Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

1 Maris 2024

14:45:20
1441421

Jagora: Idanun Duniya Na Kan Zaɓen Iran KU Sa Masoyanmu Au Yi Farin Ciki Kuma Maƙiyanmu Su Ji Kunya + Bidiyo

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Idanun Duniya Na Kan Zaɓen Iran KU Sa Masoyanmu Au Yi Farin Ciki Kuma Maƙiyanmu Su Ji Kunya

Jagoran: Ya kamata al'ummar mu abin kaunarmu su sani cewa idanun mutane da dama a duniya, na daidaiku ne ko 'yan siyasa da masu matsayi na kasa da na siyasa a yau, suna kan Iran da ku mutanenta' suna son ganin me zaku yi a wannan zabe da abin da sakamakon zaben zai kasance.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ayatullah Sayyid Ali Khamenei Jagoran juyin juya halin Musulunci a safiyar yau Juma'a - 1 ga watan Maris na shekara ta 2024 wanda yayi daidai da 11ga watan Isfand 1402- a cikin mintuna na farko na fara kada kuri'ar zaben wa'adi na 12 na zaben Majalisar Musulunci da wa'adi na 6 na Majalissar Malamai a Husainiyyar Imam Khumaini (r.a) ya jefa kuri'unsa a cikin akwatin zabe tare da jaddada cewa na faɗi a zaben da ya gabata kuma yanzu zan maimaita: ku je ku kada kuri'ar ku a cikin sa'o'i mafi mahimmanci. Inda ya fayyace cewa: Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da cewa a yau ta kasance rana mai albarka ga al'ummar Iran kuma ya zamo sakamakon kokarin al'ummarmu da masu ruwa da tsaki a bangarori daban-daban na batutuwan da suka shafi zaben su iya kaiwa ga sakamakon da ake bukata da kuma amfanar al'ummar Iran.

Ayatullah Khamenei ya ce ina da nasihohi guda biyu ga masoyana al'ummar Iran; Ya ce: Alkur’ani yana nasiha ga mutane da su yi rige-rige zuwa ga aikata ayyukan alheri da kuma su samu fifiko ga wasu. Na faɗa a zabukan da suka gabata kuma yanzu ina jaddada cewa ku jefa kuri'ar ku a cikin akwatin zabe da wuri-wuri.

Ya ci gaba da cewa: Nasihata ta biyu ita ce a zabi dukkan mutanen da suka dace a kowane fanni, ba adadi kadan ba. A kowane yanki ku kada kuri'a gwargwadon abin da ake buƙata don wannan yanki, kada ku zaɓi ƙasa kaɗan daga yadda ake bukata Misali, a Tehran, domin zabe a majalisar Kwararrun musulunci, wajibi ne a zabi mutane 16, za a zabi mutane 16 daidai ba kasa da haka ba, a Tehran a zaben majalisar Musulunci, Yakamata ne ku zabi mutane 30 cif-cif. Maganata ta karshe ga masu shakku amsata ita ce, babu bukatar istikhara wajen aikata aikin Alkhairi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da cewa: Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya sanya yau ta zama ranar farin ciki ga al'ummar Iran kuma sakamakon kokarin da al'ummarmu da kuma masu ruwa da tsaki a cikin lamurran zabe daban-daban, in Allah ya yarda ya zamo an samu sakamakon da ake so kuma a karshe ya zama ya amfanar da al'ummar Iran.

Jagoran ya ce: Ya kamata al'ummarmu masoyanmu su sani cewa idanun mutane da dama a duniya, daidaiku ne ko 'yan siyasa da masu rike da mukamai na kasa da na siyasa, suna kallon Iran. Kuma a yau suna son ganin abin da za kuyi a wannan zabe da sakamakon zaben ku, duka da masoyanmu da masu kaunar al'ummar Iran, haka su ma makiyanmu, sun tura ido suna kallon al'amuran kasarmu da al'ummarmudaga kowane bangare. Ku Kula da wannan batu na cewa ku sanya masoyanmu farin ciki su kuma makiya sanya su jin kunya da yanke tsammani.