Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

18 Faburairu 2024

11:20:47
1438691

Shahidai Fiye Da 120 Da Kuma Jikkata A Sabon Hare-Haren Yahudawan Sahyuniya A Gaza

Sabon harin ta’addanci da yahudawan sahyuniya suka aikata a Gaza ya bar shahidai fiye da 120 da kuma jikkata

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (a.s) – ABNA- ya bayar da rahoto cewa: Ofishin yada labarai na jihar Zirin Gaza ya bayyana wani sabon munanan hare-haren da sojojin yahudawan sahyuniya suka aikata a zirin Gaza tare da jikkatan wasu shahidai sama da 120 tare da sanar da cewa mayakan yahudawan sahyuniya sun kai hari kan gidaje 9 a tsakiyar lardin Gaza.