Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

18 Faburairu 2024

11:17:15
1438687

Adadin Shahidan Gaza Ya Kai Mutane Dubu 28 Da 985

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa, sakamakon kashe-kashen mutane 13 da gwamnatin yahudawan sahyoniya suka yi a cikin sa'o'i 24 da suka gabata a zirin Gaza, mutane 127 ne suka yi shahada yayin da wasu Palasdinawa 205 kuma suka jikkata.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (a.s) – ABNA- ya bayar da rahoto cewa: Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa, ciki har da wadannan shahidai, jimillar shahidai a zirin Gaza ya kai dubu 28 da 985 sannan adadin wadanda suka jikkata ya kai dubu 68 da 883 tun farkon hare-haren da aka kai a zirin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba (15 Mehr).