Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

8 Maris 2024

20:36:25
1443010

Limamin Juma'ar Alishashr: Ya Kamata Mu San Kimar Darajar Kwanakin Ƙarshen Watan Sha’aban.

Ya zo a cikin littafin Ayun Al-Akhbar, daya daga cikin sahabban Imam Rida, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana cewa na na shiga wajen Imam a ranar Juma'ar karshen watan Sha'aban, sai ya ce wannan ita ce Juma'ar karshe ga watan Sha'aban, a cikin wadannan kwanaki na karshen watan sha'aban, kayi kokarin rama abin da ka rasa a cikin wannan wata ta hanyar yin addu'a mai yawa, da neman gafara, da karatun Alqur'ani

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Hujatul-Islam Wal-Muslimin Hamidinejad, limamin juma'a Na birnin Alishashr dake Lardin Bushahr a kudubar Juma'a ta yau ya ce: yazo a cikin wani hadisi mai daraja da ya zo a cikin littafin Ayun Al-Akhbar, daya daga cikin sahabban Imam Rida, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana cewa na na shiga wajen Imam a ranar Juma'ar karshen watan Sha'aban, sai ya ce wannan ita ce Juma'ar karshe ga watan Sha'aban, a cikin wadannan kwanaki na karshen watan sha'aban, kayi kokarin rama abin da ka rasa a cikin wannan wata ta hanyar yin addu'a mai yawa, da neman gafara, da karatun Alqur'ani.

Sannan yace aci gaba da Nasihar da Imam ya ke masa cewa: ka cire kiyayyar muminai daga zuciyarka, ya ku masoyanmu, bisa la'akari da wannan hadisin, a cikin wadannan kwanaki na karshen watan Sha'aban, mu yi iyakacin kokarinmu wajen ganin mu samu cancantar halartar gagarumin bukuncin Allah a cikin watan Ramadan, wata kila wasu daga cikinmu suna da kyama da rigingimu da ’yan uwanmu na addini, kada mu bari wannan duhu ya dawwama a cikin zukatanmu, domin a iya samun lura da kulawa da mu da kuma gayyatar mu zuwa ga wannan bakunci na Ubangiji.

Watan Ramadan wata ne mai girma, Manzon Allah (S.A.W) yana da wata huduba mai fadakarwa kan muhimmancin wannan wata mai suna hudubar Shabaniyah, wacce ita ce mafi kyawu da kimar halayya da imani da idan wani bai kasance ya mallaki wadannan siffofin ba, bai kamata yana daukar kansa a matsayin musulmi na kwarai ba, kuma yana da'awar wanda yake da tsarin rayuwa na Alkur'ani da Musulunci, a cikin wannan hudubar Manzon Allah yana cewa watan Allah ya zo muku da siffofi guda uku na albarka, rahama da gafara, wata ne wanda ya fi kowane watanni da falala da dukkan kwanakinsa da dararensa da dukkan lokutansa suna daga cikin mafifita akan ranaku da darare da sa'o'i, a cikin wannan wata ana kiran ku zuwa walimar Allah kuma Allah ya karrama ku, ya sanya numfashin ku ya zamo ladan yin zikiri kuma ko barcinku ya zamo ibada ne.

Mutanen da ba su shirya shiga wannan babban bakunci ba da Allah da kansa shi ne wanda ya shiryar. Sun zamo masu tsananin kaskanci da tabewa. Kuma madalla ga wadanda suka je tarbar wannan wata da girma da kuma maraba da shi cikin farin ciki.