yawaita salati a gare ni a cikinsa, Allah zai nauyaya sikelinsa a ranar da ma'aunai ke yin sauki, kuma wanda ya karanta ayar Alkur'ani a cikinsa, yana da lada kwatankwacin wanda ya kammala Alkur'ani a kowane wata.

Ya ku mutane! Ƙofofin Aljanna a wannan wata a buɗe suke, sai ku roƙi Ubangijinku kada Ya rufe su a gare ku, kuma kofofin Jahannama a rufe suke, don haka ku roƙi Ubangijinku kada Ya bude akan ku. An daure shaidanu, saboda haka ku roki Ubangijinku kada ya ba su wani iko a kanku.

Amirul Muminina Ali binu Abi Talib, ya ce: “Sai na tashi na ce: Ya Manzon Allah! Menene mafi kyawun ayyuka a cikin wannan watan?

Sai ya ce: “Ya Abal-Hasan! Mafi alherin ayyukan wannan wata su ne nisantar abunda Allah Ta’ala ya haramta.” Sai ya fashe da kuka, na ce: Ya Manzon Allah, me ya sa ka kuka? Ya ce: “Ya Ali, ina kuka ga abin zai faru a gare ka a cikin wannan wata, kamar ina tare da kai alhali kana sallah ga Ubangijinka, kuma mafi sharrin mutanen farko da na karshe, dan’uwan wanda ya soke Rakumar Samudawa, ya zo ta sare ka a a goshinka, har jinin jike muka gemu.”

Amirul Muminin, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Sai na ce: Ya Manzon Allah, wannan zai sameni bisa kubutar addinina ne? Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Eh‚ a cikin kubuta ne ga addininka, sai ya ce: ‚Ya Ali! Wanda ya kasheka Ni ya kashe, wanda fusataka Ni ya fusata, wanda ya Zage ka Ni ya Zaga, domin kai daga gare ni kake, kamar yadda raina yake, ruhinka daga ruhina ne, yumbunka daga yumɓuna ne, lalle ne Allah, Mai tsarki da ɗaukaka, Ya halicce ni da kai, kuma Ya zaɓe ni da kai, kuma Ya zaɓe ni don annabta kuma ya zabe ka don imamanci, kuma duk wanda ya karyata imamancinka ya karyata Annabcina. Ya Ali kai ne wasiyyi na, uban ‘ya’yana, mijin ‘yata, kuma magajina ga al’ummata a tsawon rayuwata, kuma bayan rasuwata umurninka shine umurnina, haninka hani na ne. Na rantse da wanda ya aiko ni da annabta, kuma ya sanya ni mafificin halitta, lalle kai ne hujjar Allah a kan halittunsa, kuma majibincinsa a kan sirrinsa, kuma majibincinsa a kan bayinsa”.