Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

8 Maris 2024

19:39:06
1442986

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Ganawa Da 'Yan Majalisar Kwararru:

Bai Kamata A Karɓe Tutar Yaƙi Da Zalunci Da Girman Kai Daga Jamhuriyar Musulunci A Kowane Zamani Ba

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, yayin da yake bayyana dalilai na hankali da addini da na yan Adamtaka na tsayuwar tsarin Jamhuriyar Musulunci na tsayawa tsayin daka wajen nuna adawa da girman kai, ya bayar da shawarwari masu muhimmanci ga zababbun wakilan sabuwar majalisar kwararru masana jagoranci da sabuwar Majalisar Majalisar Musulunci.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ayatullah Khamenei, Jagoran juyin juya halin Musuluncin, a safiyar ranar Alhamis a wata ganawa da ya yi da shugaba da mambobin majalisar kwararrun jagoranci, ya yi bayanin mahangar hankali da addini da na dan Adam na tsarin Jamhuriyar Musulunci na tsayawa tsayin daka wajen adawa da ma'abuta girman kai, yayin da yake bayar da shawarwari masu muhimmanci ga zababbun wakilan sabuwar majalisar kwararru da kuma sabuwar majalisar dokokin Musulunci ya jaddada cewa: Kafa sabuwar majalisar dokokin Musulunci abu ne mai dadi, abun bege kuma mai kima wanda ya kamata mambobin da aka zaba su yaba da sanin hakan.

Ayatullah Khamenei a cikin wannan taro wanda shi ne taro na karshe na wa'adi na biyar na majalisar kwararru tare da shi, yana mai ishara da gudanar da tattakin ranar 22 ga watan Bahman da kuma zaben da aka yi a ranar 11 ga watan Isfand. Inda ya kira Watannin Bahman da Esfand na bana, a matsayin watanni da sukai fice fiye da sauran shekarun da suka gabata, wajen bayyanar alamomin dimokuradiyyar Musulunci. Dangane da mahangar gwagwarmaya da tinkarar ds Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke yi kan 'yan ta'adda ya ce: Kafin kafuwar Jamhuriyar Musulunci, gaba daya a duniya akwai fuskancin Dimokuradiyya ita kadai tilo da ta dogara ne da tsarin dimokuradiyya mai sassaucin ra'ayi na yammacin turai, amma bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, an kafa wani sabon fage bisa tsarin demokradiyyar Musulunci, wanda a bisa dabi'a ya sabawa tsarin demokradiyya na yammacin turai.

Jagoran ya kira ci gaban tsarin dimokuradiyyar Musulunci a Iran a matsayin abin da ke kawo cikas ga manufofin Dimokaradiyyar Yamma kuma shine mafarin ci gaba da rigingimu da adawa da tsarin Musulunci yana mai cewa: dalilin da ya sa suke jin hatsari da kin amincewa da wannan tsarin shi ne; a cikin ma'anar tsarin dimokuradiyya na yammacin Turai, akwai girman kai da wuce gona da iri kuma akwai take hakkin kasashe, yakin da ake yi da zubar da jini mara iyaka don samun madafun iko, wanda ke tabbatar da hakan shine irin mulkin mallaka na kasashe da dama na Asiya, Afirka da Latin 

Amurka a karni na 19, wato a lokacin kololuwar lokacinsu da takensu da da'awarsu ke tashe a fagen dimokuradiyya, 'yanci da 'yancin dan adam hakan ke faruwa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira lamari mafi muhimmanci a fagen Dimokaradiyyar Musulunci da cewa: ya samo asali ne ta dalilin yanayin Musulunci wajen fuskantar irin wannan ta'asa da cin zarafi, yayin da yake mai da martani kan wannan tambayar da ke cewa me yasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran take fuskantar ma'abota girman kai? yana mai cewa: Mu bamu da wani rikici tsakanin mu da kasashe ko gwamnatoci ko al'ummomi a kan kanmu, sai dai mu muna adawa zalunci da wuce gona da iri da ke cikin fagen dimokuradiyyar Yammacin Turai ne.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana abubuwan da suka faru a zirin Gaza a matsayin wani misali karara na girman kai da wuce gona da iri kan masu wata kasa da zalunci da kisan gilla da ake yi wa mata da kananan yara da lalata dukiyoyin al'ummar da hanyoyin samun wannan kasa inda ya ce: A hakikanin gaskiya adawar Jamhuriyar Musulunci tana adawa da irin wannan ta'asa kuma wadannan laifuka ne da kowane hankali da al'ada da shari'a da lamirinsu suka yi tir da su, amma Amurka da Ingila da wasu kasashen Turai suna goyon bayansu.

Ya kuma jaddada cewa: Ya kamata wannan batu ya fito fili kuma a fili ƙarara cewa fagen girman kai da zalunci da keta iyaka da kashe-kashe ana yin su ne da sunan dimokradiyya, 'yancin dan Adam da 'yanci.

