Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

7 Maris 2024

19:15:15
1442912

Adadin Shahidai A Gaza Ya Kai Mutane Dubu 31

A rana ta 153 na yakin Gazza ma'aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa a cikin sa'o'i 24 da suka gabata gwamnatin yahudawan sahyoniya ta aikata wasu sabbin laifukan Ta'addanci 9 a yankuna daban daban na zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadin shahadar mutane 83 tare da jikkata wasu 142.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: A rana ta 153 na yakin Gazza ma'aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa a cikin sa'o'i 24 da suka gabata gwamnatin yahudawan sahyoniya ta aikata wasu sabbin laifukan Ta'addanci 9 a yankuna daban daban na zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadin shahadar mutane 83 tare da jikkata wasu 142. Ma'aikatar ta kuma bayyana cewa, an bar wasu gawarwakin shahidan a karkashin baraguzan gine-gine, wasu kuma an bar su a gefen titina, kuma saboda ci gaba da kai hare-hare da yahudawan sahyuniya suke yi, kungiyoyin agaji ba su iya jigilarsu.