Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

26 Faburairu 2024

05:26:00
1440362

Kungiyar Hizbullah Ta Kasar Labanon Na Ci Gaba Da Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Kan Sansanonin Sojojin Yahudawan Sahyuniya

An kai hare-haren rokoki a kan wuraren da sojojin yahudawan sahyoniya a arewacin yankunan da aka mamaye.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (a.s) –ABNA- ya nakalto daga majiyoyin yada labarai cewa, kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta kai harin makami mai linzami kan sansanonin sojojin yahudawan sahyuniya a arewacin yankunan da ta mamaye.

A cikin wannan raahto ya zo cewa, kungiyar gwagwarmayar Islama ta kasar Lebanon ta sanar da cewa, ta auka wa dakarun gwamnatin mamaya a kewayen sansanin Marj da ke arewacin Falasdinu da ke mamaye da makamai masu linzami na Barkan.

Har ila yau Mayakan gwagwarmayar Lebanon sun yi nasarar kai hari kan wani gini a matsugunin Al-Manarah da ke arewacin Falasdinu da aka mamaye da kuma kusa da kan iyakar Lebanon, ginin da sojojin Isra'ila suke.

A cikin wata sanarwa da kungiyar Hizbullah ta fitar ta nanata cewa: Mujahidan gwagwarmayar Musulunci sun kai hari kan hedkwatar sojojin mamaya a matsugunan yahudawan sahyoniya na Malikiyya da makaman da suka dace.

Har ila yau, kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon tana kai hari kan tarurrukan dakarun mamaya a kusa da sansanin Ramim, wanda ya yi sanadiyar mutuwa da jikkata wasu da dama daga cikinsu.

 

Har ila yau, an harba makaman roka da dama a yankin “Jalili Bala”, a lokaci guda kuma, a wasu gurare da yahudawan sahyoniyawan suka mamaye a yankunan “Sheba’a” su ma suna karkashin hare-haren gwagwarmayarLebanon.

A cikin 'yan watannin da suka gabata kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta kai hare-hare kan cibiyoyin soji na wannan gwamnati a arewacin yankunan da aka mamaye, biyo bayan munanan laifukan da gwamnatin sahyoniyawan sahyoniya ta aikata a zirin Gaza da kuma zubar da jinin al'ummar Palastinawa masu yawa a wannan yanki. Lamarin da ya haifar da fargabar yahudawan sahyoniyawan da ke zaune a wadannan yankuna.

Ya zuwa yanzu, dubun dubatan yahudawan sahyoniya sun bar matsugunan da ke kusa da kan iyakokin kasar Labanon saboda fargabar hare-haren gwagwarmaya.