Haka nan kuma yayin da yake jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kasance mai rike da tuta da kuma sahun gaba wajen tinkarar girman kai, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Wajibi ne a kara daga tutar yaki da girman kai a kowace rana, kuma ba za mu bari a kwace wannan tuta daga Jamhuriyar Musulunci ba.

Har ila yau Ayatullah Khamenei ya dauki bayyana mahangar Jamhuriyar Musulunci ta Iran wajen tsayin daka da tinkarar ma'abuta girman kai ga sabbin tsatso a matsayin wani muhimmin aiki inda ya ce: Abin farin cikin shi ne, tsawon shekaru fiye da arba'in na rayuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, mun ci nasara wajen nuna fuska da fage da kuma ɓangaren hanyar yaƙin girman kai.

A wani bangare na jawabin nasa, ya dauki aikin majalisar kwararru a matsayin aikin gudanarwa mafi muhimmanci a tsarin jamhuriyar Musulunci, wato tantance shugabanci da kula da kiyaye cancantarsa, sannan ya kara da cewa: Mambobin majalisar malamai su tabbatar da cewa ba su yi watsi da ka'idojin tsarin Jamhuriyar Musulunci a zabukansu ba.

Haka nan kuma yayin da yake bayani kan kayyadaddun ka'idoji na tsarin Musulunci da ba sa canjawa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da cewa: A cikin kundin tsarin mulki akwai wasu ka'idoji da suka dace kamar tabbatar da adalci da yaki da fasadi da daukaka matsayin ilimi da aiki da Musulunci a cikin al'umma, a cikin kundin tsarin mulki maganganun Imami mai girma da koyarwar Musulunci, wadanda kwararru a cikin zaben jagoranci ya kamata a aikata su tare da la'akari da kiyaye wadannan ka'idoji.

A kashi na uku na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei, yayin da yake ishara da gudanar da zaben majalisar dokokin Musulunci, ya dauki zuwan kowace sabuwar majalisar a matsayin abu mai dadi da kuma kara samun sabbin fata ga kasar inda ya ce: kasancewar sababbin wakilai tare da wakilan zamanin da suka gabata, wanda ya haɗu da juna wani nau'i ne na kwarewa, babban jari ne mai mahimmanci da jini ajika mai kyau a cikin sassan tsarin siyasa.

A wani bangare na muhimmin bayanin da ya yi, ya kira kalamai masu janyo ce-ce-ku-ce, da tsageru, a matsayin dalilin bacin kafa sabuwar majalisar, inda ya ce: ya kamata zababbun 'yan majalisar su kula, kada su bari zakin kafa majalisar ta zama mai daci a cikin dandanon jama'a da yanayin siyasar kasar, yayin da idan majalisar ta shiga fada da fadace-fadace da fagage daban-daban, to za ta sauka daga babban aikinta da ya doru akanta.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da shawarwarin da Amirul Muminin Alaihis Salam da ya kan yi wa hakimansa dangane da kiyaye ibadar Ubangiji, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa daya daga cikin tabbatattun bukatun jami'ai da wadanda abin ya shafa a jamhuriyar Musulunci shi ne yin zamo masu bin dokan Shari'a da riko da kiyaye halal da haram da nisantar karairayi da gulma da kazafi: Kamar yadda ya wajaba a kan mu kiyaye takawa a cikin al'amuran mu, haka nan a fagen siyasa da kasuwanci mu kiyaye. takawa da nisantar haram.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Tabbas a cikin harkokin siyasa akwai banbance-banbancen salo da nau'ikan siyasa, wanda hakan ba wani cikas ba ne, amma kowa ya shirya fage don samun rahamar Ubangiji da ni'ima ta hanyar ibada.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kuma girmama magabatan majalisar kwararru musamman marigayi Ayatullah Imam Kashani, sannan kuma ya kira watan Sha'aban a matsayin watan bushara da farin ciki da kuma watan tsarkakewa da tanadin zukata tare da gafara da yin addu'o'in shiga watan Ramadan, don samun gafarar Allah a sauran kwanakin da suka rage a wannan wata.

A farkon wannan taro, Ayatullah Jannati, shugaban majalisar kwararrun jagoranci ya bayyana wasu daga cikin batutuwa da 'yan majalisar suka gabatar, dangane da gudanar da taron na baya-bayan nan.

Bugu da kari, Ayatullah Husaini Bushehri mamba a kwamitin kwararru na majalisar ya gabatar da rahoto kan zaman karshe na zaman majalisar kwararru karo na biyar da kuma muhimman batutuwan da mambobin suka gabatar, ya ce: Ganawa da shugaban kasa na wasu sa'o'i da tattaunawa kan batutuwa, nazarin batutuwan da suka shafi tattalin arziki ta hanyar gayyatar ministan tattalin arziki, da kuma rahoton ci gaban yankin daga kwamandan dakarun Quds na IRGC na daga cikin sauran shirye-shiryen wannan taro.