Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

18 Faburairu 2024

12:49:22
1438709

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Zaɓe Shi Ne Ginshikin Tsarin Jamhuriyar Musulunci

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da cewa zabe shi ne tushen tsarin Jamhuriyar Musulunci, yana mai jaddada cewa hanyar kawo gyara a kasar ita ce zabe.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei DM, yayin da ya karbi bakuncin al'ummar lardin gabashin Azarbaijan (arewa maso yammacin kasar Iran) a yau Lahadi, ya yi nuni da cewa, zabe shi ne tushen tsarin Jamhuriyar Musulunci, yana mai jaddada cewa, hanyar kawo gyara a kasar ita ce zabe.

Wannan taro da aka gudanar a Husainiyar Imam Khumaini (a.s) a birnin Tehran, ya zo ne a daidai lokacin tunawa da wani yunkuri mai cike da tarihi a ranar 18 ga Fabrairu, 1978, wato kimanin shekara guda kafin nasarar juyin juya halin Musulunci a ranar 11 ga Fabrairun 1979 da al'ummar birnin Tabriz suka gudanar.

A cikin wannan taro dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana matukar godiya da jinjinarsa ga al'ummar Iran da jami'an tsaron kasar dangane da nasarar da aka samu a jerin gwano na tunawa da nasarar juyin juya halin Musulunci, bisa la'akari da yadda al'ummar Iran suka halarta a dukkan bangarori na kasar Iran a bana sun kuma nuna alfaharinsu da samun juyin juya halin Musulunci a gaban duniya a ranar 22 ga watan Bahman.

Ayatullah Khamenei ya kuma mika godiyarsa ga wadanda suka ba da gudummawa wajen tabbatar da tsaron wannan gagarumin tattaki na kasa.

Jagoran ya yi nuni da cewa, a ko da yaushe ana gudanar da zabuka a kasarmu cikin aminci da tsari, kuma idan Allah ya kaimu a wannan karon ma za a gudanar da zabukan kasar, inda ya kara da cewa: Wajibi ya zamo bambamcin siyasa da al'adu bai shafi hadin kan kasar Iran da al'umma a gaban makiya.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Ko shakka babu ma'abota girman kai suna adawa da zabukanmu, domin tsarinmu shi ne tsarin Jamhuriyar Musulunci, suna adawa da jamhuriyarta da Musuluncinta, kuma bayyanar jamhuriya shine wadannan zabuka, don haka a lokacin da Amurka ke adawa da tsarin jamhuriyar Musulunci, a hakikanin gaskiya tana adawa da zabuka, kuma tana adawa da halartar jama'a, tana adawa wajen ganin mutane ba su kai ga akwatunan zabe ba, tana kuma adawa da ɗauki da kuma halartar mafi yawan al'ummar kasar a zaben.

Ya kara da cewa: A wani lokaci daya daga cikin shugabannin kasar Amurka ya yi jawabi ga al'ummar Iran a kusa da zabuka, ya ce, "Kada ku shiga zaben," kuma ba shakka wadannan zabukan na da sun fi a nishadi fiye da kowane lokaci, a hakikanin gaskiya shugaban na Amurka ya taimaki al'ummar Iran ba tare da saninsa ba, bayan haka, sun daina shelanta irin wadannan abubuwa, ba su fadi wadannan maganganu a zahiri ba, sai dai ta hanyoyi da nau'o'i daban-daban, suna kokarin nisantar da jama'a daga zaben, tare da dakile su.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa, kowa yana da wani aikin da ya rataya a wuyansa, kuma aikin gwamnati, majalisar shura ta Musulunci, da sauran cibiyoyi na hukuma shi ne tsayin daka, juriya da ci gaba da aiki, da amincin aiki, da gaskiya ga al'umma, da fifita bukatun kasa fiye da na kashin kai.

Ya kuma yi gargadin a kan raina karfin makiya yana mai cewa: Kada ku yi tunanin cewa makiya suna da rauni kuma ba su da karfi - daya daga cikin muhimman sharudda na samun nasara shi ne sanin karfin makiya, amma a lokaci guda kada ku ji tsoronsa, idan kun kasance kuna jin tsoronsa. Idan kuka ji tsoro, za ku yi hasara, kada ku ji tsoron maƙiyi, kuma kada ku ji tsoro, daga barazanarsa, ko girman kai da matsinsa.